Shaykhul lslam

Shaykhul lslam To create awareness among the people

SHIN YA HALATTA NA AURI WANDA BA AHLUS SUNNA BA ?TambayaSlm Malam ya halalta mace ta Auri wanda ba dan Ahlul sunnah ba??...
15/01/2026

SHIN YA HALATTA NA AURI WANDA BA AHLUS SUNNA BA ?

Tambaya
Slm Malam ya halalta mace ta Auri wanda ba dan Ahlul sunnah ba?????? Don Allah ina son aba mu Hujjoji saboda ta samu abinda zata kare kan ta da shi.

Amsa
To 'yar'uwa Annabi ﷺ yana cewa: "Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084.

Malamai suna cewa wannan hadisin yana nuni akan cewa duk wanda ba'a yarda da addininsa ba, ba za'a aurar masa ba, wannan sai ya nuna cewa duk wanda bidi'arsa take kaiwa zuwa kafirci, bai halatta a aura masa 'ya ba, don haka duk dan shi'an da yake zagin sahabbai ko yake kafirta su bai halatta a aura masa 'ya ba, saboda ba musulmi ba ne, domin ya karyata Allan da ya yarda da su, haka sufin da yake allantar da shehunansa, ko yake ganin sun fi annabawa, kuma yana sane yake hakan, ba jahili ba ne ko kuma wanda yake da shubuhar da za'a iya warware masa.

Amma duk mai aikata bidiar da ba za ta kai zuwa kafirci ba, to ya hallata a aura masa 'ya, kamar wanda yake yin maulidi saboda son Annabi ﷺ Allah ne mafi sani.

TAMBAYOYI HUDU 4 DA WANI MUTUM YAYIWA ALIYU DAN ABI DALIB.Wani mutum yazo wurin amirul mu'uminina Aliyu ibn abiy dalib y...
29/12/2025

TAMBAYOYI HUDU 4 DA WANI MUTUM YAYIWA ALIYU DAN ABI DALIB.

Wani mutum yazo wurin amirul mu'uminina Aliyu ibn abiy dalib yace zan tambayeka ne akan mas'aloli hudu 4

1️⃣.Na farko Menene wajibi menene abinda yafi zama wajibi....??
2️⃣.Na biyu menene makusanci kuma menene mafi kusa...??
3️⃣.Na uku menene abin mamaki kuma menene Wanda yafi ban mamaki....??
4️⃣.Na hudu menene abu mai wuya sannan menene mafi wuya.....??

Sai amirul mu'uminina yace........

1️⃣.Na farko abinda yake wajibi shine yiwa Allah da'a, abinda yafi zama wajibi kuma barin sabo....!!
2️⃣.Na biyu abu makusanci shine ranar alqiyama, mafi kusa kuma shine mutuwa...!!
3️⃣.Na uku abin mamaki i'tace duniya, Wanda yafi ban mamaki kuma son duniya....!!
4️⃣.Na hudu Abu mai wuya/wahala shine qabari, mafi wuya kuma shine tafiya qabarin ba guzuri....!!

Ya Allah mai jujjuya zukata katabbatar da zukatammu akan yimaka da'a/biyayya ameen ya hayyu ya kayyum

Shaykhul Islam

IBNUL QAYYUM YACE............Ibnul qayyim yace, yaro 'idan aka jefashi a sama sai yayita dariya saboda yana da cikakkiya...
13/12/2025

IBNUL QAYYUM YACE............

Ibnul qayyim yace, yaro 'idan aka jefashi a sama sai yayita dariya saboda yana da cikakkiyar yadda cewa baza'a barshi yafado ba.

Haka dai bawa shima yayarda cewa da qaddara zata jefashi bazai fadoba matukar yayi cikakkiyar yarda da ubangijinsa rahamar Allah zata cafeshi.

Allah ka yaye mana damuwar mu amin.

WANNAN ITACE AKIDAR MU...................Ko a IZALA, ko SALAFIYYA, ko a DARIKA, duk inda kake wannan kai ya dama.Matukar...
01/12/2025

WANNAN ITACE AKIDAR MU...................

Ko a IZALA, ko SALAFIYYA, ko a DARIKA, duk inda kake wannan kai ya dama.

Matukar da’awarka akan alkur’ani da hadissan annabi muhammad saw take tafiya, bisa fahimtar sahabba ta tabi'ai to wallahi kai namu ne.

Idan kaga mun samu matsala dakai, to ka bar alkur’ani da hadisi ka dauki son zuciya ne.

Sannan duk abunda ya sabawa alkur’ani da hadisi to wallahi saina fada, kuma zanyi jan kunne ga al’umma domin su guje aikata wannan dabi’ar.

Ina rokon Allah ya tabbatar damu akan tafarki nadaidaici Ameen ya hayyu ya kayyum

WANI MAI HIKIMA YACEWA DANSA.....wani mai hikima yacewa dansa, ya Dana arayuwa kada ka bari ka kubuta daga abu uku...1) ...
28/11/2025

WANI MAI HIKIMA YACEWA DANSA.....

wani mai hikima yacewa dansa, ya Dana arayuwa kada ka bari ka kubuta daga abu uku...
1) kaci mafi kyau a abinci.
2)ka kuma kwanta a shinfida mai kyau.
3)ka kuma zauna a mafificin gida.

Sai Dan nasa yace....babana ai bazan iya ba ai mu matalauta ne.
Sai mai hikiman yace....idan kaci abinci alokacin da kake jin yunwa kawai abinda kaci zai zama mafificin abinci.

Idan kuma kayi aiki tukuru a yininka ka mori lafiyarka kakai yamma a gajiye, wurin dazaka kwanta zai zama mafificin shinfida.

Kuma duk lokacin dakake mu'amalantan mutane da kyakkyawan mu'amala zaka zauna acikin zukatansu, shiyasa nace kazauna a mafificin gida wato zukatan mutane.

Allah yasa mudace.

A HALIN DA KA MUTU A HAKA ZA A TASHE KA.Jiya ina Karanta wani labari; wani mutum Yana cikin 'Adaidaita' sai wasu Mata bi...
26/11/2025

A HALIN DA KA MUTU A HAKA ZA A TASHE KA.

Jiya ina Karanta wani labari; wani mutum Yana cikin 'Adaidaita' sai wasu Mata biyu s**a shigo, da ganinsu suna cikin tashin hankali.

Sai ya ji dayar tana ce wa mai kukan ki yi hakuri, mutuwa ai rigar kowa ce. Sai ya fahimci mutuwa aka yi Mata, sai ya yi Mata Ta'aziyya.

Sai Mai kukan take cewa yaruwarta, ba za ki gane ba ne, tsorona Allah Ya sa wane (mijin Mai rasuwar) Kada ya bude wayarta, kuma tana wajensa yanzu, don Wallahi har dansu na halak sai ya kore shi cewa ba dansa ba ne.

Nan ya fahimci inda damuwar take, ba ta mutuwar ba ce, ta tonon asiri ce. Ta mutu ba ta shirya ba, kuma ta bar baya da kura.

Ita kuma wannan ba tunanin kunyar Lahira da ta Allah cewa ta fi matsala take ba, a'a ta duniya mai karewa gobe take.

Lallai yayin da mutane s**a fifita tsoron duniya a kan ta Lahira babu shegantakar da Iblis ba zai dora su a kai ba, kuma lalacewar al'umma ta Z
zama tabbas.

Allah Ya kare mu da zuriyarmu.

24/11/2025
KARANTA KA DAUKI DARASI ACIKIImamu Abu Hanifa (Allah ya ƙara masa yadda) ya wuce ta gaban wasu mutane, sai yaji suna cew...
20/11/2025

KARANTA KA DAUKI DARASI ACIKI

Imamu Abu Hanifa (Allah ya ƙara masa yadda) ya wuce ta gaban wasu mutane, sai yaji suna cewa, wannan shi ne Nu'uman, duk daren duniya ƙiyamul layli yake yi, baya barci.

Imam Abu Hanifa ya ce, lokacin da s**a faɗa barci nake yi, bana tashin dare amma wallahi tun da naji maganarsu na ce, dama haka mutane suke kallona kuma suke tsammanin nake, wallahi daga yau ba zan sake yin barci ba.

Imam ya ce, babban abin kunya ne mutane su baka siffofin d s**a kusanta ka d Allah amma kai kasan ba haka ba ne.

In mutane suna tsammanin kai mutumin kirki ne to yana da kyau ka dage, domin babban abin kunyar shi ne aje Lahira suga akasin kyautata maka zaton da s**a yi.

Allah kasu mu wanye lafiya ameen ya hayyu ya kayyum

20/11/2025

Wayewar gari dama ce Ubangiji ya baka domin gyara abin da ka yi sakaci akai, Allah ka bamu ikon gyara kuskuren mu amin.

Address

Abubakryunusauyo@mail. Com
Jigawa
336699

Telephone

+2349072412720

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shaykhul lslam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share