12/08/2022
ILLAR SIYASA BA SANA'A.
Matasa ana lalata mana yau da goben mu da ta bayan mu sakamakon
rashin dogaro da kai.
Babu laifi ayi ra'ayin siyasa amma arike sana'a domin itace zata baka
damar fadan gaskiya da bujirewa karya ga shugabannin mu da
'yansiyasar mu.
Yana daga cikin rashin sana'a da kwadayi da tsammani da karbar na
goro a hannun su ke sawa a gaban ka zasuyi ba daidai ba amma hakan
zaka bisu suna kan kuskuran kasani idan kafada zaka rasa dubu dayan
da suke baka.
Rashin sana'a da yasa kake binsu tin baka shaye shaye idan bakayi
wasa ba sai kafara domin sukan iya siyan kayan maye amma baza su
baku jari ba domin idan kazama mutum waye zai bisu?waye zaina tare
musu fada?amma idan kafara maye sun san zuciya ta mutu dari biyu
ma ta ishe ka baka bukatar abinda zaka dogara da kanka.
'Yan siyasa sun kirkirawa matasa rashin sana'a don biyan bukatar
kansu don haka dole fadar gaskiya tayi wahala domin akan dari biyun
da Honourable zai bada sai aci mutuncin mai mutunci.
daga cikin wanda yake fadawa matasa gaskiya yake musu gargadi
akan sana'a sabanin sauran 'yansiyasa da dama.
Allah ya ganar da matasan mu su samu sana'a,suyi siyasa don ra'ayi
badan yunwa da neman na maye ba.