13/07/2021
CHAIRMAN KOLA SARAWA KO MAKAHO YAYI MASA SHAIDA TAGARI
Hausawa sunce Juma'an da zata yi kyau tun laraba ake gane ta lallai tuni al'umma masu tunani da sanin ya kamata shaida ne akan alherin mai girma Chairman Alh Saminu Kola Sarawa abisa irin halin sa na dattaku. Alh Saminu Kola Sarawa yayi ayyukan alheri da har a yanzu al'umma suna ganin amfanin sa. Saidai wanda ya saninya sani, wanda bai sani ba bai sani ba shikenan kawai. Mu iya binciken mu Alh Saminu Kola Sarawa babu wanda yakai mana shi a daidai wannan zamanin saboda irin hali na tausayi, da taimakon al'umma da kuma son cigaban kowani talaka a rayuwa. Kullum shine abin alfaharin mu ko da yaushe bamu da wanda yafi mana shi mukam wallahi.