02/06/2021
*LABARAI A TAKAICE*
*TABARBAREWAR TSARO TA ZAMA BABBAR JARRABAWA GA KOWA A NAJERIYA-BAFARAWA*
*Tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nuna matukar damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, ya na mai cewa kalubalen ya wuce matsayin a tsaya a na dorawa gwamnati laifi don sai kowa ya yi tsayin daka kafin a samu saukin da a ke bukata.*
*Alhaji Attahiru Bafarawa wanda ke zantawa da Bashir Ibrahim Idris na rediyon Faransa, ya ce sai da ‘kasa kowa zai iya tabuka wani abu, don in ba kasar ba amfanin duk wata kujerar mulki. Yayin da ya ke nuna takaicin yanda barayi da 'yan bindiga kan samu kyaliyar talakawa wajen huldar cinikayya kamar kai fetur ko katin waya, ya ce kowa na da na sa laifi da sai an taru gaba daya an yi gyara don samun maslaha.*
*Dan jaridar ya nemi jin ko Bafarawa na kare gwamnati ne?, a nan bayanan na Bafarawa na nuna an wuce matsayin zargin wani ko masu mukami, kowa sai ya kula ya ba da tasa gudunmawar don ceto musamman yankin arewacin Najeriya da illar da ta'azzara.*
*SHUGABA BUHARI YA NADA BABAGANA KINGIBE A MATSAYIN JAKADAN CHADI DA TAFKIN CHADI*
*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada ambasada Baba Gana Kingibe a matsayin jakadan musamman na Najeriya a Chadi da kuma lamuran kasashen yankin tafkin Chadi don kula da lamuran tsaro da dimokradiyya. A sanarwa daga sakataren gwamnatin Boss Mustapha, ta ce Kingibe zai kula da dawo da mulkin dimokradiyya daga na soja a Chadi.*
*Hakanan jakadan zai rika tsara hada kan kasashen ga lamuran tsaro a madadin matsayin Najeriya mai muhimmanci a yankin. Kingibe wanda marigayi shugaba 'Yar'adua ya kwabe daga matsayin sakataren gwamnati ya nada Yayale Ahmed, ya zama mukarrabin shugaba Buhari da sauran manyan masu ba da shawara ga gwamnatin.*
*KUNGIYAR TUNTUBAR JUNA TA AREWA TA SHAWARCI 'YAN AREWA SU TAKAITA TAFIYA KUDU*
*Kungiyar tuntubar juna ta arewa ACF ta bukaci al'ummar arewa su dakatar da duk wata ziyara kudu musamman kudu maso gabar in ba ya zama dole ba. ACF da nuna takaicin