Hausa Novels Only

Hausa Novels Only You will be happy as long as you are with us because we will always bring you the latest breaking ne Typically replies within an hour Send Message

08/09/2025
03/09/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Ibrahim Babandada Hureerat, Billy Uthman, Al-Qasim Bin Usman Lau

An Zargi Wata Mata Da Ka*she Mijinta, Duk Da Cewa Ba'a Ga Gawarsa Ba, Haka Aka Yanke Mata Hukuncin.  Shekaru Masu Yawa B...
02/09/2025

An Zargi Wata Mata Da Ka*she Mijinta, Duk Da Cewa Ba'a Ga Gawarsa Ba, Haka Aka Yanke Mata Hukuncin. Shekaru Masu Yawa Bayan Kammala Zaman Gidan Yari, Ta Gano Cewa Mijin Nan Nata Yana Raye Ya Gudu Can Wani Gari Yayi Aure Da Wata Mata.

Taje Har Garin Da Yake Ta Harb*e Shi Kuma a Take Ya Mutu a Wannan Karon Ma Aka Sake K**a Matar Da Laifin K!san Kai Ga Mijin Nan Nata.😱

Amatsayinka Na Alkali Ya Zakayi Da Matar Nan.?
Zaka Kalli Lamarin Amatsayin Sabon K!san Kai Kayi Mata Hukunci Ko Kuwa Zaku Kalli Cewa Laifin Da Tayi Ta Riga Ta Karɓi Hukuncinsa?

Lauyoyin Dake Sahar Nan Don Allah Kuyi Mana Ƙarin Haske Akan Case Ɗin Nan!.

Abba Hikima
Barr Badamasi Suleiman
Audu Bulama Bukarti
AUDU BULAMA BUKARTI
Aisha Abubakar Ramalan

BASADAUKIYA Littafi Na Daya (1)Part B. Na Abdulaziz Sani M GiniAA Misau Ke Magana(Barkanmu da wannan lokaci Yan uwa)Ya t...
04/05/2024

BASADAUKIYA
Littafi Na Daya (1)
Part B.
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau Ke Magana

(Barkanmu da wannan lokaci Yan uwa)

Ya tafi taga-taga zai kife da fuskarsa, sai da ya dage iya
Karfinsa sannan ya iya tsaida kansa. A lokacin ne
sauran dakarun da ke kewaye da ita s**a zare mak**ai
s**a yunkura za su afka mata. Amma sai s**a ji
Husaru ya daka musu tsawa yana mai basu umarnin su
dakata. Gaba dayansu sai s**a tsaitsaya. Husaru ya
mike tsaye ya juyo ya dubi matar Mujahid cikin
tsananin mamaki, domin wannan ne karo na farko da
wani mahaluki ya taba samun damar murde hannunsa
bare ma har a kusan kaishi kasa. Babban abin da ya
jefa Husaru cikin takaici shi ne 'ya mace ce ta
wulakantashi haka a gaban dakarunsa wadanda s**a
tabbatar da jarumtakarsa.
Husaru ya zare takobinsa ya durfafi matar
Mujahid gadan-gadan. Koda ganin haka sai itama ta
zare wata takobi da ke rataye a kafadarta ta nufeshi ba
da shakkar komai ba. Sai da ya rage saura baifi taku
uku ba su hadu sai kawai aka ga Mujahid ya dako
tsalle ya dira a tsakiyarsu. Nan fa aka fara kallon-kallo
tsakanin Mujahid da Husaru. Ita kuwa matar Mujahid
sai ta koma gefe daya ta zauna tana lura da motsin
sauran dakarun.
Mujahid da Husaru s**a fara zagaya juna
kowannensu na lura da motsin dan uwansa, ko kifta
idanu ba sa yi. Kai da gani ka san cewa kowannensu
ya kware a iya yaki, kuma sun san mak**a da lago.
Bayan sun zagaya juna k**ar sau uku sai s**a
kacame da azababben yaki, suna masu kaiwa juna sara
da s**a cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta
tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane
Sai da s**a shafe lokaci mai dan tsawo a haka
dayansu bai sami nasarar komai ba. Koda ganin haka
sai Mujahid ya sauya salon fada ya fara tsalle-tsalle da
yin alkafira a sama tamkar ba ya jin nauyin jikinsa, ko
kuma yana da fuka-fukai irin na tsuntsaye
Nan da nan Mujahid ya fara rikirkita Husaru ya
zamana cewa yana shawagi a samansa tamkar baiyanar
walkiya da bacewarta. Nan fa ya zamana cewa Husaru
baya iya mai da martani sai kokarin kare kai. Babban
abin da ya tayarwa da Mujahid hankali shi ne duk
sa'adda ya sari jikin Husaru sai yaji k**ar dutse ya
sara. Shi kuwa Husaru ya kasa taba jikin Mujahid.
Lokacin da wannan gumurzu nasu ya kara
tsamari, sai Husaru ya fara amfani da karfin sihiri yana
watsawa Mujahid wuta, kibiyoyi da tsitakoki, amma
sai ya ga wadanann mugayen abubuwan sun kasa tasiri
a jikin Mujahid. Ba komai ne ya haddasa hakan ba
face addu'ar da Mujahid ya fara yi. Al'amarin da ya
dugunzuma hankalin Husaru ke nan, ya tabbatar da
cewa yau fa watan jin kunyarsa ya k**a, don haka sai
ya kara zage dantse iya karfinsa yana kokarin ya kai
Mujahid kasa da Karfin tsiya. Shi kuwa Mujahid ya ki
Zuwa kasan.
Bisa mamaki Sai Mujahid ya ga ya sami nasarar
yankar jikin Husaru a cinya har jini ya zuba. Cikin
razana Husaru ya ja da baya yana mai dafe raunin ya
Kurawa Mujahid idanu ciki mamaki. Ashe ba wani abu
bane ya janyo samun Wannan nasara ba face addu'ar da
Muiahid ya fara karantawa a ransa, wacce ta tarwatsa
sirrin tsafin Husaru.
Ya yin da sauran Dakarun s**a ga Mujahid ya
sami Wannan nasara akan shugabansu sai s**a taso
gaba dayansu s**a afka masa.
Wohoho! Nan fa wuri ya sake yamutscwa. Koda
Matar Mujahid ta ga an yiwa mijinta rubdugu sai ta
yunkura da nufin ta kawo masa dauki, amma sai ya yi
ma ta nuni da kada ta zo, baya bukatar agaji, don haka
sai ta koma tayi zamanta. Shi kuwa ya ci gaba da
fafatawa da su ya zamana cewa ya zame musu
alakakai. Abin da ya daurewa dakarun kai shi ne baya
son ya cutar da su, amma sai yai ta bugunsu yana
zubar da su kasa. Nan da nan Mujahid ya fara yin laga-
laga da su, sai gasu a zube kasa magashiyan sun kasa
tashi. Koda ganin haka sai Husaru ya yi kururuwa
cikin matukar fishi yai įifa da takobin hannunsa ya
rugo izuwa kan Mujahid da mugun nufi. Koda matar
Mujahid ta hango abin da ke shirin afkuwa ta tabbatar
da cewa idan har Husaru ya riski mijinta zai iya yi
masa mugun lahani, sai kawai ta daka tsalle a sama
daga inda take zaune tana mai karanta wata addu'a. Sai
ta tafi shuuu! K**ar an cillata daga cikin baka. Kawai
sai agni aka yi ta doki kirjin Husaru da kafafunta biyu.
Take Husaru yai samna tamkar an cillata daga cikin
baka. Kawai sai gani aka yi ta doki kirjin Husaru da
kafafunta biyu. Take Husaru yai sama tamkar an
janyeshi da kugiya yaje ya manne a jikin ginin rijiyar
nan ya sulale kasa sumamme, jini na zuba ta cikin
hanci da baki.
Koda ganin abin da ya faru sai ragowar dakarun
nan dake zube a kasa a galabaice s**a mike zumbur
s**a tsere. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face basu
taba ganin mutumin da ya taba kai Husarukasa ba, sai
yau. Babban abin mamakin ma shi ne, ya mace ce ta
kaishi kasa.
Bayan gaba daya Dakarun sun gudu sai Mujahid
ya dubi matarsa yai murmushi ya ce "Yake Sakinat
mu yi sauri mu kada Rakumanmu izuwa cikin kasuwa
mu nemi masauki tun kafin a sake turo wadansu
dakarun da za su yiwa dukiyarmu barna".
Koda jin wannan batu sai Sakinat ta dubi mijinta
cikin matukar damuiwa ta ce, "Ai ni abin da nake tsoro
ma shi ne, za a iya binmnu har cikin kasuwar a kashe
mana Rakuma kuma a kwashe mana haja."
AA Misau ke magana
Koda jin haka sai Mujahid yai murmushi ya ce,
"Kada ki damu ya matata, ai addu'a makamin
muminice, mu ci gaba da yin addu'a da yardar Allan
babu abin da zai samemu ko dukiyarmu".'
Koda gama fadin haka sai Mujahid ya kada
Rakuman, Sakinat ta taimaka masa s**a nufi hanyar
Masu iya magana sun ce idan ka je gari ka ga
jama 'ar garin na da jela, kaima sai ka nemi tsumma ka
daura, domin ka zauna lafiya ba don kana so ba.
Lokacin da Mujahid da Sakinat s**a iso kasuwa,
sai ya lura cewa mutanen birnin masu kwadayi ne
matuka da son abin duniya. Sabo da Mujahid yana son
Rakumansa da dukiyarsa su tsira sai ya kira Sarkin
kasuwa gefe ya yi masa alheri na dinare dari ya ce da
shi, yana da rakuma guda dari uku da sittin da biyu,
yana neman wurin da zai adana wadannan rakuma da
hajojinsu, inda babu wanda zai iya yi masa 6arna".
Koda jin wannan batu sai Sarkin kasuwa ya ce,
"Shi yana da wuri mai matukar sirri, amma nawa zai
biyashi ya yi masa gadin dukiyar tasa?". Mujahid ya
ce, "Zan baka dinare dari biyar". Sarkin kasuwa ya ce,
"A'a ba zan karbi hakan ba, domin wannan aiki da zan
yi maka mai hadarin gaske ne. Na sani cewa baka kai
dukiyarka gaban Sarauniya ba, domin inda ka kaita da
tuni ta rabaka da rabinta, al'adarta ke nan. Idan
Sarauniya ta fuskanci cewa ni ne na 6oye maka
dukiyarka za ta iya sawa a kaini kurkuku kuma a
rabani da duk abin da na mallaka. Idan har kana son na
boye maka wannan dukiya sai dai ka biyani dinare
dubu uku. Kuma ka sani cewa kai kanka da wannan
matar taka kuna cikin hadari, dole ne kuma ku buya".
Koda jin haka sai Mujahid ya cika da
mamaki
,"To wai shin ita wannan Sarauniya taku wace irin
dabi'ace da ita ne? Bayan ta kwacewa mutum dukiya
kuma shima sai ta zalunceshi?".
Sarkin kasuwa yai ajiyar zuciya sannan ya ce,
"Ya kai wannan bako, kayi sani cewa duk da ban ga
fuskarka ba a yanzu na fahimci cewa kai kyakkyawa
ne, haka ma matarka, domin da idanunku kawai na
lura da hakan. Kuyi sani cewa Sarauniyarmu batau
taba yin aure ba, kuma bata taba haihuwa ba, amma
tana da wata muguwar dabi'a wadda duk sa'adda ta ga
saurayi kyakkyawa sai tayi lalata da shi, sai ta sa
akaishi wani kurkuku mai suna Sijinil Maut a tsareshi
đaurin rai da rai. Tabbas idan Sarauniya tayi arba da
kai sai hakan ta faru gareka.
Ita kuwa wannan kyakkyawar mata taka ta zama
kuyangarta ke nan mai yi ma ta hidima."
Koda Mujahid da Sakinat s**a ji wannan batu,
sai hankalinsu ya dugunzuma. Sabo da haka sai s**a
amince da bukatar sarkin kasuwa s**a bashi dinare
dubu uku. Nan take sarkin kasuwa ya sa aka kada
Rakuman su Mujahid izuwa cikin wani katon kango.
Bayan Rakuman sun gama shiga sai aka rufe kofar
kangon ya zamana cewa daga sarkin kasuwa sai su
Mujahid ne kadai a cikin kangon, wato su uku rak.
Kawai sai s**a ga sarkin kasuwa ya shiga daga wasıu
dammai na ciyawa. Gama yin haka ke da wuya sai ga
murfin wata tsohuwar rijiya mai fadi sosai. Sarkin
kasuwa ya bude wannan murfin rijiya sai ga hanya
azururu izuwa gidan kasa. Sarkin kasuwa ya k**a
akalar Rakumin da ke kan gaba ya jashi izuwa cikin
wannan gida na karkashin kasa yana mai cewa da su
Mujahid, "Ku koro ragowar Rakuman su biyo
bayanmu". Ba tare da wata gardama ba s**a bi wannan
umarni. Kawai sai tsintar kansu s**a yi a cikin wani
wangamemen gida mai yalwar fadi da dakouna
barkatai, har da rijiya. Kuma ga wasu hadiman mata su
bakwai suna ta dan aikace-aikace. Al'amarin da ya
đaurewa Mujahid da matarsa Sakinat kai ke nan, s**a
cika da mamaki, domin basu taba tsammanin wajen zai
kasance haka ba.
Koda Hadiman matan nan su balkwai s**a hango
sarkin kasuwa janye da Rakuma da kuma baki sai s**a
tarbeshi cikin murna. Nan take s**a taimaka masu
wajen kora rakuman izuwa cikin babban filin s**a
zazzaunar da su kasa, sannan s**a shiga sauke hajojin
da ke kansu. Babu abin da ya kara baiwa su Mujahid
mamaki face yadda matan bakwai s**a zage damtse
suke aiki tamkar ba mata ba. Sai da aka kallama sauke
kayan gaba daya, sannan Sarkin kasuwa ya yiwa su
Mujahid jagora izuwa wani đaki mai kyau wanda aka
shimfida kilishi mai taushi a cikinsa. Da shigarsu cikin
dakin sai s**a zauna su ukun sannan daya daga cikin
hadiman matan nan ta kawowa su Mujahid abinci mai
kyau gami da ruwan sha ta ajiye a gabansu ta fita.
Fitarta ke da wuya sai Sarkin kasuwa ya dubi
Mujahid ya ce, "Ya kai wannan attajirin bako ku saki
jikinku kai da matarka, kuyi zamanku anan cikin
kwanciyar hankali, kada ku kuskura ku fita waje har
Izuwa gobe da safe, sa'adda kasuwa za ta fara ci. A
goben ma ku 6atar da k**anninku sosai. Ka
shawartawa matarka tayi zamanta anan in ya so kai ka
fita ka siyar da hajarku. Ina mai dada shawartarka da
hajar ta ka ma a rinka fita da ita da kadan-kadan har ta
kare, domin tabbas Sarauniya za ta turo nemanku da
dukiyarku. Yanzu dai ku abni labari mene ne ya faru
tsakaninku da Dakarun Sarauniya?".
Koda jin wannan tambaya sai Mujahid da Sakinat
s**a dubi juna, sannan Mujahid ya ce, "Yanzu wane
tabbaci za ka bani cewa ba za ka ci amanarmu ba ka
tona mana asiri?".
Sarkin kasuwa ya yi murmushi ya ce, "Babban
tabbaci shi ne abin da na yi muku yanzu. In da ina son
na tona muku asiri da ban baku mafaka kun 6uya ba ku
da dukiyarku. Abin da na ke so ku fahimta shi ne, gaba
daya mutanen wannan birni namu bama kaunar
zaluncinta da rashin tausayinta ga kowa. Ni kaina din
nan duk bayan kwana talatin sai na biya haraji mai
soka Na taimake ka ne ba don komai ba sai domin
dukiyarka".
Sa'adda Sarkin kasuwa ya zo nan a zancensa sai
Mujahid ya yi murmushi da godiya a gareshi, sannan
s**a yi sallama ya fita ya barsu su biyu rak a wannan
đaki.
Fitar Sarkin kasuwa ke da wuya sai Sakinat ta
dubi mijinta Mujahid cikin damauwa ta ce, "Ya kai
mijina ni fa hankalina atashe yake bisa jin dabi'ar
wannan Sarauniya akan kyawawan samari. Ina tsoron
kada ta sami nasara akanka".
Koda jin haka sai Mujahid ya cire rawanin kansa
ya taso daga inda yake zaune ya dawo inda take ya cire
nata rawainin s**a dubi kyawan fuskokinsu, sannan ya
yi murmushi a gareta ya ce, "Kwantar da hankalinki ya
abar kaunata da izinin Allah babu abin da zai faru
gareni. Kin sani cewa addu'a makamin mumini ce, don
haka Allah zai karemu daga dukkan sharrin wannan
mata."
Ya yin da Sakinat taji haka sai farin ciki ya
shigeta ta rungume Mujahid tana mai sumbatar
goshinsa ta ce, "Hakika ka gama magana ya mijina,
tabbas addu'a ce maganin fasikan wannan zamani.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Mujahid
da matarsa Sakina bayan Sarkin kasuwa ya boyesu tare
da dukiyarsu a cikin gidan kasuwa wanda ya kasance
boyayye.

A CAN FADAR Sarauniya Dulaiba kuwa,
Lbayan k**ar sa'a daya da fitar Sarkin yaki
Hasaru sai ga daya daga cikin dakarunsa ya shigo
cikin fadar jina-jina yana tafiya yana layi. Al'amarin da
ya razana gaba dayan jama'ar da ke cikin fadar ke nan,
s**a mimmike tsaye. Ita kanta Sarauniya Dulaiba bata
san sa'adda ta mike tsaye ba.
Badakaren ya isa daf da karagar Sarauniya
Dulaiba, sai ya yanke jiki ya fadi yana numfashi da
kyar, sannan ya bude baki a cikin matukar karfin halí
ya ce, "Ya shugabata kiyi sani cewa yau wasu
hatsabiban baki ne s**a shigo wadanda s**a kasance
sadaukai na gaban kwatance su biyu mijii da mata. A
halin yanzu sun sumar da Sarkin yaki Hasaru da
dukkanin dakaru dubun da yaje da su. Bayan mun
farfado ne. duk muka tsere muka nausa cikin gari a
firgice ni kadai ne ban rude ba nayi tunanin na dawo
nan na bada labari".
Sa'adda Badakaren ya zo nan a jawabinsa sai
zuciyar Sarauniya Dulaiba ta k**a tafarfasa tamkar za
ta konc, sabo da bakin ciki. Cikin tsananin fushí ta
dubi boka Gaihar ibni Sabbur ta ce, "Ya kai abin
dogarona, maza kayi bincike ga gano mini inda
wadannan baki suke a yanzu, kuma ko ta yaya ina son
muje yanzu ni da ku mu kamosu".

Topah Nima A A Misau a nan zandakata saikuma wani Lokaci

Karku manta zaku iya binmu a WhatsApp group dinmu wanda zaku dinga samun LITATTAFAN yaki dana soyayyah harda Na nishadi 👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Sannan a Facebook ma haka
Zaka iya samunmu a wadannan shafuka

Saikunzo
AA Misau Ke Magana

BASADAUKIYALittafi Na Daya (1)Part A.Na Abdulaziz Sani M GiniAA Misau Ke Magana (Ku Cigaba da binmu ta WhatsApp group di...
29/04/2024

BASADAUKIYA
Littafi Na Daya (1)
Part A.
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau Ke Magana

(Ku Cigaba da binmu ta WhatsApp group dinmu na ZAURAN LABARAI HAUSA NOVELS domin samun litattafan yaki Dana soyayyah harda Na nishadi)

Marubucin Littafin Ya Fara da cewa...

A WANI zamani can baya mai tsawo da ya shude, a birnin Askandariya, anyi wata
shahararriyar sarauniya mai suna DULAIBA.
Sarauniya Dulaiba ta tara zaratan mayaka ababan
tsoro, masu dumbin yawa, ga kuma kwarjini, har ana
vi musu lakabi da 'DAKARUN AZABA' Ba komai ne
yasa ake kiransu da wannan suna ba face tsananin
rashin imaninsu. Haka kawai idan Sarauniya Dulaiba
ta bushi iska sai ta tura dakarun ta izuwa cikin wasu
garuruwan su kai farmakin kwace dukiya da bayi. Duk
mutumin da ya yi gardama wajen bayar da dukiyarsa
take suke kashe shi. Sun mai da ran dan adam tamkar
na kiyashi.
Zaluncin Sarauniya Dulaiba bai tsaya akan maza
ba kadai, hatta mata bata raga musu, kuma ko ya ya
mutum ya yi ma ta laifi bata san afuwa ba. mafi saukin
hukuncin da take yi shi ne kisa. In kuwa ta so rashin
imani sai ta sa.a yi ta ganawa mutum azaba iri-iri
kullum har wahala ta zamo sanadin ajalinsa.
Gaba daya mutanen birnin Askandariyya suna
matukar tsoro da shakkar Sarauniya Dulaiba. Su kansu
attajiran kasar da sarakai makusantanta kullum a cikin
lallabata suke suna fadanci da bata kyautar dukiya domin su zauna lafiya.
Sarauniya Dulaiba bata taba yin aure ba, kuma bata
taba haihuwa ba, gata ta kasance kyakkyawar mace
abin kwatance. Tana da wata muguwar dabi'a wadda
duk sa'adda ta ga kyakkyawan saurayi sai ta sa a
kamoshi ta biya bukatarta da shi da karfin tsiya, daga
nan sai ta sa a kaishi wani kurkuku na musamman a
tsareshi đaurin rai da rai. Shi dai wannan kurkuku ana
yi masa lakabi da SIJNIL MAUT. Duk furfusan da aka
kaishi wannan kurkuku bai isa ya gudu daga cikinsa
ba, sai dai a fitar da gawarsa sabo da tsananin tsaron da
ke cikin kurkukun.
Shi dai kurkukun an gina shi ne a cikin karkashin
kasa da duwatsun wuta. Kofofinsa gaba daya an yi su
ne da wani murtukcken katfe wanda aka tabbatar da
cewa lu'u-lu'u ne kadai ya fishi kwari.
Masu gafin kurkukun kuwa, Dakaru ne zabab6u,
kuma zakwakuran dakaru guda dubu saba'in masu
kirar samudawa. Mak**ansu ma kadai abin kallo ne,
domin ba karamin kato ba ne zai iya daga su.
Sarauniya Dulaiba na dogaro da wani
gawurtacccn boka wanda ya kasance hatsabibin gaske
ana kiransa da suna GAIHAR IBINI SABBUR. A
gaba daya nahiyar babu boka tamkarsa. Kuma shi ne
wanda ya hana Sarauniya Dulaiba yin aure, kuma ya
haneta da samun ciki, domin ya tabbatar mata da cewa
duk ranar da ta samu ciki to fa sai ta haifi abin da zai
zamo sanadin ajalinta. Bisa wannan dalili ne yasa ya
bata wani sihirtaccen magani ta sha wanda har abada
ba za ta taba samun juna biyu ba.
A kalla Sarauniya Dulaiba ta tara da samari guda
dubu wadanda duk rayuwarsu ta kare a kurkukun
Sijinil Maut. Sarauniya Dulaiba tafi shekara ashirin da
biyar tana wannan muguwar dabi'a tata, wanda har ta
kai cewa labarin dabi'ar tata ya bazu ko ina a nahiyar.
Hakan yasa duk wani saurayi wanda ya kasance
kyakkyawa yana boye kansa. Kai ko bako ne saurayin
da zarar mutane sun ganshi ya shigo nahiyar sai su
bashi shawarar ya koma inda ya fito.
Bisa dokar Sarauniya Dulaiba duk bakin da s**a
shigo cikin birnin Askandariyya ba a barinsu su sauka
a ko ina sai an kaisu fadarta sun gabatar da kansu,
kuma sun fadi abin da s**a zo yi a kasar. A wannan
lokaci kouwa birnin Askandariyya cibiya ce ta
kasuwanci, don haka kusan kowanne wata guda babbar
kasuwar garin ke ci. Bisa ga haka ne Fatake suke cika
birnin.
Wajibi ne kowanne Bafatake yaje ya yi gaisuwa a
fada, kuma ya biya wadansu kudi da aka gindaya. ldan
kuwa mutum ya yi kuskuren kin biyan wadannan kudi
sai azo har kasuwar ayi masa dukan tsiya, sannan a
kwace duk dukiyarsa a kaiwa Sarauniya Dulaiba. Idan
ma bashi da sa'a sai Sarauniya Dulaiba ta ce a k**ashi
a kaishi kurkukun Sijinil Maut, koda kuwa ya kasanco
mace ba namiji ba.
Bisa wannan al'ada ce, wata rana wani bakon
Bafatake mai suna MUJAHID tare da matarsa s**a
shigo cikin birnin Askandariyya tare da hajar kaya bisa
rakuma dari uku da sittin da biyu. Babban abin da
ya
daurcwa jama'a kai ya jefasu cikin tsananin mamaki
shi ne duk yawan wannan dukiya da Mujahid ya taho
da ita babu dakaru masu tsaronta, daga shi sai matarsa.
Shin ya ya aka yi s**a ratso ta cikin muggan
dazuzukan da ke kun hanya ba tare da 'yan fashi sun
kwace dukiyar ba sun rabasu da rayuwarsu? Wannan
tambaya ce wadda babu wanda ya san amsarta.
Lokacin da Mujahid da matarsa s**a iso kofar
birnin Askanadariyya sai masu gadin kofar kimanin
dakaru dari s**a taresu. Ba tare da gardamar komai ba
Mujahid yaja akalar Rakuminsa ya tsaya cak, take, suma
sauran dukkanin akuman dakc biye da su sai s**a
tsaya cakjere cikin sahu tamkar sun ji umarnin da
aka baiwa maigkdansu.
Shugabarnasu gadin wani narkcken kato
mummunan gaske, ya zo gaban Rakumin Mujahid ya
kalleshi ya ce, "Ya kai wannan bako, kai waye, kuma
daga ina ka fito? Kayi sani cewa ba zamu barka ka
shiga cikin gari ba face ka gabatar da kanka, kuma
mun kaika fada wajen Sarauniya ka biya jiziya".
Koda jin wannan batu sai Mujahid ya sauko daga
kan Rakuminsa, a wannan lokaci fuskar Mujahid da ta
matarsa a rufe take cikin rawani. jdanunsu kadai ake
AA Misau Ke Magana
gani, Ko idanun nasu kadai mutumn ya gani ya isa ya
tabbatar masa da cewa kyawawan mutane ne
Mujahid ya zo daf da narkeken katon ya tsaya
Yadda suna iya jin numfashin juna, sannan ya ce, "Ya
kai, wannan mai gadi, kayi sani cewa ni ma'abocin
addinin musulunci ne, don haka ba zamu biya jiziya ba
ga kafirai irinku.
Tambaya daya zan iya amsa maka daga cikin
tambayoyinka. Mun fito ne daga birnin Misra, kuma
ba komai ne ya kawomu wannan birni ba face siyar da
hajarmu. Babu wata hujja da za ta sa ku ce sai mun
gabatar da kanmu a gareku ko kuma sai mun je gaban
Sarauniyarku. Ina mai shawartarku da ku kyalemu mu
wuce abin mu mu nemi inda kasuwa take domin nance
masaukinmu".
Koda gama wannan jawabi sai Mujahid ya zare
takobi yana wani irin huci k**ar zai ci babu.
Al'amarin da ya janyo hankalin sauran Dakarun ma
s**a zare mak**ansu. Shi kuwa Mujahid ko gezau bai
yi ba sai ya tsaya cak yana kallonsu kawai. Haka itama
matar Mujahid wadda ke zaune bisa Rakumi ko alamar
firgita babu a tare da ita.
Shugaban dakarun ya dakawa Mujahid tsawa ya
ce, "Kai! karamin alhaki, wane ne kai bar da za ka yı
mana gardama? Maza ka koma kan Rakuminka ka
zauna, kuma ka bi umarninmu ko kuma yanzun nan ka
zama gawa".
Koda jin wannan batu sai Mujahid ya juya da
baya k**ar ya saduda zai bi umarni. Ba zato ba
tsamanni sai ya juyo cikin tsananin zafin nama da
shammace va ciccibi wannan katon mai gadi da hannu
daya jal ya dagashi sama tamkar ya daga sullen kara
ya cillashi sama tamkar kugiya aka zuro daga sama
aka janyeshi. Sai ga narkcken kato ya luluka sama,
sannan ya fado kasa timn k**ar giwa ta fadi. Dai-dai
inda ya fado fin yai rami kai ka ce hakawa aka yi,
kuma kura ta turnuke wajen gaba daya. Sabo da
tsananin mamakin jarumtakar Mujahid, sai sauran
abokan aikin katon maigadin s**a kame s**a kasa
motsi, s**a zuba masa idanui kawai a lokacin da
shirgegen shugaban na su ya sume.
Cikin fushi Mujahid ya dubi wadannan dakaru ya
ce, "Ku gafara ku bamu wuri mu wuce ko kuma abin
da ya sami shugabanku ya tabbata a kanku gaba daya".
Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun
s**a dare s**a samar da hanya jikinsu na tsuma. Ba
tare da fargabar komai ba Mujahid ya haye kan
Rakuminsa ya wuce ta tsakiyarsu, Rakumin matarsa
da sauran Rakumansu na hajoji na biye da shi s**a
nufi hanyar da ta nufi cikin gari.
A ka'ida duk sa'adda baki s**a shigo cikin gari
dole ne a gansu tare da Dakarun Sarauniya wadanda za
su yi musu jagora izuwa fadar Sarauniyar, amma
wannan karon sai aka ga wadansu baki sun shigo gari
babu wakilan Sarauniya a tare da su. Nan fa jana'a
s**a kyamaci su Mujahid don gudun koda su shafa
musu kashin kaji. Duk wanda s**a tsayar don su yi
masa tarnbaya sai ya ki saurarcnsu. Wasu na sai su
take da gudu. Kai hatta ruwan sha ma hanasu aka yi
S**a rasa inda za su bi su isa kasuwa. Al'amarin da ya
daure musu kai ke nan. Duk kofar gidan da s**a dosa
da an hangcsu sai ayi sauri a rufe kofar gidan.
Al'amarin da ya matukar basu mamaki ke nan, gashi
Kishirwa ta addabesu su da Rakumansu. Bisa dole s**a
nufi bakin wata rijiya inda jama'a s**a yi dandazo
suna dibar ruwa.
Koda jama'ar dake rijiyar s**a hango tahowar su
Mujahid sai duk s**a tarwatse s**a tsere, bakin rijiyar
ya zamo wayam tamkar mutane basu taba wanzuwa ba
a wajen. Mujahid da Rakumansu s**a karasa bakin
wannan rijiya s**a tsaitsaya sannan s**a sauko shi da
matarsa daga kan Rakuma.
Shi da gugan wannan rijiya ya kasance katon
gaske wanda za a iya sanya mutum uku a cikinsa.
Sannan igiyar da aka daura a jikinsa tsawonta ya isa
sabo da tsananin zurfin rijiyar, sabo da haka sai k**ar
karti goma sun taru suke iya janyo ruwa daga cikin
rijiyar, kuma kafin su gama janyo guga daya sai su
6ata sama da dakiku dari uku. In aka janyo guga daya
na ruwan daga cikin rijiyar sai a zubashui a cikin wata

# # # # # #

AL'AMARIN Dakaru kuwa masu gadin kofar
Abirnin, koda s**a ga abin da ya faru
ga
shugabansu sai s**a yi sauri s**a yayyafa masa ruwa
Ya farfado daga Suman da ya yi bisa cillashi sama da
Mujahid ya yi ya fado kasa. Ai kuwa yana farfadowa
sai ya mike zaune a firgice ya dubesu sannan ya waiga
gabas da yamma, kudu da arewa ya ce, "Ina wadannan
shaidanun baki s**a yi? Wai shin mene ne ya faru
gareni?"
AA Misau Ke Magana
Koda jin wannan tambaya sai dariya ta kwacewa
sauran dakarun, amma da ya daka musu harara sai duk
s**a shiha taitayinsu. Kawai sai shugaban Dakarun ya
mike tsaye da sauri yana mai karkade kurar jikinsa
cikin alamun borin kunya sannan ya nufi wata hanya
dabam wadda za ta kaishi izuwa fadar birnin. Cikin
hanzari sauran dakarun s**a bishi duu a baya tamkar
kaza da 'ya'yanta.
Gidan sarautane kasaitacce wanda aka yi matukar
kawatashi da kayan alatu irin su lu'u-lu'u, jauhar,
murjani, da sauransu. Girman gidan ya kai na wani
birni guda, dormin sai da wadannan dakaru s**a shafe
rabin sa'a suna keta kofofi har guda tara sannan s**a
iso wangamemiyar fadar da Sarauniya Dulaiba ke
zaune, fadawanta sun kewayeta, kuma ga sauran
jama'ar gari ana tafiyar da harkokin mulki. A wannan
lokaci kuyangi sun baibaye karagar sarauniya Dulaiba,
Wasu na yi ma ta firfita, wasu tausa suke yi ma ta
Wasu kuma ciyar da ita 'ya'yan itatuwa iri-iri suke tana
cikin matukar nishadi, ya yin da wadansu samari da
'yan mata ke ta faman tika rawa a tsakiyar fadar ana vi
musu kida mai taushi gami da bushin sarewa mai
dadin saurare, don kawai a debewa Sarauniya kewa.
Koda aka hango masu gadin kofar gari sun taho
da sauri bazar-bazar, sai masu kida s**a tsaida
kidansu, 'yan rawa s**a kame tamkar gumaka, jama'a
s**a tsuke bakunansu, wato dai fadar tayi tsit tamkar
babu wani abu mai rai a cikinta.
Cikin tsananin fushi Sarauniya Dulaiba ta kurawa
masu gadin idanu tana sauraron isowarsu. Ai kuwa
suna isowa daf da karagar mulki sai duk s**a zube
kasa bisa guiwoyinsu s**a kwashi gaisuwa sannan
shugaban nasu ya fara jawabi cikin biyayya ba tarc da
ya d**o da kansa ba. Ya dubi Sarauniya Dulaiba ya ce
"Ya shugabata ina mai sanar da ke cewa yau wani
takadarin bako ya shigo wannan birni namu mai
albarka tare da matarsa da kuma Rakuma sama da
guda dari uku dauke da hajoji. Lokacin da muka tare
wannanbako domin mukawoshi gareki k**ar yadda
muka saba yi tsawon shekaru, sai ya zO mana da
gardama har muka yi sa'insa da shi, daga nan ban san
abin da ya faru dani ba sai ji nayi sauran abokan aikma
suna yi min sannu, ashe suma nayi s**a yayyafa min
ruwa. A takaice dai ranki ya dade wannan
bako
sadauki ne na gaske ya fi karfinmu nesa ba kusa ba.
don baka ya karya dokarki ya wuce izuwa cikin gari
kai tsaye."
Ya yin da shugaban dakarun masu tsaron kofar ya
ZO nan a zancensa sai Sarauniya Dulaiba ta bushe da
dariya. Nan take fadawanta ma s**a k**a dariyar.
sannan sauran jama'ar da ke fadar s**a yi koyi. Fadar
gaba daya ta rude da dariyar jama'a har izuwa tsawon
wadansu 'yan dakiku. Daga can sai Sarauniya Dulaiba
ta tsuke bakinta ta mike zumbur fuskarta a murtuke.
Koda ganin faruwar hakan sai kowa ya tsuke nasa
bakin, fadar ta sake yin tsit a karo na biyu. Sarauniya
Dulaiba ta dubi Sarkin yaki HUSARU cikin kakkausar
murya ta ce, "Me kake jira ne? Maza ka debi
zakwakuran dakarunka guda dubu ka tafi dasu izuwa
ga wannan bako. Kada ku kashe shi, ina son ku
kamoshi a raye shi da matar tasa da dukiyarsu duka ku
Zo mini da su nan yanzu".
Koda jin wannan umarni sai Sarkin yaki Husaru
ya mike tsaye da sauri ya fice daga cikin fadar.
Husaru ya kasance garjejen katon mutum, kuma
sadauki. Dogo ne ainun, domin komai tsawon bishiya
yana iya tsinko dan itaciyarta da hannu. Yana da
damatsa gami da kwanji da kuma murdadden jiki.
Mutum ne mai matukar kwarjini da ban tsoro. Bugu da
kari boka Gaibhar ya tsumashi ainun a cikin tsumin
tsafi, ko kadan kaifi da tsini bava tasiri a jikinsa. Haka
kuma idan mutum zai kwana yana dukansa. ba zai ji
komai ba, tamkar ma susa ake yi masa.
Lokacin da matar Mujahid ta gama shayar da
Rakuma ruwa sai itama ta sha ta koshi, sannan ta sami
wuri ta zauna tana hutawa. Zamanta ke da wuya sai ta
hango wadansu mahaya kimanin mutum dubu sun
sukwano dawakai a guje izuwa gareta. Tuni sun tashi
kura, kuma sun dugunzuma hankalin kasa, kai kace
wani gagarumin yaki s**a fito. Ko kadan matar
Mujahid bata gyara zama ba bare ta mike tsaye ko ta
nuna wata alama mai nuna cewa ta razana, har
Dakarun s**a iso gareta s**a yi ma ta kwanya. Da
zuwa sai shugabansu Husaru ya sauko daga kan
dokinsa yaje daf da ita ya tsaya yana mai dubanta cikin
gadara ya rike kugu da hannu biyu ya ce, "Ya ke
wannan bakuwa, ina mijin ki yake?".
Ko daga kai ba ta yi ta kalleshi ba bare na ta amsa
tambayar. Da farko sai Husaru ya yi tsammanin bata ji
shi ba, don haka sai ya sake maimaita tambhayarsa
yana mai daka ma ta tsawa. Bisa mamaki sai ya ga a
wannan karon ma bata d**o kai ta dubeshi ba bare ta
fahimci abin da ya ke fadi.
Cikin fushi Husaru ya kai mata cafka da
hannunsa guda da nufin ya kamo wuyanta ya yi ma ta
rikon wulakanci, kuma ya shaketa. Kawai sai ta
sunkuya a cikin tsananin zafin nama ta k**a hannunsa
ta murde ta doki gadon bayansa da kafarta. Ya tafi
taga-taga zai kife da fuskarsa, sai da ya dage iya
Karfinsa sannan ya iya tsaida kansa. A lokacin ne
sauran dakarun da ke kewaye da ita s**a zare mak**ai
s**a yunkura za su afka mata. Amma sai s**a ii
Husaru ya daka musu tsawa yana mai basu umarnin su
dakata.

Topah Nima kuwa ya dakatar dani anan

Domin jin yadda zata kaya mu hade a na gaba

Har yanzu muna maraba da masu son shiga WhatsApp group dinmu wanda zaku dinga samun litattafan yaki Dana soyayyah harda Na nishadi
👇👇👇👇

Saikunzo
AA Misau Ke Magana

GUGUWAR ANNOBALittafi Na Daya (1)Part D.Na Abdulaziz Sani M/GiniAA Misau Ke Magana(Karku Manta Zaku samemu a WhatsApp gr...
28/04/2024

GUGUWAR ANNOBA
Littafi Na Daya (1)
Part D.
Na Abdulaziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana

(Karku Manta Zaku samemu a WhatsApp grp namu ta link da ke kasa

Bayan Nan ina Mana Barka da wannan lokaci)

Marubucin yaci GABA da cewa...

Abin tambaya anan shi ne, "Ta ya ya wannan
sohon mutum ya iya daukar Wannan sungumi mai
naUyi a bayansa alhalin sungumi ne mai gima da
Idan mutum ya lura da kirar jikin tsohon
wacce ta kasance irin ta samudawa zai iya baiwa
kansa amsa cewa ai karfi yana ga mai alamar Kiba.
Kai tsaye Sarki ya nufi inda kujerar mulkinsa
take tare da bakinsa mutum biyu. Koda ganin haka
sai 'yan majalisa s**a mike tsaye don girmamawa.
Da isarsu daf da karagar mulki sai Sarki Yarduza
ya k**awa tsohon wannan katon sungumi da ke
bayansa ya ajiye a kas, sannan ya tsohon ya yi
masa umarni da ya hau kan karagarsa ta mulki ya
Zauna.
Gaba dayan jama'ar da ke cikin fadar sai s**a
bude baki s**a kurawa Sarki idanu cikin tsananin
mamaki, aka rasa wanda zai cc kala.
Sarki Yarduza ya dubi Sharlisa ya nuna ma ta
wata kujerar da ke daf da karagar mulki ya ce itama
ta zauna. Sharlisa taje ta zauna sannan Sarki
Yarduza ya tsaya a gabansu ya fuskanci fadawansa
da sauran jama'a ya ce,"Ya ku jama'ar Birnin
Kaluza ku yi sani cewa wadannan baki da nazo da
Su yanzu sun kasance masu matukar daraja a

idanuna, saboda haka daga yau ina son ayi biyayya
wannan tsoho da ke zaune akan karagata k**ar
yadda ake yi mini har izuwa tsawon kwana bakwai.
Duk irin abinda ake yi mini shi nake so dinga yi
masa. Kada a rage masa abu daya".
Koda gama fadin hakan sai Sarki Yarduza
koma gefe daya ya zauna a kasa dirshan kusa da
karagar mulki tamkar almajiri, sannan aka ci gaba
da tafiyar da harkokin mulki.
Al'amarin da ya matukar baiwa gaba dayan
mutanen da ke fadar mamaki ke nan kuma ya
dugunzuna hankalin 'yan majalisa.
Daga can sai shugaban Majalisa yazo ya
zauna daf da Sarki Yarduza yai masa rada a kunne
ya ce, "Ya shugabana wannan abu da kayi yanzu
bai taba faruwa ba a wannan masarauta tamu,
tabbas abin kunya ne kuma abin gori ne
zuri'arku"..
Koda jin wannan batu sai Sarki Yarduza ya
d**o kai ya dubeshi cikin tsananin fishi da fusata
ba tare da ya ce komai ba. Nan take jikin shugaban
majalisa ya k**a karkarwa, domin
ya san cewa
Cikin sanyin jiki shugaban majalisa ya mike
tsaye ya koma inda yake ya zauna.

Kuraisu ya k**a kallon karagar mulkin da
yake zaune a kanta tamkar dan kauye ya shigo
Birni, sannan ya rinka kallon fadawa da sauran
jama ar gari da kuma sauran kayan kawar da ke
fadar.
Daga can sai ya mike tsaye ya k**a yawo a
ikin fadar yana taba kayayyaki yana kyalkyala
ariva cikin tsananin farin ciki tamkar mahaukaci
sabon kamu.
Daga can sai ya koma kan karagar mulki ya
zauna. Kawai kuma sai aka ga ya fashe da kuka.
Koda ganin haka sai idanun Sharlisa da na Sarki
Yarduza s**a ciko da kwalla s**a k**a zubar da
hawaye, saboda tausayinsa, domin su kadai ne s**a
san dalilin dariyarsa da kukansa.
Sauran jama'a kuwa duk s**a cika da tsananin
mamaki bisa wannan bakon al'amari.
K**ar yadda Sarki Yarduza ya bayar da
umarni, haka al'amarin ya kasance, wato sai da
Kuraisu ya kwana bakwai kullum yana zama akan
karagar mulki yana shugabantar jama'ar Birnin
Kaluza, kuma yana kwana a gadon Sarki Yarduza,
yana sanya suturarsa da cin irin abincinsa.
Babu abinda ya kara daurewa mutane kai face
ganin yadda Kuraisu ke tafiyar da harkokin mulki
dai-dai k**ar yadda kowanne Sarki da ya shude ke
yi, tamkar dama can a gidan sarautar ya taso, ya
san komai ba a koya masa ba.
'Yan majalisa kuwa, s**a yi ta zunde da
munafunci a tsakaninsu suna ta
gano ko wane ne wannan bakon tsoho da Sarki
Yarduza ya zo da shi ya daukakeshi fiye da kansa
bincike akan s
Abinda kawai s**a iya ganowa shi ne, tsohon
ya kasance uba ga wannan kyakkyawar budurwa
wacce Sarki ya zo da ita.
A daren kwana na bakwai ne tsoho Kuraisu ya
kamu da tsananin zazzabi mai zafin gaske, jikinsa
ya k**a tsuma, yana kwance akan gado a cikin
turakar Sarki, 'yarsa Sharlisa na zaune daf da shi
cikin tsananin dimauta da tashin hankali, domin a
iya zamanta da mahaifin na ta bata taba ganin sa ba
Sharlisa ta kurawa Kuraisu idanu a lokacin da
hawaye ke zuba daga cikin idanunsu su biyun, ta
k**a kafadunsa ta rike tana mai cewa, "Ya kai
Abbana kayi sani cewa a tsawon zamana da kai ban
taba ganin ranar da ka yi koda ciwon kai ba, amma
yau gashi zazzabi mai zafi ya rufeka, kuma
Likitoci sama da guda hudu sun shigo sun dubata
da kuma dalilin yin hakan, amma s**a kasa.
a cikin irin wannan hali ba.
Sun baka magani ka sha amma har yanzu baka sami
latiya ba, mene ne ma'anar wannan rashin lafiya?"
hannunsa da kyar ya k**a hannun Sharlisa ya ce,
Sa adda Kuraisu yaji wannan tambaya sai ya daga
ya ke 'yata ki gafarceni, domin kuwa na 6oye
miki wani babban al'amari a rayuwata.
Tabbas numfashina a duniya yau zai yanke, a
vau ne mai rabawa za ta rabamu, domin wa'adina
ya cika.
Tun daga ranar da dan uwana Yarduza ya hau
kan karagar mulkin kasar nan, wato mahaifin Sarki
Yarduza na yanzu, wanda ya kawo mu fadar nan,
na bazama yawo wajen bokayen duniya ina neman
sihirin da zan iya hallakashi na yi masa juyin mulki
A ranar da aka haifcki ne na sadu da wani
hatsabibin boka ya ce da ni har abada ba zan iyama
komawa cikin Binin Kaluza ba sai bayan mutuwar
dan uwana a zamanin mnulkin dansa, kuma a
nan din Tna sai dai na dandani mulki na tsawon
kwana bakwai kacal, kuma a daren kwana na
Bokan ya ce da ni idan har na amince zai iya
yi mini sihirin da wannan bukata tawa za ta biya.
da karfin tsiya a darc daya, amma ban samu ba har
izuwa lokaicn da mahaifiyarki ta haifeki.
bakwan zan mutu.

Koda na ji wannan batu sai hankalina ya
dugunzuma na fashe da kukan bakin ciki saboda na
auna na ga cewa wannan dama fa sa'adda za ta zo
mini na tsufa ainun, kuma mene ne amfanin naji
dadin mulkin gidanmu na kwana bakwai kacal?
Sai da na dade ina tunani da zullumi gami da
matsanaicin bakin ciki, daga bisani sai zuciyata ta
ce da ni, "Ai idan ma ban yi amfani da wanna
dama ba dole dai mutuwa zan yI na bar duniya ba
tare da na cik aburina ba,"
Nan take na amince da sharadin wannan boka
ya yi mini wannan sihiri. labbas tsafi gaskiyar mai
shi ne, domin gashi yanzu wannan tsafi ya yi
tasirinsa.
Ya ke 'yata, kiyi sani cewa lallai ina ji a jikina
cewa a ko yaushe ruhina zai iya fita daga cikin
gangar jikina. Ma za ki ruga ki je ki nemo Sarki
Yarduza domin na bar masa wasiyya da amanarki".
Koda jin wannan umarni sai Sharlisa ta fashe
da matsanaicin kuka, ta kwanta akan kirjin Kuraisu
Kwatsam! Sai s**a ji an bude kofar turakar,
Sharlisa ta juyo da sauri, sai ta ga ashe Sarkı
Yarduza ne ya shigo.
Koda ya hango Sharlisa kwance akan kirjin
ta kasa tashi ta tafi kiran Sarki Yarduza.

Kuraisu tana ta faman sharba kuka sai hankalinsa
ya dugunzuma ainun ya rugo garesu ya zauna a
geten gadon ya k**a hannun Kuraisu ya rungume
kirjinsa, shima idanunsa s**a ciko da kwalla.
Kuraisu ya dubi Yarduza cikin murmushin
karfin hali ya ce, "Ya kai dana, kayi sani cewa
vanzu zan tafi izuwa inda mahaifinka ya tafi, kuma
ina matukar farin ciki da ya kasance zan tafi a
lokacin da na sami damar ganawa da kai.
Wasiyata a gareka ita ce, ga 'yata nan na baka
ita halak, malak! Kuma ka riketa amma ka ci gaba
da jiyar da ita irin dadin da ka jiyar da ni tsawon
kwanakin nan bakwai har izuwa ranar da mutuwa
za ta rabaku.
Tabbas idan kayi haka za ka yi nisan kwana,
kuma za ka sami magaji. Idan kuwa ka bijirewa
wannan umarni nawa mulkin kasar nan zai bar
hannun zuri'arnu har abada, kuma ba za ka ta6a
samun magaji ba wanda zai cika maka naka burin
k**ar yadda ka cika na mahaifinka".
Koda Kuraisu yazo nan a zancensa sai jikinsa
ya k**a karkarwa mai karfi, idanunsa s**a kafe.
Sharlisa ta ciccibeshi cikin matukar firgici ta
rungumeshi a kirjinta tana mai fashewa da kuka.
Daga can sai taji jikin nasa gaba daya ya
AA Misau Ke Magana

sandare ko motsi baya yi, kawai sai ta dada
kankameshi ta fashe da wani sabon matsanaicin
kukan.
Da kyar Sarki Yarduza ya bambareta daga
jikin gawar mahaifin na ta.
Sharlisa ta rungume Yarduza ta ci gaba da
kuka, shima sai zuciyarsa ta karaya ya k**a kukan
mazaje yana zubar da hawaye kawai.
A dai-dai lokacin ne Dakaru s**a shigo cikin
turakar s**a dauki gawar Kuraisu s**a fita da ita
domin a fara shirye-shiryen bikin binneta.
Bayan kwana uku da binne gawar tsoho
Kuraisu a inda aka saba binne duk Sarakunan da
s**a yi mulki a gidan sarautar, sai Sarki Kuraisu ya
ki ci gaba da zaman fada bare ya ci gaba da zartar
da sauran harkokin mulki.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin 'yan
majalisar ke nan s**a yi gangami s**a zo s**a
sameshi har cikin turakarsa.
A wannan lokaci yana tare da Sharlisa yana
rarrashinta da lallaminta domin ta ci abinci, saboda
tunda mahaifinta ya rasu sau daya ta ci abinci loma
uku kacal, har ta rame ta fita haiyacinta.
A sannan ne Yarduza ya shawo kan Sharlisa
ta ci abinci mai dan yawa har ta koshi ta sha ruwa.

Koda Sarki Yarduza ya ga 'yan majalisa Sun
shigo har cikin turakarsa sai ya mnike da sauri ya
dubi Sharlisa ya ce, "Ki jirani ina zuwa ya ke
masoyiyata,"
Cikin sauri ya tari 'yan majalisar ya fitar da su
waje kuma ya jasu s**a tafi izuwa can fada.
Da shigarsa cikin fadar sai yaje ya zauna a kasa
maimakon ya zauna a kan karagar mulki. Da ganin
haka sai suma 'yan majalisar duka s**a zazzauna a
kasa kusa da shi.
Tsawon 'yan dakiku kowa yai shiru bai ce
kala ba.
Daga can sai shugaban majalisar yai gyaran
murya ya ce, "Ya shugabana, kayi sani cewa
hankalinmu ya dugunzuma ainun saboda tunda
wannan bakon tsoho ya mutu baka fito fada ba.
Ai ya k**ata ace yanzu ka gama alhinin
rashinsa.
Abu na biyu shi ne, muna son ka gaya mana
matsayin wannan kyakkyawar budurwa da ka zo da
ita da kuma alakarta da wannan tsoho da ya mutu,
da kuma irin darajarsu a wajenka, domin mun ga ka
darajtasu fiye da kima".
Sa'adda shugaban majalisar yazo nan
zancensa sai Sarki Yarduza ya turbune fuskarsa

k**ar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Al'amarin da ya frgita 'yan majalisar ke nan gaba
đayansu.
Sarki Yarduza ya dubi shugaban majalisa a
fusace ya daka masa tsawa ya ce,
"Sarki Sarki ne!
A ko yaushe duk abinda ya yi dai-dai ne. Babu
wata huja da za ta sa ku tuhumeni bisa abinda na
aikata, domin ba zan taba yin abinda na san zai
cutar da jama'ata ba ko kasata.
Duk irin jita-jitar da ake yi a garin nan da
gulma suna dawowa kunnena. Na san cewa kowa
so yake ya san sirrin da ke tsakanina da wadannan
baki da na kawo.
To ku sani cewa ko za ku san wannan sirri sai
dai bayan raina! Daga yau ni ba zan sake hawa kan
karagar mulki ba kuma ba zan bayar da umarnin
komai ba.
Wannan bakuwar budurwa da na zo da ita, ita
ce za ta ci gaba da zartar da komai. Wannan yana
nufin cewa ita SARAUNIYARKU!
Har gobc ni ne Sarkinku, kuma a gobe da safc
za a daura aurcna da ita. Na sallamcku kowa ya
k**a gabansa!"
Koda gama fadin hakan sai Sarki Yarduza ya
mike tsayc ya fice daga cikin fadar ya koma izuwa
i
cikin gidan sarautar ya bar yan majalisa a zaune
suna muzurai da kallon Juna cikin tsananin
mamakin jawabin da ya yi musu ya zamana cewa
on rasa wanda zai ce kala a cikinsu.
Kashe gari kuwa aka daura auren Sarki
Yarduza da Sharlisa, aka shiga shagalin biki.
Mawaka, Makada, Maroka s**a yi ta bidirinsu.
Sauran Sarakuna, Attajirai da masu fada aji na
kasashen makwabta s**a yi ta kawo ziyarar taya
murna da kawo kyauttuttuka, ya zamana cewa
Birnin Kaluza ya cika ya batse da mutane
Sai da aka kwana goma ana rakashewa sannan
Sarki ya sallami bakinsa aka watse.
Daga wannan rana Sharlisa ta zamo tamkar ita
ce Sarauniyar Birnin Kaluza, sai umarnin da ta
bayar shi ake bi.
Abinda ya kara daurewa jama'a kai shi ne, a
lokacin Sharlisa nc arzikin kasar ya bunkasa fiye
da ko yaushe, kuma alka sami zaman lafiya da
kwanciyar hankali irin wanda ba a taba samu ba a
tarihin mulkin masarautar da ya shude.
Kuma a sannan ne Dakaru s**a rinka samun
horon yaki na musamman irin wanda ba a taba
basu ba. Kuma Sharlisa ce take basu horon da
kanta.

A wannan lokaci ne labarin Sharlisa ya bazu a ko
ina nahiyar har ma aka fara tunanin tafi Sarki
Yarduza jarumtaka da iya yaki, saboda ganin wata
gagarumar bajinta da tayı bayan ta sami wata uku
cif akan karagar mulki.
Al'amarin ya faru ne wata rana, da rana tsaka
ana zaune a fada, Sharlisa na tafiyar da harkokin
A wannan lokaci mijinta Sarki
zaune a gefe daya yana kallonta kawai yana
murmushi cikin farin ciki.
Kwatsam! Sai ga wani babban
makiyayi da ake kira Zamaranu dan Bilsaru ya shigo fadar a
rude jina-jina. Da zuwa sai ya fadi gaban Sharlisa
yana haki k**ar ransa zai fita.
Da kyar ya budi baki ya ce, "Ya shugabata ki
yi sani cewa na fita bayan gari tare da dabbobin
jama'a, kimanin guda dubu saba'in tare da
Dakaruna su dari bakwai, domin mu gudanar da
kiwo k**ar yadda muka saba yi kullum a cikin
daii. sai kwatsam! MuKa ga Dakarun sumame
kimanin su dubu talatin sunyi mana
kawanya.
Ba tare da jiran komai ba s**a hau mu da sara
da s**a s**a karkashe dukkan yarana. Da kyar ni
kadai na sha na gudu izuwa nan cikin gari.

Abin takaici shi ne, ko alamar guduwa ma
basu yi ba, har na ji Shugabansu yana cewa naje na
gayawa wannan macen sarauniyar tamnu idan ta isa
tazo ta karba maku dabbobinku. Idan kuna ba za ta
a ba ta turo Dakarunta tunda yanzu mijinta ya
zama mace kamnar ita. tun
Kafin
makiyayi Zamaranu dan Bilsaru ya
gama rufe bakinsa tuni Sarki Yarduza ya zare
takobinsa cikin zafin nama ya fille masa kai. Take
kan ya fice fit daga jikin wuyansa yai sama ya fado
kasa kuma jini yai tsartuwa da fushi.
Gaba daya jikin Sarki Yarduza ya k**a
tsuma, kawai sai ya mike tsaye a fusace ya dubi
wani Badakare ya ce, "Aje a kawo masa
garkuwarsa da dokinsa zai fita shi kadai ya yaki
wadannan Dakarun sumame".
Koda jin wannan batu sai Sharlisa ta ce, "A
dakata". Kawai sai ta mike tsaye daga kan karagar
mulki ta tako ta zo gaban Yarduza ta tsaya, ta
dubeshi cikin murmushi ta ce da shi, "Haba ya kai
mijina, ai wannan karamin aiki ne, ka fi ga nan, sai
dai ni!
Ka sani cewa kai gwarzon sadaukai ne, baka
tarar iska sai dai GUGUWAR ANNOBA. Ka
kyaleni da wadannan marasa kunya ni ne zan yi maganinsu"

Gama fadin hakan ke da wuya sai ta karői
takobin da ke hannun Sarki Yarduza ta ruga da
gudu izuwa wajen fadar ta fita daga cikin harabar
gidan sarautar gaba daya ko doki ba ta nema ba.
Abinda ya fara baiwa jama'a mamaki shi ne,
ganin azababben gudun da take falfalawa tamkar
na doki, kuma babu alamar gajiya a tare da ita.
Kafin wani lokaci tuni ta fice gaba daya daga cikin
Birnin gaba daya.
Bayan Sharlisa ta fice daga cikin fadar
hankalin Sarki Yarduza ya dugunzuma ya fara
tunani a ransa ya ce, "Anya kuwa Sharlisa ba ta yi
ganganci ba? Ta ya ya za ta iya tarar wadancan
Dakarun sumame kimanin su dubu talatin ita
kadai?
To wai shin ma ta iya yaki ne sosai? Kuma
wacce irin juriya ce da ita? Shi dai bai taba ganin
yanayin yakinta ba, abinda ya taba gani kawai shi
ne, wannan jarumtaka da tayi ta kamo barewar da
va kasa k**awa sak**akon hawa kan tsauni mai
Santsin
Sa'adda Sarki Yarduza ya zo nan a zancen
Zucinsa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, nan
take ya mike zumbur! ya sake bada umarni aka
kawo nasa kayan yaki yai damara, sannan ya hau
doki ya zaburcshi da gudu izuwa wajen gidan sarautar
Nan take shugaban majalisa ya umarci
shugaban Dakaru ya ce maza su bi bayan Sarki
Warduza da matarsa su kai musu đauki.
Cikin gaggawa sama da Dakaru dubu arba'in
s**a yi hawa s**a bi bayan su.

AL'AMARIN JARUMA
SHARLISA
Akuwa, lokacin da ta ke falfala azababben
gudu ta fito daga cikin Birnin Kaluza, sai ta hango
dandazon Dakarun sumamen sun kafa sansani.
Saboda wulakanci ma har sun yanka
cikin dabbobin sun kunna wuta suna
wadansu daga
gasawa za su
Koda Dakarun sumamen s**a hango mutum
daya kacal ya fito daga cikin Birnin Kaluza a guje
ya durfafo sansaninsu sai s**a cika da tsananin
mamaki s**a mimmike tsaye s**a zuba idanu suna
jiran karasowar mutumin, domin su ga ko wane
mai tsaurin ido ne haka.
Koda Sharlisa ta iso daf da su sai tayi turjiya
ta tsaya tana haki ana kallon-kallo.
Ya yin da Dakarun sumame s**a ga ashe
mace ce sai gaba dayansu s**a bushe da darivar
mugunta. S**a yi ta kyalkyalawa k**ar ba za su
daina ba.
Kwatsam! Sai s**a ji Sharlisa ta daka musu
tsawa, tsawar da ta cika filin wajen gaba daya da
amsa kuwwa.
Gaba dayansu sai da s**a shiga taitayinsu
domin tsawa ce irin wacce manyan mazaje ke yi a
filin daga, ka ga mutane sun dimauce sun k**a
gudu suna neman maboya.
Sharlisa ta dubi Dakarun sumamen gaba
dayansu ta ce, "Ku kananan kwari, ku yi sani cewa
ni ce dan hakin da kuka raina mai tsokane muku
Tabbas yau kun yi babban kuskure, kuma
babban ganganci da kuka kawo hari nan Bimin
domin gwara ku je ku jefa kanku a cikin wutar da
ta shekara tana ci da ruruwa.
Na rantse da darajar wannan takobi ta sarautar
Bimin Kaluza da ke hannuna sai na zare muku
ruhin numfashinku gabe dayanku, dayanku ba zai
tsira da rayuwarsa ba."
Koda jin wannan
Dakarun sumamen s**a
batu sai gaba dayan
sake bushewa da dariyar mugunta lokaci guda Kuma s**a tsuke bakinsu

Topah Nima Kuma A A Misau Anan zan tsuke bakina nake cewa Sai wani lokaci Kuma

WhatsApp grp

Facebooks

AA Misau Ke Magana

Address

Hadejia
730102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Novels Only posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Hausa Novels Only:

Share

Category