FARIN GIDA TV

FARIN GIDA TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from FARIN GIDA TV, Hadejia general hospital Road, Hadejia.

Wata Kotun Shari’a da ke Dutse a Jihar Jigawa ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan Habibu Muhammad Ringim bisa zargi...
12/05/2026

Wata Kotun Shari’a da ke Dutse a Jihar Jigawa ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan Habibu Muhammad Ringim bisa zargin cin mutunci, kazafi da kuma kage ga tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Adamu Aliyu.

Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Habibu Muhammad Ringim a gaban kotun ne ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026, inda aka fara sauraron shari’ar bayan korafin da aka shigar a kansa.

Bayan sauraron ɓangarorin da abin ya shafa, Alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali har zuwa ranar 28 ga watan Mayun 2026 domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Yanzu-Yanzu:An yi garkuwa da manyan ’yan siyasa a Jigawa, Hon. Abba Anas Laushi da Hon. Ali Gantsa, a hanyar Abuja.Rahot...
08/05/2026

Yanzu-Yanzu:
An yi garkuwa da manyan ’yan siyasa a Jigawa, Hon. Abba Anas Laushi da Hon. Ali Gantsa, a hanyar Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, a daren jiya ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne s**a sace jigo a jam’iyyar ADC, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Guri, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya tare da tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu Laushi, tare da amininsa Hon. Ali Gantsa.

An ce lamarin ya faru ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Abuja.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro ba dangane da yadda lamarin ya faru ko kuma inda aka kai su.

Al’umma da magoya bayansu na ci gaba da kira ga jama’a da su sanya su cikin addu’a domin Allah Ya kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.

Farin gida TV

Yanda Hadadiyar kungiyar Manoma takasa  ( AFAN ) Reshen karamar hukimar milki ta Hadejia ta Rantsar da shubanninta. Wand...
27/04/2026

Yanda Hadadiyar kungiyar Manoma takasa ( AFAN ) Reshen karamar hukimar milki ta Hadejia ta Rantsar da shubanninta. Wanda ya gudana a cikin harabar karamar hukimar a yau 27/4/2026. Ta kar kashin jagoracin shuganta na Jiha. ALH. YAU IDRIS MAI UNGUWA tare da sauran abonkan aikin sa na Jiha. Taro ya sami halartar matemakin shugaban karamar hukimar milki ta Hadejia da. H.O.D AGRIC. Muna rokon Allah y tasu Riko yasa Agama lapia.

YAR BAIWA KENAN .... Masha Allah Matar da ta haifi ya'ya' hudu russ, Kuma duk su hudun suna cikin koshin Lafiya.🫡✌️😇 😇 😇
21/04/2026

YAR BAIWA KENAN .... Masha Allah Matar da ta haifi ya'ya' hudu russ, Kuma duk su hudun suna cikin koshin Lafiya.
🫡✌️😇 😇 😇

19-04-2026              HADEJIAShugaban Babban Ƙwamatin Bikin tunawa da ranar da Hadejiyawa s**a yi Turjiya ga Mulkin Ma...
20/04/2026

19-04-2026 HADEJIA
Shugaban Babban Ƙwamatin Bikin tunawa da ranar da Hadejiyawa s**a yi Turjiya ga Mulkin Mallaka na Turawan Birtaniya, Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdul'aziz ya ce manufar Bikin shine inganta Ruhin Jarunta da kishin Addinin Muslunci da kuma kiyaye Al'adu na Mutanen Kasar Hadejia ga matasa masu tasowa.
Ya baiyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a Ofishin sa da ke fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia a cigaba da shirye-shiryen bikin da za'a gudanar daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Afrilu a Garin Hadejia.
Alhaji Usman Abdul'aziz ya ce wannan Tarihi daya faru a shekara ta 1906 kimanin shekaru 120,ya yi sanadiyar mutuwar Mayaƙan Hadejia sama da 800 ciki har da Sarkin Hadejia na lokacin Alhaji Muhammad Mai Shahada.
Ya ƙara da cewa sojojin kasar Birtaniya ma sunyi asarar rayuka a lokacin gumurzun,ciki har da Babban Kwamandan su Captain H.C.B Philips tare da wasu manyan jami'an su,inda yace cikin shirye-shirye bikin akwai ziyara zuwa wasu muhimman wuraren tarihi domin tunawa da faruwar lamarin.
Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa za'a ƙaddamar da wani littafi mai ɗauke da cikekken tarihin wannan Rana wanda marigayi Professor Haruna Wakili ya rubuta tare da haɗin gwiwar wasu masana Tarihi.
A jawabinsa tun da farko , shugaban Ƙaramin kwamatin kuma kwamishinan yaɗa labarai Sagir Musa Ahmed yayi wa 'Yan Jaridu jawabin maraba tare da ƙira a garesu da su yi amfani da kafafen watsa labaran su wajen manufar Bikin.

TAKAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO Asali da Girman Daular Auyo Auyo tana daya daga cikin tsofaffi kuma mashahuran garuruwa ...
20/04/2026

TAKAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

Asali da Girman Daular Auyo

Auyo tana daya daga cikin tsofaffi kuma mashahuran garuruwa masu cin gashin kansu tsawon zamani. A tarihi, Auyo birni ne da ya dade kwarai da gaske, inda tarihi ya nuna ya wanzu tun dubban shekaru kafin zuwan Annabi Musa (A.S). Kafin bayyanar Daular Fulani, Daular Auyo babbar masarauta ce mai karfi wacce ke da ganuwa da ta kewaye ta, kuma tana da iko akan garuruwan da ke makwabtaka da ita kamar su Hadejia, Madachi, da Kirikasamma wadanda a wancan lokacin suke karkashin ikon Hausawa. Garin ya tara dakaru da baraden yaki wadanda sunansu kadai yana sanya gaban abokan gaba faduwa.

Alaka da Kanem Borno da Tasirin Harshen Kanuri

Daular Auyo tana da kyakyawar dangantakar kasuwanci da abota tsakaninta da Kanem Borno tun babban birninta yana Ngazargamu (a yanzu Geidam). Sakamakon wannan alaka da kuma kasancewar yawancin mazauna Hadejia, Madachi, da ita kanta Auyo mutanen asalin Kanuri ne, hakan ya sa lunguna da tituna da yawa a yankin suke da sunayen Kanuri. Misali:
• Yayari
• Gagulmari
• Auyakayi
• Makerayi
• Galdimari
• Kaigamari
• Matafari

Dalilin wannan alakar ce ta sa ake kiran Sarkin Auyo na yanzu da “AUYOMA” wanda a harshen Kanuri take nufin “MAI AUYO ko SARKIN AUYO”

Garuruwan da ke karkashin daular Auyo:
• Hadejia
• Madachi
• Kirikasamma
• Kafin Hausa

Da sauran kananun Daulolo kamar su:
• Garin Gabas
• Kazura
• Gaduwa, da sauran su

Samuwar Masarautar Hadejia

Tarihin Hadejia ba zai taba cika ba sai an ambaci Daular Auyo, domin da can babu Hadejia. A hakikanin gaskiya, garuruwa ne irin su Auyo, Garin Gabas, Kazura, da Gaduwa aka hade su waje guda domin samar da Masarautar Hadejia. Asalin sunan "Hadeja" ya samo asali ne daga wani maharbi dan kabilar Kanuri daga kasar Machina mai suna Hade, da kuma matarsa mai suna Jiya. Allah ya kawo su bakin kogi s**a zauna suna sana'ar harbi. Daga nan sauran maharba da masunta s**a dawo wurin har kasuwancin fatu, nama, da kifi ya habaka. Idan mutane za su je cin

AIKIN TANTACE RIJISTAR MASU ZAƁE NA ƘASA 2026Kamar yadda da yawa s**a sani INEC ta ce dole sai kowa ya sake sabunta kati...
05/04/2026

AIKIN TANTACE RIJISTAR MASU ZAƁE NA ƘASA 2026

Kamar yadda da yawa s**a sani INEC ta ce dole sai kowa ya sake sabunta katin zaɓen shi, to jama'ah kar muyi ƙasa a gwiwa, mu dage muyi wannan domin kawo ƙarshen wannan gomnatin ta ƙasa .

za'a fara wannan aiki kamar haka 👇👇

Rana da Wuri:
✅13 ga wata Afrilu 2026 zuwa 2 ga watan Mayu 2026
✅ Tantancewa a matakin ƙananan hukumomi (LGAs) – Kwana 20
✅5 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Mayu 2026
✅ Tantancewa a matakin yankunan rajista (RAs) – Kwana 7
13 ga Mayu zuwa 19 ga Mayu 2026
✅A wuraren zaɓe (Polling Units) – Kwana 7
20 ga Mayu zuwa 29 ga Mayu 2026
✅Komawa LGAs – Kwana 10

⏰Lokaci: 9:00 na safe – 3:00 na rana
Zaku iya zuwa daga ranar Litinin har Lahadi
Mu sani : Wannan sabuwar ta shafi waɗanda s**a yi rajista daga 2011 zuwa 2024.

Zaku iya sabuwar a wayoyin ku idan kuka shiga wannan link ɗin
: https://cvr.inecnigeria.org⁠�
Ga yadda zakuyi
📌Ƙirƙiri asusu (account)
📌Shigar da Lambar Shaidar Mai Zaɓe (VIN) ko bayanan kai
📌Tantancewa (biometric) ta hanyar hoton fuska
📌Shikenan an kammala
Bayan kammalawa akwai takarda da za'a baku, ko kuma a tura muku saƙon takarar ta E-mail 📩

Wadanda ba su da manyan wayoyi kuma, akwai tsarin 👉 TANTANCEWA A ZAHIRI (IN-PERSON)
Yadda ake yi shine
📍Kowa yaje zuwa cibiyar da INEC ta tanada
📍Zaku bada katin zaɓen ku domin ɗaukar lambar jikin katin
📍Za'ayi muku hoton fuska
📍Duk wani bayani da ke buƙatar gyara za a iya sabunta shi
📍Za'a baku takarda (printout) bayan an kammala
📍Za a aika saƙo zuwa Email 📩 ko lambar waya

Umar Abusufyan Yusuf (Ladan) ✍️✍️

03/04/2026

JARRABAWAR TANTANCE BUKATAR MALAMAI (TTNA)
Shugaban Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, yana sanar da daukacin malamai cewa za a ci gaba da gudanar da jarrabawar tantance bukatar malamai a ranar Asabar, 04/04/2026.
Muhimman Bayanai:
Wadanda s**a riga s**a yi jarrabawar a baya kuma s**a yi submitting successfully, ba su da bukatar sake zuwa.
Domin tabbatarwa, za su iya duba exam slip dinsu da misalin karfe 5:00 na yamma.
Cibiyoyin da aka samu matsaloli, musamman a Federal University Dutse (Centre One), za a sake jarrabawar gaba daya.
Wadanda s**a fuskanci matsalar na’ura a Gumel, su duba dashboard dinsu domin sanin ko za su sake jarrabawa ko a’a.
Cibiyoyin Jarrabawa (Centres):
Dutse Zone: Federal University Dutse (har da Ringim – an tanadi centres guda 3)
Hadejia Zone: Bilyaminu Usman Polytechnic (a maimakon NITDA)
Gumel Zone: Jigawa State College of Education, Gumel
Kazaure Zone: Hussaini Adamu Polytechnic
Babura & Garki: Federal University of Science and Technology, Babura
Kafin Hausa: Sule Lamido University
Ana bukatar dukkan malamai su fara cire exam slip dinsu, wanda zai nuna cibiyar jarrabawa da lokacin rubuta jarabawar.
Za a fara fitar da exam slip daga yau da misalin karfe 5:00 na yamma.
Sanarwa daga:
Farfesa Haruna Musa
Shugaban Hukumar Ilimi ta Matakin Farko
Jihar Jigawa

Shugabanin Matasan APC Uku Sun Mutu akan hanyarsu ta zuwa babbar taron APC Wasu matasan APC uku daga Ogbadibo, jihar Ben...
27/03/2026

Shugabanin Matasan APC Uku Sun Mutu akan hanyarsu ta zuwa babbar taron APC

Wasu matasan APC uku daga Ogbadibo, jihar Benue, sun rasu a hatsarin mota a hanyar Makurdi zuwa Lafia yayin da suke zuwa taron jam’iyya na APC.

Sauran da ke tare da su sun samu raunuka kuma suna jinya. Allah Ya jikansu da rahama.

Abdullahi Isawa

INNALILLAHI WA'INNA'ILAIHI RAJI'UN 😭Allah sarki rayuwa kwana ya Kare Wata mata kenan a ASIBITIN Murtala da ke Kano yadda...
26/03/2026

INNALILLAHI WA'INNA'ILAIHI RAJI'UN 😭

Allah sarki rayuwa kwana ya Kare

Wata mata kenan a ASIBITIN Murtala da ke Kano yadda ta haifi Yara Biyar amma tarasu bayan ta haife su 😭😭... Yar baiwa kenan muna mata Addua Allah yaji kanta da Rahama Yasa Aljannar Firdausi ta zama makomarta Ameen ya hayyu ya qayyum

Address

Hadejia General Hospital Road
Hadejia

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FARIN GIDA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share