Sarari Hausa news

Sarari Hausa news Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sarari Hausa news, Awala tudun wada gusau, Gusau.

Iyalan El-Rufai sun ba Janar Christopher Musa kwanaki bakwai ya janye kalamansa ko su garzaya kotuIyalan tsohon gwamnan ...
07/09/2026

Iyalan El-Rufai sun ba Janar Christopher Musa kwanaki bakwai ya janye kalamansa ko su garzaya kotu

Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun buƙaci ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da ya janye zargin da ya yi wa tsohon gwamnan na cewa ya shirya hallaka wasu mutane a kudancin Kaduna, ko kuma su ɗauki matakin shari'a a kansa.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa iyalan sun damu matuƙa da kalaman da ministan ya yi a ranar 3 ga watan Satumban 2026 yayin wani shirin kai-tsaye na "Politics Today" a gidan talabijin na Channels.

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Fiye da mutum miliyan 26 na fararen hula a ƙasar 1ràn s**a bayar da kansu domin shiga aikin soja a Tehr...
07/09/2026

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Fiye da mutum miliyan 26 na fararen hula a ƙasar 1ràn s**a bayar da kansu domin shiga aikin soja a Tehran, duk da tsagaita wuta da aka cim ma. Rahotanni sun ce wannan na cikin wani shiri mai suna “Ku sadaukar da rayuwarku”, inda za a haɗa masu sa kai da rundunar ju¥in ju¥a hali da kuma sojoji, tare da kafa garkuwar mutane don kare muhimman wurare.

Cikin masu rajista akwai shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian da shugaban majalisa Mohammad Bagher Ghalibaf, da sauran manyan jami’ai.

An kaddamar da shugabannin wata kungiyar da za ta shiga mazabu a Arewa domin neman goyon baya ga Bola Tinubu a jihar Kat...
07/09/2026

An kaddamar da shugabannin wata kungiyar da za ta shiga mazabu a Arewa domin neman goyon baya ga Bola Tinubu a jihar Katsina. Karanta cikakken rahoton a sashen sharhi.

'Yan uwa da abokan arziki na cigaba da nuna alhini kan rasuwar jarumar fim Zainab Diamond. Karanta abubuwan da suke fada...
07/09/2026

'Yan uwa da abokan arziki na cigaba da nuna alhini kan rasuwar jarumar fim Zainab Diamond. Karanta abubuwan da suke fada game da ita a sashen sharhi.

Jarumi a masana'antar Kannywood, kuma guda cikin masu tsaron lafiyar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da yi masa hidima, Tijja...
03/09/2026

Jarumi a masana'antar Kannywood, kuma guda cikin masu tsaron lafiyar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da yi masa hidima, Tijjani Asase ya bayyana cewa yana matuƙar biyayya ga Rarara ne saboda yadda yake tsare masa mutuncinsa a matsayinsa na maraya wanda ba shi da uwa da uba a raye.

Dokin Karfe TV ta ruwaito Asase na bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Podcast na Jita, inda ya ƙara da cewa:

"Kuma in ka ga gawar Rarara a nan, to za ka ga tawa a kusa da ita, domin shi allon rantsuwata ne; ba ni da kowa sai shi, shi ne komai nawa". In ji Asase.

👉Sanata Dino Melaye ya tashi hankalin yan Najeriya bayan yasa ₦ miliyan 5 ga duk wanda zai iya kawo ɗan ajinsu Shugaba T...
21/08/2026

👉Sanata Dino Melaye ya tashi hankalin yan Najeriya bayan yasa ₦ miliyan 5 ga duk wanda zai iya kawo ɗan ajinsu Shugaba Tinubu na firamare ko sakandare, wannan ƙalubalen ƴan adawa ke iƙirarin har yanzu ba a amsa ba saboda rashin bayanai na ilimi. Shi, Melaye ya ce kyautar ta shafe tsawon watanni ba wanda ya lashe, hakan ke tabbatar da cewa rayuwar shugaban ƙasar ba tabbas, magoya bayan Tinubu sun musanta labarin ta hanyar nuna bayanansa na ilimi mai zurfi da aka tabbatar bisa doka. Abokan karatunsa na jami'a biyu da aka tabbatar daga Jami'ar Jihar Chicago - Olajide Adeniji, wanda ya shigar da takardar rantsuwa a kotun Amurka, da Durojaiye Ogunsanya, wanda ya kare Shugaban a gidan talabijin na ƙasa - sun tabbatar da cewa sunyi karatu tare da Tinubu a aji a 1979. Amma kuna ga meye haɗin zuwa makaranta da shugabanci?

19/08/2026

Alhamdulillah alah kulli halin

Address

Awala Tudun Wada Gusau
Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarari Hausa news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share