06/03/2023
SAKON GODIYA TARE DA KIRA NA MUSAMMAN DAGA SHUGABAN KAMFANIN AMINU WAKSONG YECO BUSINESS COMPANY MARADUN.
Amadadin shugaban kamfanin Activist Aminu Waksong Maradun tare da mataimakan sa, Na mika sako na Godiya da kuma jinjina Zuwa ga Ilahirin Mambobin wannan kamfani a bisa fitowa da s**a yi tare da Iyalan su kuma s**a jajirce wajen Zaben Shugaban kasa da Yan Majalisar dattijai da kuma Yan Majalisar Wakilai na Abuja, Wanda ya gabata. Wanda Allah (SWT) Cikin ikon sa duk anyi Nasara Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasa. AL-hamdulil-lah wannan Babbar Nasara ce a garemu, inda muka bayar da karfin mu da lokacin mu anyi Nasara.
Haka Zalika Shugaban wannan kamfani yayi kira Zuwa ga Mambobin wannan kamfani da su fito kwansu da kwarkwartasu Maxan su da Matan su domin Marawa Maidararaja Gwamnan Jihar Zamfara Bello Dan Maradun baya akan Neman komawa saman kujerar sa ta Gwamnan Jihar Zamfara karo na biyu, Wanda zai gudana a ranar Assabar 11-03-2023. Shugaban wannan kamfani yayi kiran ne yayin da yaga Zaben na karatowa, Haka Zalika ya bayyana Members Din tamkar kariya suke a wannan kamfani domin sun fito ranar farko ta zabe kuma sun bayar da Gudunmuwa sosai Saboda haka Ana kira zuwaga Mambobin da su kara bada hadin kai na Ganin an samu Nasarar sake kafa Gwamnanati In Sha Allahu.
Nasarar Wannan Gwamnanati Nasarar mu Ce, Faduwar Gwamnanati Faduwar mu Ce, saboda haka Ana kara kira ga kowa ya fito yaje wajen Runfar sa, ya yi zabe yasa ayi zabe, kuma ya kasa ya tsare runfar sa Dan Ganin Maidaraja Governor Bello Matawalle ya samu Nasara. Allah ya bamu Cikakkiyar Nasara da galaba a wannan Zabe. Allah ya Maimaita Muna Mulkin Matawallen Zamfarawa Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.
Rahoto:-
Sarkin Samari
Publicity Secretary Waksong yeco Business Maradun.