Danhauwa foundation for zannan bungudu

Danhauwa foundation for zannan bungudu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Danhauwa foundation for zannan bungudu, Political organisation, Gusau.

13/09/2026

Hon Abdul Malik zubairu zannan zamfarawa three years in office

13/09/2026

Hon Abdul Malik zubairu zannan zamfarawa,ya gwangwaje masoyansa da romon dimukuradiyya!!!

Hon Abdul Malik zubairu zannan zamfarawa yasake halin nasa                 Dan majalisa mai wakiltar Maru/bungudu ya bad...
13/09/2026

Hon Abdul Malik zubairu zannan zamfarawa yasake halin nasa


Dan majalisa mai wakiltar Maru/bungudu ya bada Gudummawar Kudi naira Milion Dari (100m)zuwa ga Jami,ar Federal University Of Health Sciences and technology Tsafe.

Haka kuma ya kara da Alkawarin Gina masu Sabuwar Clinic A cikin makarantar, wanda aikin zai fara bada jimawa ba.

Wannan Na daya daga cikin Tsarin Zannan Bungudu na baiwa ilimi da fannin lafiya fifiku domin amfanuwar Dubbban Al umma.

Allah ya saka masa da Alheri.

12/09/2026
ALHAMDULILLAH! SHEKARU 3 NA AIYUKAN ALHERI NA ZANNAN BUNGUDUAlhamdulillah, yau mun rufe littafin shekaru uku na wakilci,...
10/09/2026

ALHAMDULILLAH! SHEKARU 3 NA AIYUKAN ALHERI NA ZANNAN BUNGUDU

Alhamdulillah, yau mun rufe littafin shekaru uku na wakilci, hidima da ayyukan alheri na Maigirma Hon. Dr. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu, tare da bude sabon shafi na shekara ta hudu.

A cikin wannan gagarumin bikin, an gudanar da rabon motoci 100 ga magoya bayan Zannan Bungudu da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC, tare da rabon babura, kekunan ɗinki, transformers, computers, injinan ban ruwa da sauran kayan dogaro da kai.

Bikin ya samu halartar manyan baki da s**a hada da Maigirma Gwamna Dauda Lawal, Jagora Senator Abdul’aziz Yari, kuma DG Campaign na Shugaba Bola Ahmad Tinubu a karo na 2 kaka zaben 2027 manyan jagororin da ’yan Jam’iyyar APC sassa daban-daban na Jihar Zamfara, da kuma sarakunan gargajiya na Bungudu/Maru.

Wannan ba bikin shekaru uku kawai ba ne, biki ne na shekaru uku na wakilci, sadaukarwa, hidima da ayyukan alheri da s**a taba rayuwar al’umma a fannoni daban-daban, a Bungudu/Maru, Jihar Zamfara da ma Najeriya baki daya.

Mun rufe shekara ta uku da godiya ga Allah da goyon baya da fatan Alheri da al'ummah keyi muna, tareda bude shekara ta hudu da zimma lunki sabbin ayyuka In Sha Allahu

DG Zannan Bungudu New Media & Publicity

ZAMA NA MUSAMMAN DA MALAMMAI DA MASU RUWA DA TSAKI NA KARAMAR HUKUMAR BUNGUDU WANDA YA GUDANA A MASARAUTAR BUNGUDU.Dan M...
09/09/2026

ZAMA NA MUSAMMAN DA MALAMMAI DA MASU RUWA DA TSAKI NA KARAMAR HUKUMAR BUNGUDU WANDA YA GUDANA A MASARAUTAR BUNGUDU.

Dan Majalisar Wakilai Hon Dr. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu Ya Halarci Taron Malammai Da Masu Ruwa da Tsaki Dake Masarautar Bungudu Karkashin Jagorancin Mai Martaba Sarkin Fulanin Bungudu Alh. Hassan Attahiru (MFR).

Taron Ya Mayarda Hankali Ga Addu’o’i Na Musamman Zuwaga Wannan Gari Na Bungudu Tareda Neman Tsari Ga Ubangiji, Muna Rokon Allah Ya Kara Kawo Mana Zaman Lafiya Mai Dorewa Amin.

Muhimmiyar Sanarwa!!!Taron Bukin shekara 3 na Zannan Bungudu ya tashi daga 11 na safe ya  dawo karfe 10 na safen Gobe, B...
09/09/2026

Muhimmiyar Sanarwa!!!

Taron Bukin shekara 3 na Zannan Bungudu ya tashi daga 11 na safe ya dawo karfe 10 na safen Gobe, Bisa Wani muhimmin zama da zasu Gudanar na Masu Ruwa da tsaki a Goben,

Don haka Muke Sanar da Mahallarta taro cewa kowa zai taso da wuri domin Shaidar wannan buki da kaddamar da kayan arzukka Zuwa Ga al'umma ba tare da bata Lokaci ba domin ana bukatar a Fara da wuri a Kammala da wuri domin baiwa Shugabanni Damar yin ayyukkansu na Gaba.

Allah yasa mu wanye lafiya ya saka Albarka aciki. Allah ya kawo kowa Lafiya Kuma ya mayar da kowa Gidansa lafiya.

07/09/2026

SANARWA TA MUSAMMAN.!

Sanarwar taron bukin cika shekaru ukku (03), Na mai girma Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bunguɗu da maru a zauren majalisah ta goma, Hon (Dr), Abdulmalik Zubairu (Zanna Bunguɗu), da rabon motoci sama ga ɗari (100), da transformers ranar Alhamis goma ga watan satumba na shekarar dubu biyu da ashirin da shidda 10/9/2026 a garin Bunguɗu da misalin karfe goma sha ɗaya na safe 11:00am in sha Allah

HON. ABDULMALIK ZUBAIRU ZANNAN BUNGUDU YA HALARCI TARON ƘADDAMAR DA TINUBU SUPPORT GROUP (TSG) A JIHAR KANOMai Girma Ɗan...
05/09/2026

HON. ABDULMALIK ZUBAIRU ZANNAN BUNGUDU YA HALARCI TARON ƘADDAMAR DA TINUBU SUPPORT GROUP (TSG) A JIHAR KANO

Mai Girma Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Maru da Bungudu, Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu, Ya halarci taron ƙaddamar da Tinubu Support Group (TSG) wanda aka gudanar a yau a jihar Kano.

Taron ya samu halartar ɗimbin magoya baya daga sassa daban-daban, inda aka bayyana ƙudurin ci gaba da ƙarfafa goyon baya ga shugaban ƙasa gabanin zaɓen shekarar 2027.

An rufe garin Kano gaba ɗaya a yau domin ƙaddamar da Tinubu Support Group (TSG) a kakar zabe Mai zuwa 2027

Address

Gusau
33209812

Telephone

+2348033668025

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Danhauwa foundation for zannan bungudu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Danhauwa foundation for zannan bungudu:

Shortcuts

Share