Zamfara State APC Network Awareness

Zamfara State APC Network Awareness Wannan shafi an buda shi ne domin wayar da kan jama'a bisa kyakkyawar manufar jam'iyyar APC da Kuma kare martabar jam'iyyar.

Ga dukkan alamu baya za ta haihu. Za ta haifi 'Da, kuma 'Dan shege, kuma makaho.Komawar Matawalle APC!!!
27/06/2021

Ga dukkan alamu baya za ta haihu. Za ta haifi 'Da, kuma 'Dan shege, kuma makaho.

Komawar Matawalle APC!!!

25/06/2021

Mu 'ya'yan Jam'iyyar APC mun gamsu da cewa Allah shi ke ba da mulki ba mutum ko Jam'iyya ba. Wannanne dalilin da yasa muka tsaya kai da kafa cikin Jam'iyyar mu.

Su ko 'yan PDPn Zamfara ba su yarda da imanin Allah ke ba da mulki ba. A tunanin su Jam'iyyar APC ke ba da mulki. To gamu gane! Jam'iyyar APC dai na da 'yan Takara kamar irin su:

Sanata Kabiru Marafa

Hon. Muktar Shehu Idris

Hon. Aminu Sani Jaji

Hon. Mahmud Aliyu Shinkafi

Dr. Dauda Lawan Dare

Dr. Ibrahim Shehu Bakyauye

Hon. Sagir Hamida

Idan Matawalle ya dawo APC, zai zama 'dan Takara na 8.

TALAKA YA GA TA KANSA A JAHAR ZAMFARA!Gwamnatin PDP ta Matawallen Maradun na cika shekaru biyu bisa karagar mulki amma b...
09/06/2021

TALAKA YA GA TA KANSA A JAHAR ZAMFARA!

Gwamnatin PDP ta Matawallen Maradun na cika shekaru biyu bisa karagar mulki amma babu abu ko guda da zakace Talaka ya amfana da shi. A cikin mafi yawancin jawaban Gwamna, yana mai maita cewa ya sabunta gidan Gwamnati tare da gina Masaukin ba'ki na shugaban Kasa da Mataimakin shi. Haka, yace ya gida Masauki na Gwamnoni 36.

Tambaya a nan, shin

Talakan Zamfara nawa ne ke iya zuwa gidan Gwamnati?

'Yan gudun hijira na kauyuwan Zamfara da 'yan Ta'adda ke rabawa da muhallan su, suna da Masauki a cikin wadannan Masaukai da gwamna ya gina cikin gidan Gwamnati?

Abu na biyu, Gwamna na ta ikirarin ya gina Filin Jirgi. Shin Filin Jirgin ya fara aiki da ake ikirarin an gina cikin ayyukan Gwamnati na shekaru biyu?

Gwamna zai raba Motoci ga Alkalan Kutonan shari'ar musulunci, to su na manyan Kutona fah (high Court)? Idan yace na Kutonan shari'ar musulunci kawai zai ba, sai muce saboda suna taimakawa zaluncin da yakeyi ne ya sa zai ba su. Sannan menene alfanun Motocin ga Talakan Zamfara?

Sarakuna da Gwamna yace zai ba Motoci har ake lissafa ba da Motocin cikin ayyukan Gwamnati na shekaru biyu, shin Sarakunan da aka tantance zai ba ko hadda wadanda ake zargi da hannu cikin aika-aika da 'yan Ta'adda ke yi Zamfara? Sannan menene alfanun Motocin ga Talakan Zamfara?

Gwamna yace za ayi taron ranan Dimukuradiyya. Shin mai zan fadawa Talakawan jahar Zamfara shawan shekaru biyu yana mulkin su?

Wallahi Talaka yaga ta kan sa a jahar Zamfara.

04/06/2021

INNALILLAHI wa'inna'ilaihi RAJI'UN!!!

Alh. Bashir Ataka, Allah ya kyauta. Taka ta kare. Allah ya tsare 'yan baya.

Ya Allah duk abinda zai kawo cikas ga zamuwar jagoran Jam'iyyar APC na jahar Zamfara a matsayin shugaban Jam'iyya na Kas...
16/04/2021

Ya Allah duk abinda zai kawo cikas ga zamuwar jagoran Jam'iyyar APC na jahar Zamfara a matsayin shugaban Jam'iyya na Kasa Allah ka kawar mana da shi alfarmar wannan Wata.

Muna jin dadi duk lokacin da muka ga Gwamna Bello Matawalle yayi koyi da kyawawan ayyukan alkhairi na jagoran Jam'iyyar ...
15/04/2021

Muna jin dadi duk lokacin da muka ga Gwamna Bello Matawalle yayi koyi da kyawawan ayyukan alkhairi na jagoran Jam'iyyar APC Dr. Abdul'azez Yari Abubakar.

Sanin kowa ne cewa shekarun Gwamna Bello Matawalle sha biyu a Majalisar Wakilai yana wakiltar kananan hukumomin Maradun da Bakura, amma ko sau guda ba a taba jin ya shirya shan ruwa ko da abokai nai ba.

Allah ya sakawa Malam Abdul'azez Yari Abubakar da mafificin alkhairinsa bisa wannan namijin kokari da yayi. Haka, muna jinjina ga Gwamna Bello Matawalle da baiyi girman kai wajan koyi da Malam Abdul'azez Yari ba.

Tambaya anan itace, shin Gwamna Bello Matawalle yayi koyin bada SALLAH kamar yadda Malam Abdul'azez Yari yayi?

14/04/2021

Muna kira ga Kwamishinan Addini na jahar Zamfara cewa kada ya yarda a sake bata mishi suna irin yadda akayi mishi bara.

12/04/2021

Tuni babban Kwamitin rabon kayan tallafin Azumi da jagoran Jam'iyyar APC na jahar Zamfara His Excellency Dr. Abdul'azez Yari Abubakar, ya samar ga al'ummar shi, ya fara rarraba kayan. Ya zuwa yanzu, Kwamitin ya samu nasarar hannunta tallafin ga kwamitin Kananan hukumomin:

1. Shinkafi

2. Kaura Namoda

3 Zurmi

4. Birnin Magaji

Babban Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Hon. Bello Dan Kande Gamji (Walin Bakura) yana aiki tukuru domin ganin ya sauke nauyin da aka aza mishi.

Shugaban babban Kwamitin yayi kira ga kwamitotan kananan hukumomi da suji tsoron Allah su aiwatar da rabon kayan kamar yadda jagora ya umurta.

10/04/2021

Bincike ya nuna cewa jahar Zamfara ta afka cikin har kar ga ta banza; WANKIYA! Ya zuwa yanzu ta wanki 15M.

07/04/2021

Yanzu muka fahimci dalilin komawar Anas Abdullahi Kaura, PDP. Gwamnonin APC, Allah ya mayar muku da alkhairi!

A cigaba da shirye-shirye da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ke yi na kutsowa cikin Jam'iyyar APC ta ko wane hali. Yau, ...
05/04/2021

A cigaba da shirye-shirye da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ke yi na kutsowa cikin Jam'iyyar APC ta ko wane hali. Yau, 5/4/2021, ya gayyaci Gwamnonin Jam'iyyar APC, ciki hadda shugaban riko na Jam'iyyar APCn, Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni, Gwwmnan jahar Kebbi, Bagudu da Gwamnan jahar Jigawa, Badaru, ya ba su cin hancin gidan masaukin baki na jahohin su, da gwamnatin jahar Zamfara ta gina mu su.

Babban abunda ya ba kowa mamaki shine irin yadda aka kammala taron cin hancin ba tare da ambata maganar WANKAN Gwamnan zuwa Jam'iyyar APC ba.

A cewar 'yan PDPn, a gobe Talata 6/4/2021 ne Gwamnan zai aiyana ficewa daga Jam'iyyar shi ta PDP zuwa Jam'iyyar APC. Wasu na ganin zuwan su Mai Mala Buni, na da alaka da ficewar Gwamnan a gobe. Zuwa yanzu da yawa cikin al'ummar Zamfara sun saki kari kan maganar WANKA da Gwamnan zaiyi a gobe.

Muna rokon Allah ya kara daukaka Jam'iyyar APC, da jagoran Jam'iyyar APC na jahar Zamfara Dr. Abdul'azez Yari Abubakar.

04/04/2021

GASKIYA KULLUN SUNANTA GASKIYA

Ga dukkan alamu kucce-kucce da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ke yi na barin Jam'iyyar shi ta PDP zuwa Jam'iyyar Mutanan kirki ta APC ba ya rasa nasaba ko ala'ka da zargin da yayi na wasu manyan mutane da hannu cikin matsalar tsaron jahar Zamfara.

'Ya'yan Jam'iyyar APC mu godema Allah. Wannan ya nuna karara cewa jagororin mu da aka zarga a lokota da s**a wuce da hannu cikin matsalar tsaron jahar Zamfara ba gaskiya ba ne. Sau da yawa maganar fatar baki ke wanke wanda ake zargi. Haka, aiki a aikace shima na wanke zargi a kan wanda ake zargi. Ko gwamna Bello Matawalle ya dawo APC ko kada ya dawo APC, wannan ya muna Jam'iyyar APC, jagororinta da mabiyanta ba su da hannu ko kadan cikin wannan matsala.

Allah ka kara dora gaskiya a kan karya tayi mata bugun Ka'dan Mahaukaciya.

Address

Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamfara State APC Network Awareness posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Zamfara State APC Network Awareness:

Share