Dairar Gumel

Dairar Gumel Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dairar Gumel, Public Service, Gumel, Gumel.

UpdateSheikh Ibraheem Zakzaky (H) has offered Qurban after observing Eid Adha at his Abuja residence.      10/ZulHijja/1...
27/05/2026

Update

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) has offered Qurban after observing Eid Adha at his Abuja residence.






10/ZulHijja/1447
27/05/2026

Hausa

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya yi layya yau Laraba 10 ga Dhul Hijja 1447, wanda yayi daidai da 27/05/2026, a gidansa dake Abuja.






10/ZulHijja/1447
27/05/2026

Shahadar Imam Muhammad Al-Baqir (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) 7 ga Zulhijja. Lokacin da Hisham Ibn Abdul Malik y...
24/05/2026

Shahadar Imam Muhammad Al-Baqir (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) 7 ga Zulhijja.

Lokacin da Hisham Ibn Abdul Malik ya karbi mulki, mulkinsa ya koma na ta'addanci da zalunci. Siyasar zalunci da azabtarwa ita ce ta haifar da tawayen su Shahid Zaid ɗan Imam Ali Al-Sajjad (SA) wanda ya yi shahada tare da sahabbansa aka ƙone gawarsu.

Haka kuma Hisham ya tsanantawa ɗaliban Imam Muhammad Al-Baqir (SA), duk da haka waɗannan matakan zalunci ba su hana yaɗuwar musulunci da wayar da kan Al'umma akan addini ba. Hisham Ibn Abdulmalik ya bada umarnin sanya wa Imam Muhammad Al-Baqir (SA) guba wanda ya zama sanadin shahadarsa (S) a tafarkin Allah. Imam yayi shahada yana da shekaru 57.

السلامُ عليكَ يا حجة الله على الخلق أجمعين،

أعظم الله أجورنا وأجوركم بذكرى شهادة الإمام الباقر عليه السلام






07/ZulHijja/1447
24/05/2026

An rawaito daga Imam Musa al-Kazim (A.S):Ya kasance yana cewa wa ɗansa:“Wannan ɗan naku, Aliyu ɗan Musa ar-Ridha, shi ne...
29/04/2026

An rawaito daga Imam Musa al-Kazim (A.S):
Ya kasance yana cewa wa ɗansa:
“Wannan ɗan naku, Aliyu ɗan Musa ar-Ridha, shi ne malamin gidan Annabi (Ahlul Baiti). Ku tambaye shi game da addininku, kuma ku riƙe abin da yake faɗa muku. Lalle ni na ji daga mahaifina, Ja’afar ɗan Muhammad (A.S), sau da dama yana cewa mini:
‘Lalle malamin gidan Annabi (Ahlul Baiti) yana cikin zuriyarka. Da ace na riske shi, da na riƙe shi da ƙarfi. Lalle shi yana da suna iri ɗaya da Amirul Mu’minin Ali (A.S).’”
Madogara: Muntaha al-Aamal
Muna taya Muminai Murna zagayowar, ranar haihuwar daya daga cikin limaman shiriya, a bayan Maaiki (sawa).

WALIMA DAGA FUDIYYA GUMEL TA AUREN DAN GIDAN WAKILIN YAN UWA  NA GUMEL MALAM MANSUR YUSUF GUMEL.  Da yammacin yau Talata...
07/04/2026

WALIMA DAGA FUDIYYA GUMEL TA AUREN DAN GIDAN WAKILIN YAN UWA NA GUMEL MALAM MANSUR YUSUF GUMEL.

Da yammacin yau Talata 07/042026 aka gabatar da, walimar Taya murna ta auren Ahmad El Mansur Yusuf Gumel, da Amaryarsa Fatima Abubakar Nguru. Wanda aka daura ranar asabar, 04/04/2026 da ta gabata, a garin na Nguru. An gabatar da Walimar ne, a Fudiyya Islamiyya Gumeldake kan titin Hadejia. Malam Kabiru Musa ya gabatar da, jawabi a muhallin.
Munayiwa amarya da ango fatan alkhari Allah ya kare fitina ya bada zuriya dayyiba bi haki Muhammad wa Ali Muhamma.
07/04/2026

WA'AZIN GORON SALLAH DAGA GARIN GUMEL Yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (h) na garin Gumel sun fara gabatar da Wa'azin go...
20/03/2026

WA'AZIN GORON SALLAH DAGA GARIN GUMEL

Yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (h) na garin Gumel sun fara gabatar da Wa'azin goron Sallah yau a unguwar kofar yamma Gumel.

Shidai wannan taron na goron Sallah ana gabatar dashi ne domin taya Al'ummar musulmi murna kammala ibadar azumin watan Ramadan da kuma ƙara tunatar da al'ummar musulmi darussan da ya kamata a dauka na ibada da aka gudanar a Ramadan.

Babban abinda ake so ga Musulmi ya dauka shine kamewa daga aikata dukkan wani aikin zunubi wanda Allah baya so, da kuma aikata kyawawan ayyuka na ibada da Allah yake so. kamar Zikirori, salloli,sadakoki,kyaututtuka,karatun Alkur'ani, addu'o'i, sada zumunci Da sauransu. Wanda anaso bayan azumi a bawa ya tsayu da aikata Kyawawa, da gujewa aikata mummuna.

Wakilin yan uwa na Gumel Malam Mansur Yusuf Gumel ne ya gabatar da jawabi a muhallin. wanda daga karshe ya taɓo abubuwan da suke faru na siyasar duniya da kuma Yaƙin al'ummar musulmi da ake a kasashen duniya musamman IRAN da makwabtan ta.

Matsayar mu shine: Muna tare da gaskiya da ma'abota gaskiya. Muna tare da mazlumai.

Bama tare da ƙarya da masu mara mata baya. bama tare da Azzalumai da masu mara mata baya kowaye.





Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky, na Dairar Gumel sun bi sahun Al'umar Duniya, wajen gabatar da Muzahar...
13/03/2026

Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky, na Dairar Gumel sun bi sahun Al'umar Duniya, wajen gabatar da Muzaharar Qudus ta Duniya.

Wafatin Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) 21 Ga Watan Ramadan Shekara Ta 40 Bayan Hijira Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) ya y...
11/03/2026

Wafatin Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) 21 Ga Watan Ramadan Shekara Ta 40 Bayan Hijira

Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) ya yi shahada a ranar 21 ga watan Ramadana, shekara ta 40 bayan hijira (40 AH), bayan da Abdurrahman bn Muljam ya soka masa takobi mai dafi a masallacin Kufa yayin sallar asuba. Ya yi wafati yana da shekaru kusan 63 a duniya, wanda hakan ya kawo karshen halifancinsa. An soka masa takobi a Masallacin Kufa, Iraki, a ranar 19 ga Ramadana, baiyi wafati ba sai bayan kwanaki 2, a ranar 21 ga watan Ramadan.

Imam Ali (AS) ya bar gado mai girma na ilimi, adalci, da sadaukarwa, kuma ana tunawa da shi a matsayin daya daga cikin mafi girman sahabbai da kuma shugabannin Musulunci.

07/03/2026

AYATULLAH ALI KHAMENE'I| Garkuwar Musulunci, Tafiyar Da Bata San Rauni Ba

Ku kalla tare da NASMA CREW

01/03/2026

Ana sanar da yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yakoub Al Zakzaky h, na Dairar Gumel cewa akwai Muzahara yau. Wadda zaa da yamma, karfe hudu 4:00 pm. Baa daukema dukkan Yan Uwa ba.
Allah ya bada ikon zuwa.

Kafin ka mutu, ka tabbata ka faɗa wa ’ya’yanka da kuma masu tasowa da za su zo a gaba cewa mun shaida wani zamani da wan...
01/03/2026

Kafin ka mutu, ka tabbata ka faɗa wa ’ya’yanka da kuma masu tasowa da za su zo a gaba cewa mun shaida wani zamani da wani mujahidi mai shekara 86 ya tsaya shi kaɗai yana yaƙin kare Musulunci, alhali kuwa duk duniya da kuma ƙasashen Musulmi sun nutse cikin barcin shiru da ko-in-kula. Duk da tsufansa, bai gaji ba kuma bai lanƙwashe ba; sai dai ya ci gaba da ɗaga muryar gaskiya. Wannan wani babi ne na tarihi da al’ummomi na gaba za su karanta cikin mamaki da alfahari. Allah Ya jikan wannan babban mutum, lallai zance be saba da aiki n ku ba, Ya kuma ba gaskiya nasara.

SANARWA:Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ  اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُح...
20/02/2026

SANARWA:

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ

وَمَا كَانَ الْمُؤْمِنُونَ لِيَنفِرُواْ كَآفَّةً فَلَوْلاَ نَفَرَ مِن كُلِّ فِرْقَةٍ مِّنْهُمْ طَآئِفَةٌ لِّيَتَفَقَّهُواْ فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُواْ قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُواْ إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ.

ALHAMDULILLAH! TASHAR ABS NA SANAR DA AL'UMMA FARA SHIRYE SHIRYANTA A TAURARON ƊAN ADAM (SATELLITE) DAGA GOBE KARFE 7:00AM NA SAFE INSHA ALLAH TA’ALA.

TASHAR ZATA FARANE DA ADDU'A DA JAWABIN BUƊEWA DAGA BAKIN JAGORA (H), SANNAN ZA'A SA TAFSIRIN JAGORA (H) A MAIMAITA SAU 4, NA FARKO KARFE 9:00PM, KARFE 2:00PM, KARFE 5;00PM, SAI KUMA KARFE 9:00PM, NA DARE. SAURAN SHIRYE SHIRYE ZA SU ZO BISA MATAKIN GWAJI.

MUNA ROƘON ALLAH YA YI MANA TAUFIƘI A CIKIN WANNAN WATA MAI ALFARMA DA YIN AYYUKAN IBADODI. YA KUMA NUNA MANA ƘARSHENSA LAFIYA.

ZA'A SAMU TASHAR ABS A WANNAN FREQUENCY:

Eutelsat 16est/Amos17 Frequency 12169/H/30000

WASSALAM






02/Ramadan/1447
20/02/2026

Address

Gumel
Gumel

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dairar Gumel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category