13/04/2026
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ph'D ya karɓi baƙuncin ɗan takarar majalisar tarayya na ƙananan hukumomin Bakori da Ɗanja Amb. Abduljabar Surajo Guga.
Ranar Juma’a 13th April, 2026 Amb. Abduljabbar Surajo Guga ya ziyarci gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD a ofishin dake fadar gwamnatin jihar Katsina.
Ziyarar na zuwa ne a cigaba da bin shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Apc ta jihar Katsina domin tabbatar masu da aniyar sa ta tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakori da Ɗanja.