Pamtamiya Onlineupdate

Pamtamiya Onlineupdate Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Pamtamiya Onlineupdate, Government Official, Gombe.

Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami  Ta Rabawa Al'ummar Anguwan Pantami Kyautar Naira Miliyan 15,620,000 Kamar Yadda Ta...
15/03/2026

Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami Ta Rabawa Al'ummar Anguwan Pantami Kyautar Naira Miliyan 15,620,000 Kamar Yadda Ta Saba Gudanarwa A Kowane Azumi

A jiya Asabar gidauniyar Professor Isa Ali Pantami karkashin jagorancin Alhaji Hassan Ali (Sintalin Pantami) da Ahmad Muhammad (Master) da Dan Kaden Pantami da Sarkin Malaman Pantami da Mai Goro Sale s**a jagoranci rabawa al'ummar anguwan Pantami da s**a hada da Dattawan anguwa, shugabannin jam'iyya, iyaye Mata da Matasa kyautar Naira Miliyan 15,620,000.

Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami ta dade tana rabawa al'ummar anguwan Pantami irin wa 'yan nan kyaututtukan tun a shekarun baya, wanda a wannan shekarar ta kara yawan kudin fiye da na shekarun baya.

Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya shafe shekaru da dama yana tallafawa jama’a a lokacin watan Ramadan, inda adadin tallafin ya karu a wannan shekarar. Sama da mutane 600 ne s**a samu tallafin kudin da gidauniyar ta raba a cikin anguwan Pantami.

15/03/2026
15/03/2026
07/03/2026

Professor Isa Ali Pantami




02/03/2026

Muna Alfahari da Kai Uban Gidanmu Professor Isa Ali Pantami




28/02/2026

Namu Kenan kuma Jagaban Mata Jamil Muhammad Gidado Amanan Professor Isa Ali Pantami Yayin Raba Kayan Abincin Azumi Wa Yan Uwa Musulmai




28/02/2026

Yadda Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami Ta Ƙaddamar Da Fara Raba Kayayyakin Abinci Fiye Da Buhu Dubu 12,500 Da Kuma Kuɗi Naira Miliyan 33,750,000 Ga Malaman Addini A Gombe.

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami   Ta Ƙaddamar Da Fara Raba Kayayyakin Abinci Fiye Da Buhu Dubu 12,500...
28/02/2026

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami Ta Ƙaddamar Da Fara Raba Kayayyakin Abinci Fiye Da Buhu Dubu 12,500 Da Kuma Kuɗi Naira Miliyan 33,750,000 Ga Malaman Addini A Gombe

Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami (PIP Foundation) ta ƙaddamar da raba kayan abinci kusan buhu 12,500 da s**a haɗa da shinkafa, masara, gero, s**ari, taliya (spaghetti da macaroni), da sauran su a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

Aikin raba kayayyakin abincin yana gudana ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Ahmad Walama (Sarkin Malaman Gombe), Dr. Abubakar Saidu (Tsohon babban daraktan asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe), Arch. Dahiru Saidu, da kuma uwar gidan Farfesa Isa Pantami, tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki, matasa, da mata.

Kayan abincin da ake rabawa sun haɗa da buhu 3,500 na shinkafa mai nauyin 50kg, buhu 1,000 mai nauyin 25kg, da kuma fiye da buhu 2,000 mai nauyin 10kg. Bugu da ƙari, akwai fiye da buhu 1,000 na gero da buhu 1,000 na masara. Sauran kayan sun haɗa da buhu 900 na kus-kus, fiye da buhu 2,500 na semovita, katan 500 na macaroni, da kuma fiye da buhu 150 na s**ari.

Ana raba waɗannan kayayyaki ne ga shugabannin addini, shugabannin al’umma, ‘yan siyasa, matasa, mata, marayu, da kuma mutane masu buƙata ta musamman. Kwamitin raba kayan ya tabbatarwa da jama’a cewa za a raba abincin ne a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, sai dai saboda yawan jama’a, ba kowa ne zai iya samu ba, sai waɗanda Allah ya ƙaddara suna cikin jerin waɗanda za su amfana.

Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya shafe shekaru da dama yana tallafawa jama’a a lokacin watan Ramadan, inda adadin tallafin yake sauyawa shekara bayan shekara. Waɗanda s**a amfana sun nuna godiyarsu ga wannan karamci wanda ya kawo farin ciki ga iyalansu, sannan sun yi wa Farfesa da tawagarsa addu’ar Allah ya saka musu da mafificin alkhairi.

Gidauniyar Farfesa Isa Pantami (PIP Foundation) ta ware zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 33,750,000 domin tallafawa malaman addini a Gombe. Gidauniyar ta daɗe tana tallafawa malaman addini a Gombe da ma Najeriya baki ɗaya. A shekarar da ta gabata, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ta hanyar wannan gidauniya, ya tallafa wa malaman Gombe da Naira miliyan 27 a jihar Gombe kaɗai, baya ga sauran tallafi. Dr. Umar Garba Dokaji ne yake jagorantar aikin raba tallafin ga malaman addinin.

Uwar gidan Professor Isa Ali Pantami    Hajiya Khadija Isa Ali Pantami, ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga al'umma dom...
26/02/2026

Uwar gidan Professor Isa Ali Pantami Hajiya Khadija Isa Ali Pantami, ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga al'umma domin sauƙaƙa musu gudanar da ibadar azumin Ramadana.

Hajiya Jamila, wadda ta wakilci uwar gidan Farfesan, ita ce ta kaddamar da rabon ga ’yan uwa musulmi, inda ta bayyana cewa wannan tallafi na nufin rage raɗadin tsadar rayuwa da kuma neman yardar Allah a wannan wata mai alfarma.

Wannan na cikin kwaryan jihar Gombe ne sauran kananan hukumomin nasu yana nan tafe In Sha Allah.

Address

Gombe

Telephone

+2348184494467

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Pamtamiya Onlineupdate posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share