Nanasiyya movement

Nanasiyya movement Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nanasiyya movement, Political organisation, Akko LGA ., Gombe.

KUNGIYAR NANASIYYA DOOR TO DOOR TA ZIYARCI HON.AISHATU MB AHMAD.Shahararriyar kungiyar nan ta Nanasiyya Door to Door ta ...
12/07/2022

KUNGIYAR NANASIYYA DOOR TO DOOR TA ZIYARCI HON.AISHATU MB AHMAD.

Shahararriyar kungiyar nan ta Nanasiyya Door to Door ta samu daman ziyartar Magayakin Akko Hon.Aishatu MB Ahmad a gidanta .

Ziyaran nada nasaba ne da jaddada alkawari tare da tayata murnar lashe zaben fidda gwani da tayi.

Muna Addu'ar Allah yasa tayi nasara ababban zabe dake karatomu.

Ahmad Abdullahi Deputy✍️
12/7/2022.

IYAYE MATA SUN KIRA WANI TARO DOMIN KARA JADDADA GOYON BAYANSU GA HON.AISHATU MB AHMAD A GARKO WARD.Wasu gungun iyaye ma...
27/06/2022

IYAYE MATA SUN KIRA WANI TARO DOMIN KARA JADDADA GOYON BAYANSU GA HON.AISHATU MB AHMAD A GARKO WARD.

Wasu gungun iyaye mata mazauna Garko Ward sun kira wani taron kara tuntubar juna tare da tabbatar da alkawari tsakanin su da Hon.Aishatu MB Ahmad.

Zaman wanda shugabar Mata na Garko Ward Hajiya Fatima Danladi (Aunty Fancy ) ta jagoranta yayi matukar kayatarwa kuma ya samu halartar iyaye Mata daga addinai mabanbanta .

Akarshe sunyi alkawarin hada karfi da karfe wajen kawo sauyi a kujerar majalisar tarayya mai wakiltar Akko.

Muna fatan Allah ya fadawa wannan kuduri nasu.

MASU RUWA DA TSAKIN JAM'IYYAR PDP(STAKEHOLDERS) SUN JADDADA GOYAN BAYANSU GA HON.AISHATU MB AHMAD.Mai girma Magayakin Ak...
21/04/2022

MASU RUWA DA TSAKIN JAM'IYYAR PDP(STAKEHOLDERS) SUN JADDADA GOYAN BAYANSU GA HON.AISHATU MB AHMAD.

Mai girma Magayakin Akko Hon.Aishatu MB Ahmad ta samu daman ganawa tareda gabatar da tallafi na makuden kudade ga shugabannin jam'iyyar PDP (Party Stakeholders).

Hon.Aishatu MB Ahmad tunma kafin lokacin takara ta saba gabatar da wadannan tallafi ga shugabannin jam'iyyar PDPn a lokuta mabanbanta .

Da suke jawabi masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP na Akko sunce ya zama musu wajibine su tabbatar da goyon bayansu ga Hon.Aishatu MB Ahmad ganin cewa itace tayi zarra wajen rike jam'iyyar PDP dama shugabannin ta .

Muna rokon Allah ya baiwa Hajiya nasara azaben fidda gwanin dake karatomu a wata mai kamawa .

Ahmad Abdullahi Deputy✍️
21/4/2022.

16/04/2022
HON.AISHATU MB AHMAD DA ABOKAN AIKINTA SUN GANA DA GWAMNAN JIHAR BAUCHI.Mai girma Magayakin Akko Hon.Aishatu MB Ahmad ta...
14/04/2022

HON.AISHATU MB AHMAD DA ABOKAN AIKINTA SUN GANA DA GWAMNAN JIHAR BAUCHI.

Mai girma Magayakin Akko Hon.Aishatu MB Ahmad tareda abokan aikinta na zauren amintattun jam'iyyar PDP na matakin Nigeria baki daya sun amsa gayyatar Gwamnan jihar Bauchi His.Execellency Sen.Bala Muhammad (Kauran Bauchi).

Ganawar nada nasaba ne da neman hadin kansu ganin sune jam'iyyar a matakin kasa tare da bayyana kudurin sa na takaran shugaban kasar Nigeria .

Idan baku manta ba a kwanakin baya Hon.Aishatu MB Ahmad sunyi irin wannan ganawar da tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Alh.Atiku Abubakar a gidansa dake Abuja.

Muna Addu'ar Allah ya karawa Hon.Aishatu MB Ahmad daukaka a dukkan mataki.

Ahmad Abdullahi Deputy✍️
Thur 14,April 2022.

"INSHA ALLAHU BAZAMU TABA CIN AMANAR HON.AISHATU MB AHMAD BA"___INJI SHUGABANNIN PDP.Da safiyar yau lahadi 10/4/2022 Hon...
10/04/2022

"INSHA ALLAHU BAZAMU TABA CIN AMANAR HON.AISHATU MB AHMAD BA"

___INJI SHUGABANNIN PDP.

Da safiyar yau lahadi 10/4/2022 Hon.Aishatu MB Ahmad ta gana da shugabannin jam'iyyar PDP na karamar hukumar Akko wadanda basuda kuri'a a zaben fidda gwani domin ta musu goma ta arziki na kyautan kudade a cikin wannan wata mai alfarma.

Hon.Aishatu MB Ahmad ta bayyana cewa dayawan 'yan siyasa basa la'akari dasu ganin cewa su basuda kuri'a a zaben cikin gida amma ita a gunta lallai su masu kuri'a ne sabida ko babu komai suke tsayawa a gindin akwatuna domin ganin jam'iyyar PDP tayi nasara a zabukan gama gari.

Da suke maida martani Shugabannin Jam'iyyar PDPn sunce tabbas basu taba haduwa da wata ko wani dake tsaye tsayin daka kan jam'iyyar PDP irinta ba ,kuma sun yaba mata bisa tallafa musu da takeyi a lokutan aure ,jinya ,makaratun yara da sauransu, bugu da kari Shugabannin PDPn sun lashi takobin nemawa Hon.Aishatu MB Ahmad alfarma harta kai ga nasara .

Akarshe shugaban jam'iyyar PDP na Akko Hon.Baba S Fulani ya bayyana Hon.Aishatu MB Ahmad a matsayin jaruma kuma kashin bayan PDP a karamar hukumar Akko tareda mika mata godiya bisa hidimar da take akansu .

HON.AISHATU MB AHMAD TA CHANCHANCI YIN TAKARA A DUKKAN MATAKI.Ko shakka babu Hon.Aishatu MB Ahmad ta cika dukkan ka'idoj...
29/03/2022

HON.AISHATU MB AHMAD TA CHANCHANCI YIN TAKARA A DUKKAN MATAKI.

Ko shakka babu Hon.Aishatu MB Ahmad ta cika dukkan ka'idoji da ake la'akari dasu wajen tsaida 'Dan takara wanda al'umma da kuma mutanen jam'iyya zasuyi na'am dashi domin samun kyakkyawan wakilci kuma taci zabe batare da wahalarwa ba.

1.KYAUTATAWA 'YAN JAM'IYYA :-

Tun bayan zabukan 2019 Hon.Aishatu MB Ahmad ta dauki dakon jam'iyyar PDP wajen dafawa shugabanninta wanda sanadin irin ayyukan alkhairanta da kuma jajirtaccen jagora Hon.Baba S Fulani yau jam'iyyar PDP sha'awar shigowa cikinta ake ba dare ba rana .

2.ILIMI:-

Ilimi nada cikin ka'idan farko da ake dubawa wanda kuma alhamdulillahi Hon.Aishatu MB Ahmad ta samu gogewa wanda iliminta yakai ta tashi a ko'ina ta gabatar da kuduri kuma ta fafata muhawara da gogaggun 'yan siyasa domin kawo cigaba cikin yankinta.

4.TAIMAKON AL'UMMA:-

Hon.Aishatu MB Ahmad tayi ayyuka da dama na taimakon al'umma a karamin dama data samu wajen daukan aiki,tura 'yayan marasa karfi zuwa manyan jami'oin kasa,gina makarantu ,tallafin asibitoci dama ababayen more rayuwa wanda zata iya nunawa amatsayin abinda tayiwa al'umma domin siyasa yanzu ta koma mekayi ne ? bawai kaine wane ba.

5.KARBUWA WAJEN JAMA'A:-

Tabbas Hon.Aishatu MB Ahmad ta karbu matuka wajen jama'a ,kuma tanada farin jini da kyakkyawar alaka da mutane wanda hakan zai bata daman cin zabe akowani matakin kujera ta tsaya .

Muna fata shugabannin jam'iyyar PDP zasuyi la'akari da wadannan abubuwa da suke tattare da wannan baiwar Allah tareda kyakkyawan alaka dake tsakaninsu, su tabbatar mata da tikitin takarar kujerar majalisar tarayya a zaben fidda gwani dake karato mu .

Daga Ahmad Abdullahi Deputy.

March 29,2022.

GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA  GA SHUGABANNIN JAMA'IYYAR PDP NA AKKO.Da safiyar yaune shugabannin Jam'iyyar PDP na karamar huk...
28/03/2022

GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA GA SHUGABANNIN JAMA'IYYAR PDP NA AKKO.

Da safiyar yaune shugabannin Jam'iyyar PDP na karamar hukumar Akko s**a bayyana a gidan Hon.Aishatu MB Ahmad domin cika mata form dinta na takarar majalisar tarayya .

Amadadin dukkan masoyan ta muna godiya matuka da irin hadinkan da suke bamu.

Allah ya shige mana gaba.

MUDDIN AKA TSAYAR DA HON.AISHATU MB AHMAD KUMA ALLAH YA AMINCE MATA ,TO TABBAS ITA MAI IYA CIN ZABE NE.Shi Mulki Allah i...
26/03/2022

MUDDIN AKA TSAYAR DA HON.AISHATU MB AHMAD KUMA ALLAH YA AMINCE MATA ,TO TABBAS ITA MAI IYA CIN ZABE NE.

Shi Mulki Allah idan yaga dama zai baka shine batare da la'akari da jinsinka ,addini, ko kuma kabilarka ba. Haka zalika idan ya baka bawai kafi kowa kwarewa bane ,inkuma ya hanaka bawai kafi kowa gazawa bane .

Misali cikin hukunci irinna ubangiji a shekarar 2019 Alh.Ibrahim Hassan Dankwambo ko kaine hasidun iza hasada kasan cewa yafi abokin takararsa kwarewa,Ilimi,farin jini,karbuwa,chanchanta,da karfin iko amma da Allah ya tashi hukunci irin nasa sai yabaiwa 'Dan Alkali nasara badon yafi Dankwambo da komai ba.

Nayi wannan bayanine domin na jawo hankalin shugabannin jam'iyyar PDP musamman akaramar hukumar Akko da cewa shi faduwa a zabe kocin zabe wasu lokutan bawai suna nuna rashin nagartan 'Dan takara bane ,domin da rashin nagartan 'Dan takarane kawai ke jawo faduwa zabe da lallai Dankwambo bai fadi ba a zaben shekarar 2019 .

Ko shakka babu rashin nasarar jam'iyyar PDP a zaben majalisar tarayya mai wakiltar Akko a shekarar 2019 yanada nasaba da rigingimun cikin gida bawai rashin nagarta daga 'yar takarar mu ba ,wanda ko kaki Allah kasan hakan ya faru kuma bama fata hakan ya sake faruwa Insha Allahu.

Lallai Hon.Aishatu MB Ahmad ta chanchata ta kowani bangare domi tanada rikon amana irin na siyasa ,ta taimaki al'umma da dama kuma tayiwa jam'iyyar PDP rikon gaske lokacin da jam'iyyar keda bukatan hakan , tanada ilimi da gogewar da zata iya tashi ta gabatar da kuduri akan al'ummar ta koda kuwa a majalisar dinkin duniya ne ,Hon.Aishatu MB Ahmad mace ce da Allah ya h**e mata farin jinin da zata iya cin zabe a kowani mataki domin al'umma na tare da ita.

A irin ra'ayi nawa zan iya cewa a matakin kujerar majalisar tarayya lallai ba bukatan chanza 'yar takara sai dai kawai neman hadinkan 'ya'yan jam'iyya .

Allah ya bamu ikon biyayya ga duk wanda Allah ya baiwa nasara a zaben fidda gwani .

Ahmad Abdullahi Deputy✍️
Sat 26,March 2022.

LOKACI YAYI DA ZAMU HADA KAI BAKI DAYA MU GOYI BAYAN HON.AISHATU MB AHMAD.Tabbas muka hada kai kuma muka cire son zuciya...
26/03/2022

LOKACI YAYI DA ZAMU HADA KAI BAKI DAYA MU GOYI BAYAN HON.AISHATU MB AHMAD.

Tabbas muka hada kai kuma muka cire son zuciya to karban kujerar majalisar tarayya a karamar hukumar Akko zata zo mana da sauki ganin yadda akalan siyasar Gombe baki daya ke tafiya.

Hon.Aishatu MB Ahmad mace ce hazika data daga yatsa wajen taimakon al'umma ba tareda ta taba rike wani zababben mukamin siyasa ba kuma cikakkiyar 'yar siyasace da karanta yakai tsaiko.

Hajiya Nana tayiwa jam'iyyar PDP hidiman gaske wanda hakan ya nuna mana ba 'yar siyasace da zamu bari ta subuce mana ba ,ita tamkar kadarace a garemu da Allah S.W.A ya albarkace mu dashi .

Muna kara jaddada kiranmu ga shugabannin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Akko da su baiwa wannan baiwar Allah dama munada tabbacin cikin ikon Allah zafa cire mana kitse a wuta .

Muna Addu'ar Allah ya tabbatar mata da nasara a zaben cikin gida mai karatowa.

Nanasiyya Media Office.
26/03/2022.

*HON AISHATU MB AHMAD TA HALARCI AUREN YARAN GIDAN TUKUR LUMBI*A yammacin yau ne Mai girma hajiya Aishatu mb ahmad magay...
25/03/2022

*HON AISHATU MB AHMAD TA HALARCI AUREN YARAN GIDAN TUKUR LUMBI*

A yammacin yau ne Mai girma hajiya Aishatu mb ahmad magayakin Akko ta halarci bikin yaran tukur lumbi daya gudana a garin gombe.

yau juma'a hon Aishatu mb ahmad tayi addu'an Allah yasanya alkhairi acikin wannan aure.
✍️Adamu Hassan kumo.
25/3/2022

Address

Akko LGA .
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nanasiyya movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share