24/08/2026
HAPPY MAULUD, GOMBAWA
Ina taya daukacin al’ummar Gombe da Musulmi baki ɗaya murnar zagayowar Mauludin Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).
A wannan rana mai albarka, ina roƙon Allah Ya ƙara mana ƙaunar ManzonSa (SAW), Ya amsa ibadunmu, Ya kawo mana zaman lafiya, haɗin kai da albarka a jiharmu ta Gombe da ƙasa baki ɗaya.
Kamar yadda muka saba duk shekara, Munir Dankwambo Foundation za ta gudanar da rarraba ruwa da kayan zaki (sweet) ga al’umma a wajen taron Mauludi, domin ci gaba da nuna ƙauna da hidima ga jama’a.
Allah Ya saka wa dukkan masu halartar taron Mauludi da alheri, Ya sa mu ci gaba da rayuwa cikin aminci da fahimtar juna.
Happy Maulud, Gombawa!
Munir Dankwambo
Munir Dankwambo Foundation
The Following
Following
Governor Dankwambo
Professor Isa Ali Pantami