Juma'ar da Zatai Kyau.

Juma'ar da Zatai Kyau. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Juma'ar da Zatai Kyau., Political organisation, Fagge.

A. A. Zaura: Jumma’a Mai Kyau…Rahotanni masu inganci daga kowane lungu da sako na Jihar Kano, musamman a farfajiyar siya...
13/04/2022

A. A. Zaura: Jumma’a Mai Kyau…

Rahotanni masu inganci daga kowane lungu da sako na Jihar Kano, musamman a farfajiyar siyasa, suna nuni kan cewa, ba a taba yin wani dan siyasa mai dama, ba shi da damuwa, kamar Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura, wanda aka fi sani da A. A. Zaura ba. Wannan ya kara tabbatar da cewa Juma’a mai kyau, tun daga Laraba masu hankali ke gane ta!

Hakika, wata guguwa mai cike da launin canji na alheri ke rururwa a babbar birni, da har ta a kullum ake ganin tagomashin Alhaji A. A. Zaura da yunkurinsa na ganin an cimma nasara.

Bisa ga dukkan alamu, siyasar shekarar 2023 ta matasa ce, su ne ake ganin za su fi kowa taka mahimmiyar rawa a cikinta, saboda yadda shi ma kansa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a shekarun baya, ya marawa kudurin da tawagar wasu matasa s**a mika masa na a ba wa matasan dama su taka rawa a fagen mulki.

Shin wane ne Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura?
- Idan kana son fassara wannan bawan Allah, tilas ka tanaji wasu kyawawan kalmomi masu dangogin alheri!
- Idan kai matashi ne, to ka sani cewa sami abokin tafiya a wajen Zaura!
- Idan kuma kai dattijo ne, shakka babu, ka sami da-nagari mai biyayya ga iyaye, mai neman albarkar iyaye, mai tsananin girmama nag aba da shi.
- Idan kuma dan kasuwa ne kai, ko tantama babu, kana da abokin huldayyar kasuwanci!
- Idan kai matashi ne mai son wanka da kwalliya, to, ka sani ka zo gidanta!

A. A. Zaura matashi ne mai sanyin rai, mai hangen nesa, mai dubun-dubatar basira, wanda Allah Ta’ala Ya huwace ma sa ayyuka da dama. Wadanda s**a san Zaura, za su fada maka cewa gabanin shigarsa harkar siyasa ne, yake kan gaba wajen yi wa al’ummarsa hidima ta fuskoki da daman gaske. Ya riki harkar kasuwanci, tun lokacin da yake karatu a makarantar Sakandare.

A takaice dai, Alhaji Abdulsalam Zaura mutum ne mai dimbin basira da fasaha ta zamani, musamman ma, da ya shiga jami’a, ya sami digiri kan sha’anin mulki da tattalin arziki. A nan, ma ya yi zarra, inda kuma yake tunanin ya sanya karatunsa a aikace idan har Allah Ta’ala Ya ba shi damar samun nasara a zabukan da za a yi nan gaba a shekarar 2023.

Muradinsa ga Kanawa: A nan dai, ko ba a ce komai ba, A. A. Zaura ya karanci dukkanin lamura da jihar ke bukata a yau. Sannan daga cikin manyan muradunsa dai, yana da kudurin dorawa daga inda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye ayyukansa na alheri.

A kodayaushe za ka ji yadda Alhaji Zaura ke yabawa kokarin da wannan gwamnati mai ci ke yi a harkar mulki da yunkurin farfado da darajar Jihar Kano masu albarka. Hakan ce ta sanya a yanzu, yake da muradin ci gaba da gyara fasalin Jihar Kano, domin ya tabbatar Kanawa sun ji dadin harkar mulkinsa, idan Allah Ya tabbatar.

Wannan makalar ba za ta iya daukar muradun A. A. Zaura masu mahimmanci ba, amma manazarta dai sun yi amanna cewar kusan dukkanin ‘yan takarkarun da s**a fito, muradun Zaura sun fi haskawa, kuma sun fi samun karbuwa ga Kanawa ciki da waje.

Abin da ya rage dai shi ne, kamar yadda muka sani Jumma’a ce babbar rana a duk ranaku, ashe Kenan ya zama wajibi mu tsimayi wannan babbar ranar!

Alhamdulillah
02/04/2022

Alhamdulillah

23/03/2022

Har Kwanan Gobe Babban Kudirin His Excellency Abdussalam Abdulkarim A A Zaura, Muradinsa Shine Ya Haskaka Rayuwar Talakkawa da Matasan Kanawa domin yanaso jahar kano tazamo cikin tarihi jahohin da Nan gaba kadan za,ayi Tinkaho dasu, ta zama Abin kwatance ta fuskar cigaba.

Babbar Damuwar A A ZAURA da Bakin cikinsa Shine ganin rayuwar talaka da matasa Acikin yanayi marar dadi

A Kullum Al'umma jahar kano shine kyautata masa zaton cewa zai Samar masu adalci dai-dai gwargwadonsa

Munga Zahiri kuma mun shaida cewa babu wata kujera a hannunsa kuma bai ta6a rike wata kujera ba Amma muna ganin irin Alkhairansa ga Al'umma da Talakawa wanda kullum jiya da Yau sai munji wani Abin Alkhairi da yayi domin shi Alkhairinsa baya karewa, Taimakonsa Zuwa ga 'yayan talakkawa shine yasa darajarsa take kara fitowa da kwarjininsa a fili da idon Am'ummar jahar kano.
His Excellency Abdussalam Abdulkarim A A Zaura mutum ne Wanda yake bakin cikin ganin matasan mu Zaune ba tareda wani aikinyi ba Ko Wata Madogara da Zata Taimaki Rayuwarsu ba.

His Excellency Abdussalam Abdulkarim A A Zaura, jagorane ne Wanda ke bakin cikin ganin talakawa Zaune Acikin yanayin dabai daceba koma Jagorane ne irin Wanda matasan wannan lokaci s**a jima suna nema domin sauya rayuwarsu daga bauta zuwa Yanci. Muna Rokon Allah da ya yiwa A A ZAURA Gwamnan jahar kano.

Tabbas inada kyakykyawan tabbaci akansa, Akan cewa Zai Cigaba da kulawa da matasanmu hannu bi-biyu ba tareda taimakon rayuwar matasanmu da Al'ummar jahar kano gaba daya.

Jin dadin sa shine yaga ya samarwa matasa hanyar da zasu dogara da kafafuwansu domin basu Tallafi Su Dogara da kafafunsu Alhamdullahi inada kwarin Gwewa akan cewa nan gaba kadan bada jimawa ba zaku fara tabbatar da abunda nake fada akansa Allah kabashi nasara Allah kabashi Gwamnan jahar Kano.

✍🏻

zauran dai shine amsa
15/03/2022

zauran dai shine amsa

Da yammacin Jiya, Na Zaura Yayi Kira Ga Matasa Da Ƴan Siyasa Kan Su Daina Siyasar DabaDan kasuwa kuma jigo a jamiyaar AP...
11/03/2022

Da yammacin Jiya, Na Zaura Yayi Kira Ga Matasa Da Ƴan Siyasa Kan Su Daina Siyasar Daba

Dan kasuwa kuma jigo a jamiyaar APC Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura yayi kira akan daina siyasar daba.

Zaura ya bayyana farin cikinsa yadda shugaban jam'iya na jiha, Prince Abdullahi Abbas ya jadda wannan kira.

"Tabbas Kano da tsantsagwaron siyasa aka santa ta aƙida da cigaba, kuma zamu haɓɓaka wannan irin siyasa ta cigaban al'umma cikin ikon Allah."

"Ƙarin Farin cikina shine yadda Jagoran jam'iya Kuma gwamna yaja kunnen kowa akan siyasar daba, Maigirma gwamna mungode, kuma da yaddar Allah bisa jagorancinka zamu kai ga gaci." Inji Zaura

Sannan yayi kira ga abokansa na siyasa da su ƙara haɗa kai wajen saka al'umma gaba don taimakamusu fiye da yadda sukeson kansu, kuma su faɗaɗa yadda suke taimakon wannan gwamnatin domin takai ga gaci.

"Tabbas samun nasarar gwamna Ganduje samun nasarar mu ce baki ɗaya." Inji AA ZauraZaura Yayi Kira Ga Matasa Da Ƴan Siyasa Kan Su Daina Siyasar Daba

Dan kasuwa kuma jigo a jamiyaar APC Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura yayi kira akan daina siyasar daba.

Zaura ya bayyana farin cikinsa yadda shugaban jam'iya na jiha, Prince Abdullahi Abbas ya jadda wannan kira.

"Tabbas Kano da tsantsagwaron siyasa aka santa ta aƙida da cigaba, kuma zamu haɓɓaka wannan irin siyasa ta cigaban al'umma cikin ikon Allah."

"Ƙarin Farin cikina shine yadda Jagoran jam'iya Kuma gwamna yaja kunnen kowa akan siyasar daba, Maigirma gwamna mungode, kuma da yaddar Allah bisa jagorancinka zamu kai ga gaci." Inji Zaura

Sannan yayi kira ga abokansa na siyasa da su ƙara haɗa kai wajen saka al'umma gaba don taimakamusu fiye da yadda sukeson kansu, kuma su faɗaɗa yadda suke taimakon wannan gwamnatin domin takai ga gaci.

"Tabbas samun nasarar gwamna Ganduje samun nasarar mu ce baki ɗaya." Inji AA ZauraHalarci The Vue, Novare Mall, wuse Zone 5, Dake Birnin tarayya Abuja domin Amsa gayyatar Abokina, Jakadan Kasar Palestine a Nijeriya, Elkachach Ahmed wajen liyafar cin Abincin dare na bikin Diyarsa
- Alia.

Ina Adduar ALLAH Madaukakin Sarki ya Basu zaman Lafiya itada Mijinta Ahmad, YA Kuma saka Albarka auren.

Amin

A Fada A Cika Sai Zaura
09/03/2022

A Fada A Cika Sai Zaura

Afada A Cika Sai Zaura
09/03/2022

Afada A Cika Sai Zaura

Zauran Kanawa
09/03/2022

Zauran Kanawa

Alhamdulillah Mudai Mama'ar Kano Sai Godiya. Zauran Kanawa
09/03/2022

Alhamdulillah Mudai Mama'ar Kano Sai Godiya. Zauran Kanawa

Political organisation

Address

Fagge
700

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Juma'ar da Zatai Kyau. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share