Tahir Adamu

Tahir Adamu This page was created purposely for Jigawa state politics.

A heartfelt congratulations on your Second degree Your hard work, dedication, and perseverance have paid off. May this a...
15/08/2025

A heartfelt congratulations on your Second degree Your hard work, dedication, and perseverance have paid off.

May this achievement be a stepping stone to even greater success in your future endeavors. Embrace the next chapter with excitement and courage, knowing you have the potential to make a real difference. Congratulations Amb Muhammad Salisu Seeker ......

01/12/2024
Sarkin waka fa k**ar lamarin sa fa Babu ban banci da na Umar bush
14/08/2024

Sarkin waka fa k**ar lamarin sa fa Babu ban banci da na Umar bush

07/08/2024

"Abin Hannun k**a Za'a iya kwace maka"

(Buhari Daura)

07/05/2024

If you can't post my picture when am struggling for survival, don't try it when I succed................🧏🏻‍♂️🧏🏻‍♂️😎😎😎😎😎

Alhamdulillah bi'ni'imatil Islam.Allah ya karawa Annabin Muhammad S.W.A.......................Ubangiji Allah ya albarkac...
06/05/2024

Alhamdulillah bi'ni'imatil Islam.

Allah ya karawa Annabin Muhammad S.W.A.......................

Ubangiji Allah ya albarkaci Rayuwar mu, abin da muke na badaidai ba allah ya bamu ikon gyarawa.......

Allah ya hadamu da masu kaunar mu...............................................

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZA TA SAMAR DA TARAKTOCIN NOMA 300.A matsayin wani ɓangare na alfanun tafiyar Gwamna Mallam Umar ...
02/05/2024

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZA TA SAMAR DA TARAKTOCIN NOMA 300.

A matsayin wani ɓangare na alfanun tafiyar Gwamna Mallam Umar Namadi zuwa ƙasar Amurka, a yanzu haka Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin guiwa da wasu manyan kamfanoni da s**a yi fice a fannin dabarun bincike da samar da kayan aikin gona na zamani domin bunƙasa harkar noma a wannan jiha.

An ƙulla wannan yarjejeniyar haɗin guiwa ne a wani zaman tattaunawa da aka yi a birnin Washington DC tsakanin tawagar ƙwararru daga Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Namadi da kuma wakilan shugabannin kamfanonin John Deere da Tata International.

Tattaunawar da ta gudana tsakanin ɓangarorin biyu ta ta’allaƙa ne kan yadda za a samar da kuma bunƙasa dabarun noma tare da shigar da matasa cikin harkar noma domin ganin an ɗaga matsayi da inganta rayuwar al’ummar jihar Jigawa ta hanyar noma.

Daga cikin kyawawan sak**akon da wannan tattaunawa ta haifar shine ƙuduri na haɗin guiwa da aka zartas na samar da wani shiri da a cikinsa za a sayo tantan ɗin noma guda 300 daga kamfanin ƙera taraktocin noma na Deere, wanda ba da daɗewa ba za a kawo su jihar Jigawa don cigaba da inganta harkar noma a jihar. Wannan zai taimaka matuƙa wajen bunƙasar samun amfanin gona mai kyau da inganci a tsakanin ƙananan manoma na wannan jiha.

A ƙarƙashin wannan shiri ana sa ran za a horas da matasa sama da 1,200 kan harkar kasuwancin sayarwa da ba da hayar kayan aikin gona da kuma sarrafawa tare da gyaran taraktoci da sauran na’urorin aikin da za a samar. Babbar manufar wannan shiri ita ce jawo matasa su shiga cikin harkar noma, wanda a yau ita ce hanyar samar da isasshen abinci da bunƙasar tattalin arziki a jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.

Wannan kuwa wani ɓangare na manufofin da Gwamna Mallam Umar Namadi ya ƙudurci aiwatarwa don inganta fannin noma da sauran fannonin rayuwa a Jigawa da ya zayyana a cikin ƙudurori 12 na gwamnatinsa.

Da yake magana kan ƙulla wannan haɗin guiwa, Gwamna Namadi ya ƙara jaddada muhimmancin yin amfani da dabaru da kayan aikin gona na zamani tare da jawo matasa cikin harkar domin ta hakan ne za a tabbatar an inganta wannan fannin na noma a nan gaba. Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ttallafawa manoma, musamman matasa da a yanzu s**a farar ganin muhimmancin wannan fanni, ta hanyar samar da kayan aiki da dabarun noma na zamani don cigaban al’umma.

Da wannan haɗin guiwa da aka ƙulla da kamfanin John Deere, wanda fitaccen kamfani ne a duniya kan harkar noma ta zamani, da kuma takwaran kamfanin wato Tata International, jihar Jigawa ta k**a hanyar kai wa tudun-mun-tsira ta fuskar noma na zamani da zai ɗaga matsayin rayuwar al’ummarta tare da bunƙasa tattalin arzikinsu.

-Government House Media Office
02/05/2024

Address

Dutse

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tahir Adamu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share