14/03/2024
ƳAN JIGAWA: "IDAN SUKACE DAKU ƳAN ƘAUYE"
Kada wannan Ya ɓata muku rai, itace kalmar da Haryanzu Wasu suke kallon ƴan jihar Jigawa da ita, kokuma ake jifansu da ita, abin mamaki maimakon ƴan jihar Jigawa suyi alfahari da ita, wasu ma wai wannan kalmar ɓata musu rai take, kunsan meyasa suke kiranku da ƴan ƙauye:
•Saboda Har yanzu a jihar Jigawa ana jin kunyar aikata manyan laifuka da addinin Músluñci ya hana, wanda su suke kallonsu amatsayin wayewa.
•Saboda Haryanzu matan jihar Jigawa suna saka manyan hijabi, maimakon subar jikinsu a fili, wannan itace rashin wayewa a wajensu.
•Saboda ƴan siyasar jihar Jigawa adawar siyasa batasa suna zazzafar Gaba ba, kokuma jifan junansu da munanan kalamai ba, sannan siyasa bata Hanasu ziyara, kokuma jaje Alokacin da wani iftila'i Yasamu wani daga cikinsu ba.
•Saboda ƴan jihar Jigawa sunyi riƙo da kyawawan ɗabi'un addinin Muslunci wanda wasu daga cikin wayewar wannan zamani saikayi hannun riga da wasu daga cikin waɗannan kyawawan ɗabi'u.
•Saboda har yanzu a Jigawa idan kikayi shigar banza bazata sa a ƙaunace kiba, sannan idan kayi wani Hali wanda yasaɓawa Addiñi bazaisa mutane su ƙaunace ka.
•Waɗannan kyawawan ɗabi'un da akeso ƴan Jigawa subari, sune rashin wayewar, wanda ga duk mai hankali kuma wannan abin alfahari ne.
Amma idan Ba Haka ba, Tayaya?
•Jihar da take da filin sauƙar jirgi mafi kyau na huɗu a Afrika zaka kirata da ƙauye?
•Jiha ta huɗu mafi zaman lafiya, zaka kira mutanen cikinta ƴan ƙauye?
•Jiha ta uku mafi fitattun ƴan siyasa a Najeriya zakace bata waye ba?
•Jihar datake da sakatariya ta biyu mafi kyau a Nijeriya?
•Gidan rediyo mafi kyau A Najeriya?
•Sarakuna masu ilimi da haɗin kai, masarautu masu tarihi da kyawawan al'adu, wajen tarihi masu Kyan gani da abubuwan al'ajabi.
Badan niɗan Jigawa bane, badon nafison Jigawa Ba, Yaa Allah! Allah kada kasa nayi wayewar da zata Rabani da kyawawan ɗabi'u masu kyau na Jihar Jigawa.
Allah Yaƙarawa Jiharmu ALBARKA.
Ina alfaharin kasancewa ɗan Jihar Jigawa.