24/09/2016
BUHARI YA FASA KWAI - Karanta ka Raba a
shafinka
Dalilin da yasa Najeriya ta shiga cikin Matsalolin
Tabarbarewar Tattalin Arziki da Talauci -
Muhammadu BUHARI
------------------------
Shugaba Muhammadu Buhari a birnin New York na
kasar Amurka, ya sake yin bayani dalla - dalla kan
dalilan da ya sa Nigeria ta samu kan ta cikin
matsalolin da muke fama da su a yanzu.
Shugaba Buhari yayi bayanin ne a lokacin da ya
karbi bakuncin wasu 'yan Nigeria su 15 da s**a yi
fice tare da kwarewa a wuraren da suke aiki a
kasar ta Amurka, wadanda Babbar Mai Bawa
Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan
Harkokin Kasashen Waje, Mrs. Abike
Dabiri-Erewa ta jagoranta s**a gana da Shugaban
Kasar.
Ganawar ta bawa Shugaba Buhari damar yi musu
bayanin dalla-dalla kan dalilan da ya sa 'yan
Nigeria da kasar ke cikin wahalhalu a yanzun, sai
dai ya basu
tabbacin cewa idan dukkan 'yan Nigeria zasu bada
gudunmawarsu ciki harda mazauna kasashen waje,
Kasar za sake daidaituwa har ma a koma fiye da
yadda
ake a baya cikin lokaci ba mai tsawo ba.
Ga bayanin na Shugaba Buhari wanda ya ratsa
zukatan duk wadanda suke wurin ganawar...
"Na yi matukar farin cikin wannan ganawa da ku,
dukinda ka je a fadin duniya, za ka samun 'yan
Nigeria na
kwarai kuma hazikai da s**a yi fice ta fannoni
daban -daban. Kuma ba suna amfanar kasar da
suke zaune ne kadai ba, mafi yawan lokuta suna
taimakawa Nigeria musamman a bangaren tattalin
arziki.
"Mun shiga matsalolin da muke ciki a yanzu
saboda ba mu yi tanadi domin lokaci makamancin
wannan ba. A misali, daga shekarar 1999 zuwa
2015, a lokacin da muke iya samar da danyen mai
ganga milyan biyu da rabi a kullum kuma farashin
danyen man ana sayar da
shi fiye da dalar Amurka $100, ba mu yi tadani ba,
kuma ba mu samar da ayyukan da zasu ciyar da
kasar nan gaba ba. Cikin kankanin lokaci a yayin
da muka zo a 2015, farashi danyen mai ya fadi
zuwa kasa da dalar Amurka $30.
"Na tambaya, ina tanade - tanaden da muka yi
domin irin wannan lokaci? Sai aka ce Babu komai,
ba mu yi tanadin komai ba. Na sake tambayar ina
hanyoyin jiragen kasa da tituna da zasu saukaka
mana rayuwa a irin wannan lokaci? Wadanan ma
babu. Na sake
tambaya, me da me muka yi da biliyoyin dalolin da
muka tara cikin wadannan shekaru? Sai s**a ce
wai
sun sayo abinci. Abinci na biliyoyin daloli? Ban
yarda da su ba kuma ba zan taba yarda ba.
"A mafi yawan yankunan Nigeria, muna cin abin da
muka noma ne. Mutanen Kudu suna cin gari ne,
wadanda suke Arewa suna cin gero ne, wanda su
s**a
noma shi, kuma wannan abincin da suke nomawa
ya kai akalla kaso 60% na abin da muke ci.
Saboda haka, ina biliyoyin dalolin s**a tafi? Mun yi
wa kan mu
matukar barna, mun ki ciyar da kasar mu gaba a
lokacin da muke da makudan kudade.
"Idan za mu yi maganar jami'an tsaron mu ne, sun
samu daraja, ana girmama su, saboda kokarin
samar da zaman lafiya da s**a yi a kasashen
kamar su
Burma, Zaire, Sudan, Liberia, Sierra-Leone, kawai
cikin kankanin kokaci wadannan jami'an tsaro sai
s**a kasa kawo kananan hukumomi 14 daga cikin
774 da muke da su daga hannun 'yan Boko
Haram. 'Yan ta'adda sun gagare su, har sai lokacin
da muka zo, muka hargitsa su, muka nakasa su,
muka rage musu karfi tare da kwato duk wuraren
da suke hannun su.
"Kafin mu zo, Boko Haram suna yin abin da suke
so, suna kashe mutanen da basu ji ba, basu gani
ba a masallatai, majami'u, makarantu, kasuwanni
da
tasoshin motoci da sauran su. Kuma suna kiran
Allahu Akbar, kuma idan har da gaske sun san
Allah ba zasu taba yin irin wadannan ta'addanci
ba. Musulunci ko kowane addini da na sani ba,
bai yarda da ta'addanci ba. Amma sun kashe
dubban mutane da sunan addini.
Yanzu mun yi maganin wannan ta'addancin.
"Haka kuma wadanda s**a sace dukiyar Nigeria ba
sa cikin farin ciki, sun dauki tsageru a yankin Niger
Delta, suna yi mana zagon kasa ta hanyar farfasa
hanyoyin mai. Muna yin asarar miliyoyin gangar
danyen mai a kullum, a lokacin da duk dala dayan
da muka samu tana da amfani. Kuma abin haushi
ne a ce
jihohi 27 daga cikin 36 da muke da su a Nigeria
ba sa iya biya albashin ma'aikata.
"Nayi addu'a sosai, Allah ya bani Shugaban Kasa,
na tsaya a 2003, 2007, 2011 da kuma 2015, Allah
ya amsa addu'a ta. Ku kalli abin da nazo na samu
a kasa.
Amma ba zan yi nadama ko korafi ba, tunda na
roki Allah ne kuma ya bani. A aikin Soja, na samu
karin matsayi daga Laftana zuwa Manjo-Janar. Na
rike matsayin Gwamna a 1975 a jihar da a yanzu
ta haifar da jihohi 6. An daure ni na tsawon
shekaru 3, na kuma rike mukamin Shugaban PTF,
wanda a lokacin
take da naira bilyan 53 a asusun ta.
"Allah ya albarka ce ni sosai, so ba zan taba nuna
damuwa ta ko korafi ba. A duk sanda wani ya
zalunci ne, ina rokon Allah ne ya bani ikon yafewa.
Allah ya
bani abubuwa masu tarun yawa. "Sannan ku tuna,
bayan shekaru 16, Jam'iyya guda na mulki, ba
jam'iyyar da za ta zo ta samu abubuwa cikin sauki,
haka halin Dan Adam yake. Muna bukatar
nagartattun hannaye su rike Nigeria, kuma zamu yi
amfani da wadanda suke da su a yanzu. Za su na
gayyace ku ku dawo gida idan lokacin yayi,
saboda
haka ina so ku zama cikin shiri."
Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala
wannan jawabi na sa mai matukar ratsa jiki,
dukkan wadannan s**a halarci zaman sun tabbatar
da cewa a shirye suke don bada gudunmawarsu
don ganin kasar su ta gado ta ci gaba ta kowane
fanni.
— Bashir Ahmad,
Maitaimakawa Shugaba Buhari
Kan Sababbin Kafafen Yada Labarai
(Social Media).