Future Light For Dmd Yobe State

Call Directions Contact the organization

Future Light For Dmd Yobe State Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Future Light For Dmd Yobe State, Political organisation, Abbari ward damaturu gjuba Road, Damaturu.

🌟 Official Page of Future Light for DMD – Yobe State Chapter. 🤝 Mobilizing support, promoting leadership, civic engagement, and advancing DMD's vision across Yobe State. 🇳🇬✨ Together for progress, unity, hope, and a brighter future for all.⭐✨

HotunaDaga Wajen Launching na Jibwis Yobe State NHQ Jos A Garin Damaturu Wanda Dan Takarar Gwamnan Jahar Yobe karkashin ...
03/10/2026

Hotuna

Daga Wajen Launching na Jibwis Yobe State NHQ Jos A Garin Damaturu

Wanda Dan Takarar Gwamnan Jahar Yobe karkashin jam’iyar YPP HE. Dr Muhammad Dawud yasamu Halarta.

Saboda Mahimmancin Taron yasa Yabar Duk abun da yake A Garin Fika domin halartan Launching din.

Cikin Tawagar DMD Akwai DG campaign tare da State Party Chairman na YPP tare da sauran Tawaga.

Allah yasa albarka a wannan taro

DMD MEDIA TEAM✍🏼

HOTUNA*CIGABA DA YAKIN NEMAN ZABE A FIKA LGA - RANA TA BIYU GA WATAN OKTOBA, 2026*Tawagar Yakin Neman Zaben YPP ta Jihar...
03/10/2026

HOTUNA

*CIGABA DA YAKIN NEMAN ZABE A FIKA LGA - RANA TA BIYU GA WATAN OKTOBA, 2026*

Tawagar Yakin Neman Zaben YPP ta Jihar Yobe tana Cigaba da yakin neman zabe a Karamar Hukumar Fika.

A cigaba da ziyarar ranar farko, tawagar ta ziyarci garuruwa da kauyuka kamar haka: *Fika Ta yamma, Gadaka, maidowa, Goge.

Sannan Rana ta Biyu kuma Tashiga Garin Babaji, Garin Gamji, Amzai, Ngalda, Dumbulwa, Tadangara da kuma kauye mai wuyar shiga inda mota ma sai anyi da gaske wato garin Zamba.*

Duk da tsawon hanya da wuyar shiga garin Zamba, tawagar Yakin neman Zaben tashiga domin isa kowane lungu da sako, domin jam'iyyar YPP ta tabbatar musu cewa babu wata al'umma da za'a bari a baya.

A duk garuruwan da muka ziyarta a yau, dubban magoya bayan jam'iyya na kwarai da masu biyayya ne s**a tarbe mu. Tarbar ta kasance mai girma da ban sha'awa. Mata, matasa, dattawa da shugabannin al'umma duk sun fito domin tarbar jam'iyyar YPP.

Mutanen Babaji, Garin Gamji, Amzai, Ngalda, Dumbulwa, Tadangara da Zamba sun nuna karara cewa sun gaji da tsohon tsari kuma a shirye suke domin sabuwar Yobe da YPP ke wakilta - Yobe ta Ci Gaba, Hadin Kai da hidima Ga Jama'a.

Muna godiya ga al'ummar wadannan yankuna bisa hakuri, kauna da goyon baya mara misaltuwa.

Yakin neman zabe a Fika LGA na ci gaba. Fika ta ce sai YPP!

DMD MEDIA TEAM✍🏼

02/10/2026

DMD AKE MAGANA 🔥🔥🔥

Future Light For Dmd Yobe State

02/10/2026

SIGMA MODEL ✊✊✊

YOBE SAI MALAM



02/10/2026

Namu Ba Irin Nasu Bane 🫡

DAMATURU CENTRAL DA IKON ALLAH 🔥Future Light For Dmd Yobe State
02/10/2026

DAMATURU CENTRAL DA IKON ALLAH 🔥

Future Light For Dmd Yobe State

Kunga Matasan Nan, Na Bayan Dakta?To babu wanda yace suzo za'a basu alawus ko kudin abinci tsantsar kishin Jihar ne kawa...
01/10/2026

Kunga Matasan Nan, Na Bayan Dakta?

To babu wanda yace suzo za'a basu alawus ko kudin abinci tsantsar kishin Jihar ne kawai da kuma gane halin da jihar nan ta tsunduma ciki.

Mune fa jiha ta shida a tsananin talauci da kuncin rayuwa a duk fadin nijeriya.

Amman zamu hau fly over mu yanki tumu ko masara.

Mu tashi muyi chanji, zai yiwu matukar muka jajirce kuma mukayi tawassali da sunan Allah.

Wannan ba tafiya bace ta jam'iyyar YPP ko kuma Dakta, tafiyace ta ceto Jihar Yobe, da ceto matasan jihar Yobe.

Nuradistin

🇳🇬 1st October, 2026 | Tafiyar 2027 ta fara!A yau, 1st October 2026, Dr. Muhammad Dawud ya fara wannan sabuwar tafiya ta...
01/10/2026

🇳🇬 1st October, 2026 | Tafiyar 2027 ta fara!

A yau, 1st October 2026, Dr. Muhammad Dawud ya fara wannan sabuwar tafiya ta neman shugabancin Jihar Yobe da neman albarkar iyaye, ta hanyar ziyartar mahallin iyayensa.

Wannan ziyara ta kasance farkon matakin Ward-to-Ward Campaign da Jam’iyyar YPP ta tsara domin tunkarar babban zaben 2027.

Jam’iyyar YPP ta dauki alwashin zagaya wards 178 na Jihar Yobe, domin kai sakon sauyi, ci gaba da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar jihar. Za a fara wannan gagarumin yakin neman zabe daga Zone C, Insha Allah.

Tambaya gare ku:
👉 Mene ne ra’ayinku game da takarar Dr. Muhammad Dawud a matsayin Gwamnan Jihar Yobe a 2027?

Ku bayyana ra’ayinku a cikin comments. 👇

Future Light For Dmd Yobe State

Address

Abbari Ward Damaturu Gjuba Road
Damaturu
001

Telephone

+2348130148106

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Future Light For Dmd Yobe State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Future Light For Dmd Yobe State:

Shortcuts

Share