Jigawa State Social Media Crew Birniwa L.G Chapter

Jigawa State Social Media Crew Birniwa L.G Chapter JIGAWA ABAR ALFAHARINMU

Maigirma Mataimakin Shugaban Kungiyar YanKasuwar Jihar Jigawa(Deputy Vice PresidentJigawa State Commerce Chamber)Muhamma...
03/06/2016

Maigirma Mataimakin Shugaban Kungiyar Yan
Kasuwar Jihar Jigawa(Deputy Vice President
Jigawa State Commerce Chamber)Muhammad
Mukhtar Birniwa A Gidan Gwamnatin Jihar Niger
(Minna),Bayan Kammala Zaman Meeting(Zonal
Meeting),Maigirma Gwamnan Jihar Niger Alhaji
Abubakar Sani Bello Ya Shirya Musu Liyafar Chin
Abinchi Dashi(Dinner)
Sir Allah Yasa Wannan Tafiya Taka Ta Zama Silar
Karuwar daukakar Darajar Ka.
3/6/2016
BK BIRNIWA

27/02/2016

Y'ay'an Gwamna

20/01/2016

A Social Media Ana Saka Tarbiyya Kuma Ana
Koyar Da Tarbiyya.
Dan Uwa Karkayi Tunanin Ka Bude Whatsapp,
Facebbok Koh Twitter Kayi Ta Rubuta Abunda
Kaga Dama dan Ama Comment koh Like, Toh
Wallahi Ta Wannan Kafa Al umma Zasu Iya
Gane Tarbiyya, Hankali Da Kuma Tunaninka.
Yin Rubutu Ayima Comment Bashi Yake Nuna
Kwarewarka A Harkar ba,Yin Rubutu Mai
Ma'Ana Shine Abu Mai Kyau, Sabo Koh Babu
Wadda Yayi Comment Kasan Abin kirki Ka
Rubuta Kuma Al umma Ta Shaida Hakan, Amma
Inka Sake Ka Rubuta Abun Tsiya Kasan Abun
da Zai Faru.,
Raqib/Atid Ba Wai Furuci Kadai Suke
Rubutawa Ba, Ayyuka Suke Rubutawa Mai Kyau
koh Maras Kyau, Wannan Abu Da Muke Yana
Cikin Ayyuka Da Muke Aikatawa
Gyara Kayanka......
BK BIRNIWA Jscmc Coordinator Birniwa Chapter.

16/01/2016

Allah Ya Kara Mana Lafiya Da Zama Lafiya A Kasar Ta Jigawa Da Najeriya Baki Daya,

10/01/2016

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ____ A Karkashin Jagorancin Alhaji Muhammad
Badaru Abubakar Maitamiz Babura Tanaci Gaba Da Shirye - Shiryenta Na
Alkhairai Ga Al'Ummar Jihar Jigawa Don Samun Jindadin Al'Ummar Jihar Da
Walwalar Su Tare Da Kwanciyar Hankalin Su .
Allah Yakara Yiwa Gwamnatinka Jagoranci Nagari Sardaunan Ringim .

07/01/2016

ASLM USMAN AL'AMEEN BIRNIWA YAKE MUKU BARKA DA ASBAHI DAFATAN KUN TASHI LAFIYA FRIENDS ALKHAIRIN DA YAKE CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA SADAMU DA ITA SHARRIN DAKE CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA KAREMU DA KARIYARSA...

05/01/2016

° Ginin Dam A Kananan Hukumomin Birniwa, Guri Da
Kirikasamma____________________=============________________________________====================

• Gwamnatin tarayya za ta gina dam
guda uku a kananan hukumomin
Birniwa da Kirikasamma da kuma
Guri a kasafin kudin 2016.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar
kananan hukumomin uku, Dr
Abubakar Hassan Fulata ya sanar
da haka a lokacin da ya ziyarci
mazabun Batu da Diginsa da Guwa
da Matamu da kuma Machinamari duk a Birniwa.

• Ya ce idan aka kammala ayyukan
dam din, zai amfani manoma dubu
uku a kananan hukumomin guda
uku tare da samar da ayyukan yi
daban-daban.

• Dr Abubakar Fulata ya ba da
gudummawar naira miliyan daya
da dubu dari biyar domin tallafawa
harkokin ruwa da kiwon lafiya da
kuma dalibai.

• Ya dau alkawarin yin duk abinda
ya kamata domin tabbatar da sare
ciyawar kacalla domin amfanin
manoman da ke bakin kogi.

• A nasu jawaban, masu magana da
yawun al’ummomin, Malam
Muhammad Ibrahim da kuma Mai
Mamman sun yabawa dan
majalisar bisa kokarinsa na kawo
ayyukan ci gaba ga al’ummar
mazabarsa.

GININ DAM A KANANAN HUKUMOMIN BIRNIWA, GURI DA KIRIKASAMMA.Gwamnatin tarayya za ta gina damguda uku a kananan hukumominB...
01/01/2016

GININ DAM A KANANAN HUKUMOMIN BIRNIWA, GURI DA KIRIKASAMMA.
Gwamnatin tarayya za ta gina dam
guda uku a kananan hukumomin
BIrninwa da Kirikasamma da kuma
Guri a kasafin kudin 2016.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar
kananan hukumomin uku, Dr
Abubakar Hassan Fulata ya sanar
da haka a lokacin da ya ziyarci
mazabun Batu da Diginsa da Guwa
da Matamu da kuma Machilari na
k/h Birniwa.
Ya ce idan aka kammala ayyukan
dam din, zai amfani manoma dubu
uku a kananan hukumomin guda
uku tare da samar da ayyukan yi
daban-daban.
Dr Abubakar Fulata ya ba da
gudummawar naira miliyan daya
da dubu dari biyar domin tallafawa
harkokin ruwa da kiwon lafiya da
kuma dalibai.
Ya dau alkawarin yin duk abinda
ya kamata domin tabbatar da sare
ciyawar kacalla domin amfanin
manoman da ke bakin kogi.
A nasu jawaban, masu magana da
yawun al’ummomin, Malam
Muhammad Ibrahim da kuma Mai
Mamman sun yabawa dan
majalisar bisa kokarinsa na kawo
ayyukan ci gaba ga al’ummar
mazabarsa.
BK BIRNIWA

01/01/2016

NEW YEAR MESSAGE
FROM GOVERNOR
MUHAMMAD BADARU
ABUBAKAR (MON, MNI)

The Executive Governor
of Jigawa State Alhaji
Muhammad Badaru
Abubakar (MON, mni)
has urged the people of
the state and Nigerians
in general to use the
opportunity of the 2016
New Year celebration to
rededicate themselves
and all their useful
energies to the urgent
task of rebuilding the
nation's economy.
While felicitating with
the people of the state
and other Nigerians on
the New Year
celebration, Governor
Badaru noted that
Nigerians, along with all
those in authority,
needed a deep sober
reflection as they
embrace 2016 in order
to get all hands on deck
in tackling the myriads
of socio-economic
problems that
confronted the people in
2015.
Governor Badaru also
recalled the
unprecedented massive
support he garnered at
the polls during the
governorship election in
the state and the
equally unrivaled hands
of fellowship the people
have continued to
extend to his
administration in spite
of present economic
crunch and thanked the
good people of Jigawa
state for their support
and understanding.
He assured the people
of the state that his
administration' s
actions would always
be guided by the fear of
Allah (SWT) while
working hard with the
meager resources
available to it to provide
the gains of democracy
to the people.
In his words, Governor
Badaru said "I would like
to wish the indigenes of
Jigawa State and the
Citizens of Nigeria a
very safe, happy and
healthy new year. 2015
was a year of great
Change in Jigawa State
and Nigeria at large, but
the hard work and
challenges are far from
over. My hope for this
new year is that we
grow and work
together to make this
beautiful state a better
place to live, work and
invest.”
Lastly, Governor
Muhammad Badaru
prayed for everlasting
peace in the State and
the country at large.
***************
***************
***************
***************
SAKON SABUWAR
SHEKARA DAGA
MAIGIRMA GWAMNA
MUHAMMAD BADARU
ABUBAKAR (MON, MNI)
Maigirma Gwamnan
Jihar Jigawa Alhaji
Muhammad Badaru
Abubakar (MON, mni)
yayi kira ga al'umar Jihar
Jigawa da ma Najeriya
baki daya suyi amfani
da damar murnar
shigowa sabuwar
shekara domin kara
jajircewa da bada
gudunmawar su wajen
gina kasar Najeriya.
A yayin da yake taya
al'umar Jihar da ma
sauran 'yan Najeriya
murnar Sabuwar
Shekarar 2016, Gwamna
Badaru yace dukkanin
'yan Najeriya da masu
mulki suna bukatar suyi
tunani mai zurfi da
neman hadin kan al'uma
domin warware irin
matslalolin da s**a
addabi kasar nan a
Shekarar 2015.
Gwamna Badaru ya
kuma waiwaya domin
jinjinawa da irin goyon
baya da ya samu a
yayin Babban Zabe na
Gwamnoni da kuma irin
hadin kai da al'umar
Jihar Jigawa ke bashi da
kuma fahimtar salon
jagorancin sa, duk da
sanin irin halin da kasar
ke ciki na koma bayan
tattalin arziki, anan ne
ya gode da kuma yaba
musu saboda irin hadin
kai da suke bashi da
kuma fahimtar da suke
dashi.
Ya tabbatarwa al'umar
Jihar cewa duk abinda
zai yi, zai yi shi da
tsoron Allah (SWT),
kuma zai yi aiki tukuru
da dan abinda Jihar take
dashi domin ayyukan
alheri ga jama'a domin
sharbar romon
dimokradiyya.
A cewarsa, "Ina yiwa
al'umar Jihar Jigawa da
daukacin 'yan Najeriya
murnar shigowa
Sabuwar Shekarar 2016.
Shekarar 2015, shekara
ne da aka samu canji a
Jigawa da Najeriya,
amma duk da haka
akwai kalubale a
gabanmu. Fatana shine
wannan shekara na
2016, ya zamo shekarar
da zamu samu cigaba
da aiki da juna, domin
samun Jihar da zamu yi
alfahari da ita domin
zama, aiki da
kasuwanci.
A karshe, Gwamnan
yayi addu'ar samun
zaman lafiya mai
dorewa a Jihar da Kasar
baki daya.
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the
Executive Governor of
Jigawa State on New
Media
(Mataimaki na
Musamman ga Maigirma
Gwamnan Jihar Jigawa a
Sabbin Kafafen
Sadarwa)
01/01/2016

GWAMNA BADARU YA UMURCI BIYAN KUDINTALLAFIN KARATU GA DALIBAN JIHARJIGAWAMaigirma Gwamnan Jihar Jigawa AlhajiMuhammad Ba...
22/12/2015

GWAMNA BADARU YA UMURCI BIYAN KUDIN
TALLAFIN KARATU GA DALIBAN JIHAR
JIGAWA
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji
Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) ya
amince tare da bada umarnin biyan Kudin
Tallafin Karatu na zangon karatu na 2013/14
ga Daliban Jihar dake Karatu a manyan
makarantun kasar nan. Daliban da zasu samu
wannan tallafi sune wadanda aka tantance na
zangon karatu shekarar 2013/14 su 8440 (Maza
6894 da Mata 1564).
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da
Kwamishiniyar Ilimi, Kimiyya da Fasaha na
Jihar Jigawa Hajiya Rabi Ishaq ta fitar.
Sanarwar tace wannan umurni na daga cikon
alkawuran da Maigirma Gwamna ya dauka ne
ga 'yan Jihar Jigawa na tallafawa da bunkasa
harkar Ilimi a Jihar.
Idan za a iya tunawa a Kwanakin baya ne
Gwannatin ta bada umarnin biyan Daliban Jihar
dake karatu a kasashen ketare tallafinsu na
karatu.
Haka sanarwar ta kara jaddada kudirin
gwamnatin na biyan hakkokin daliban da sauran
bukatunsu akan lokaci.
Kwamishiniyar tace Maigirma Gwamnan ya
umurci ma'aikatan hukumar bada Tallafin su
gudanar da aikin nasu ta hanyar da ya dace,
sannan yayi kira ga Daliban su mayar da
hankalinsu wajen karatunsu domin ta hakan ne
kadai jarin da gwamnatin ta zuba a kansu ba
zai tafi a banza ba.
Shugaban Hukumar Bada Tallafin na Jihar
Jigawa Alhaji Babandi Abubakar Gumel, ya
bayyana cewa Gwamnati mai ci a yanzu
karkashin jagorancin Gwamna Badaru Abubakar
ta gaji bashin kudaden Tallafin Dalibai da ke
karatu a manyan makarantun ciki da wajen
kasar nan har na yawan Naira Biliyan Daya, da
Miliyan Dari Biyu da Tamanin da Biyar, da
Dubu Dari da Shida, da Dari Hudu da Casa'in
da Takwas (N1, 285, 106, 498.25), inda
Maigirma Gwamnan cikin karimcinsa da
dattakonsa ya biya kudin Tallafin har na Naira
Miliyan Dari Bakwai da Takwas, da Dubu Dari
Shida da Hudu da Dari Takwas da Ashirin da
Bakwai da Kobo Sittin da Biyar cikin
basuss**an da aka barwa Hukumar, wanda
kusan kashin 70 ne cikin 100.
^
BK BIRNIWA

BIRNIWAMasha Allah.^Jam iyyar PDP Sai Qara Rikicewa Take Ta koina, A Jiya Juma'a Shugaban Karamar HukumarBirniwa (Alh Ja...
19/12/2015

BIRNIWA
Masha Allah.
^
Jam iyyar PDP Sai Qara Rikicewa Take Ta ko
ina, A Jiya Juma'a Shugaban Karamar Hukumar
Birniwa (Alh Jaji Muhammad Dole) Tare da
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birniwa
lokacin Saminu (Alh Ahmad muhammad
Karanka) S**a Chanja Sheka Daga PDP Zuwa
APC..
^
Sun Bayyana Ficewar Tasune Da Cewar Zasu
Taho Jam iyyar APC Ne Dan Su Taya Maigirma
Gwamnan Jihar Jigawa (Badaru Abubakar Mon,
mni) Ayyukan Alkhairi Da s**a Gani Yanayi A
jihar.
^
BK BIRNIWA

Address

Birniwa
JSSMCBC

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jigawa State Social Media Crew Birniwa L.G Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share