07/05/2026
Gwamnatin Kebbi ta goyi bayan aikin tantance bayanai na hukumar
Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da shirinta na bai wa Hukumar Rarraba Kudin Shiga da Kasafin Kudi ta Tarayya (RMAFC) cikakken hadin kai domin gudanar da aikin tantance bayanai kan rabon kudaden shiga a fadin kasa.
Mataimakin Gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida, ne ya bayyana haka yayin karbar tawagar hukumar da kwamitin FAAC a Birnin Kebbi.
Ya ce gwamnatin jiha ta fahimci muhimmancin sahihan bayanai wajen tabbatar da adalci wajen rabon kudaden shiga ga jihohi da kananan hukumomi.
Tafida ya kara da cewa Gwamna Nasir Idris ya umarci Ma’aikatar Kudi, Hukumar Tattara Haraji, shugabannin kananan hukumomi da sauran ma’aikatu da su bai wa tawagar cikakken hadin kai.
Shugaban tawagar, Farfesa Olusegun Adekunle Wright, ya ce aikin na da muhimmanci wajen sabunta bayanan da ake amfani da su wajen rabon kudaden shiga domin dacewa da sauye-sauyen tattalin arziki da ci gaba.
Itama Kwamishiniyar RMAFC, Hajiya Rakiya Tanko Ayuba, ta yabawa gwamnatin Kebbi bisa goyon bayan da take bai wa hukumar tare da neman a ware mata fili domin gina ofishin hukumar a jihar.