16/10/2022
*Shugabanci*
yana nufin shugabantar al'ummah ko kuma jagorancin al’umma. Haka kuma shugaba shi ke tabbatar da cewa ana bin doka da oda kamar yadda aka tsara. Kuma shi ne mai bayar da umarni wajen tafiyar da ayyukkan yau da kullum wadanda mabiyansa za su yi. Shi ne ke wucewa gaba al’ummarsa na biye da shi.
*Wasu Abubuwan da suke wajibi ne ga shugaba*
*Ilimi*
Dole ne shugaba na-gari ya zama yana da ilimin da zai gudanar da aikinsa, hakan zai sa mabiya bayan sa su girmama shi tare da amincewa da duk wani hukunci da zai yanke.
*Gaskiya da tsare mutuncin kai*
Dole ne shugaba ya zama mai gaskiya, ya kamata na kasa da shi su iya bada shaidar Shuganbansu a matsayin mai gaskiya, ba wai game da aiki kawai ba har ma akan irin halayen sa.
*Jajircewa*
Dole ne shugaba na gari ya zamo mai jajircewa a kowane irin yanayi, kada ya karaya har sai ya kai ga samun nasara.
*Mutuntawa da TAUSAYI*
daya daga cikin alamun shugaba na gari shi ne mutunta na qasa da shi.
*Adalci ga kowa*
adalci wa kowa batare da nuna kabilanci ko fifiko ba ko nuna bangarenci ko alfarma sabida addini ko al`ada.
*Yarda da kai*
Dole ne shugaba nagari ya zama mutumin da ya yarda da kansa wajen fuskantar kowace irin matsala da za ta iya tasowa, duk kuwa irin wahalar da ke tattare da ita da kuma faduwar gaba.
*Mai qirqira*
Ba ya tsayawa jiran wai sai mabiyan sa sun yi abu, sai dai kawai ayi kwatance da shi.
Tarihi ya nuna da cewa GEN. AMINU BANDE shugaba ne mai ILMI, GASKIYA, AMANA, MUTUNCI, TAUSAYI, JAJIRCEWA, shugabane MAI QIRQIRA da ya YARDA da KANSHI.
muna kira ga al’ummar Jahar kebbi da mu fito mu zabi *AMINU BANDE* Domin samun cigaban JAHAR KEBBI.
Fodio Gwandu