Mujaddadi TV

Mujaddadi TV WANNAN GIDAN TV AN KIRKIROSHI NE DOMIN TALLATA AYYUKAN SANATAN BAUCHI TA KUDU SANATA SHEHU BUBA UMAR

10/05/2026
Alhamdullah,Yanzu yanzu an gama tantance Sanata Shehu Buba Umar a matsayin Dantakarar Gwamnan Jihar Bauchi 2027 a Jamiyy...
09/05/2026

Alhamdullah,
Yanzu yanzu an gama tantance Sanata Shehu Buba Umar a matsayin Dantakarar Gwamnan Jihar Bauchi 2027 a Jamiyyar APC,
Allah tabbatar mana da Nasara cikin sauki.

KARYA NE!!!.Babu Wani shiri na chanja Jamiyya Sannan Sanata Shehu Buba Umar Bai sayi form a Jamiyyar PDP ba .
08/05/2026

KARYA NE!!!.

Babu Wani shiri na chanja Jamiyya Sannan Sanata Shehu Buba Umar Bai sayi form a Jamiyyar PDP ba .

Mai Dakin Sanata Shehu Buba Ta Tallafawa Mata 200 Da Jari a Bauchi.Mai dakin Sanata Shehu Buba, Hajiya Zainab Shehu Buba...
08/05/2026

Mai Dakin Sanata Shehu Buba Ta Tallafawa Mata 200 Da Jari a Bauchi.

Mai dakin Sanata Shehu Buba, Hajiya Zainab Shehu Buba, ta kaddamar da wani shiri na tallafawa mata da jari domin karfafa musu gwiwa wajen dogaro da kai.

A cikin wannan sabon shiri, an tallafawa mata kimanin 200 da jari, wanda ake sa ran zai taimaka musu wajen fara kananan sana’o’i da bunkasa rayuwarsu.

Hajiya Zainab ta bayyana cewa, wannan ba shi ne karo na farko da take gudanar da irin wannan tallafi ba. A baya, ta taba tallafawa mata sama da 1000 masu juna biyu da kayan haihuwa, wanda darajarsa ta kai kusan naira 100,000 ga kowacce mace.

Ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da tallafawa mata a fadin yankin, inda ta yi alkawarin cewa za su ci gaba da aiki tare da su tun daga lokacin yakin neman zabe har zuwa lokacin mulki, idan har aka samu nasara.

Wasu daga cikin matan da s**a amfana da shirin sun nuna jin dadinsu tare da yabawa wannan kokari, suna mai cewa zai taimaka matuka wajen rage radadin talauci da kuma inganta rayuwar iyalansu.

MUJADDADI TV.

Masu Ruwa da Tsaki a Bauchi Sun Amince da Tsarin “Kato Bayan Kato” Gabanin Zaɓen 2027Abuja – Bayan dogon tattaunawa da s...
08/05/2026

Masu Ruwa da Tsaki a Bauchi Sun Amince da Tsarin “Kato Bayan Kato” Gabanin Zaɓen 2027

Abuja – Bayan dogon tattaunawa da shawarwari, masu ruwa da tsaki na Jihar Bauchi sun cimma matsaya tare da amincewa da amfani da tsarin “Kato Bayan Kato” wajen gudanar da zaɓen fidda gwani a kakar zaɓen shekarar 2027.

Taron wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya samu halartar kusan dukkan manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar. Mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi tsarin zaɓe, inda a ƙarshe s**a amince da wannan tsari domin tabbatar da haɗin kai da kuma rage rikice-rikice a cikin jam’iyya.

Bayan cimma yarjejeniya, mahalarta taron sun rubuta matsayar tasu a hukumance, inda nan take s**a miƙa takardar ga Shugaban Ƙasa da kuma uwar jam’iyya domin sanar da su hukuncin da s**a yanke.

Masu sharhi na ganin cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen kawo zaman lafiya da daidaito a harkokin siyasar jihar, musamman
yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.
Ana sa ran cewa wannan tsarin zai taimaka wajen gudanar da zaɓe cikin lumana da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan jam’iyyar a Jihar Bauchi.

ANYI ZAMAN HADIN KAI DA NEMAN MAFITA A APC KUMA AN CIMMA MATSAYA....Masu fada aji a siyasar APC na Jihar Bauchi wanda s*...
08/05/2026

ANYI ZAMAN HADIN KAI DA NEMAN MAFITA A APC KUMA AN CIMMA MATSAYA....

Masu fada aji a siyasar APC na Jihar Bauchi wanda s**a hada da masu ruwa da tsaki Masu rike da kujerun Sanata da Majalisr Tarayya, Tsohon Gwamna, Tsohon Kakakin Majalisr Dokokin Nigeria Hon. Dogara, Shuwagabannin Jamiyyar APC na kananan hukumomi, shuwagabannin Jihar da Sauran fitattaun Mutane sunyi Zama domin Neman mafita wa Jamiyyar APC Kan yadda za'a cire Dan Takarar Gwamnan APC a zaben 2027 mai zuwa inda Dukkan Wanda s**a halarci Zaman sun amince da ayi zaben KATO_BAYAN_KATO (Direct Primaries) domin fidda Dan takara wanda hakan zai kawo hadinkai a Jamiyyar bayan fitar da Dan takarar.

Wannan mataki an daukeshi ne domin Dawo da Martabar Jamiyyar APC a Jihar Bauchi a zaben 2027 Mai zuwa.

Daga karshe ni Auwal Umar Luti ina bada Shawari da a zabi Sanata Shehu Buba Umar donin shine Wanda aka yarda zayyi Adalci kafin da bayan kasancewarsa akan Karagar Mulki Insha Allahu.

07/05/2026

7/05/2026,
KUNGIYAR SBU VANGUARD 4GOV. 2027 SUNKAI ZIYARAR TA'AZIYYA WA COMR. SABO MUHAMMAD

Kungiyar nan rajin ganin Sanata Shehu Buba Umar ya zama Gwamnan Jihar Bauchi karkashin Jagorancin Engr.Ishaq Dabo takai gaisuwar ta'aziyya wa daya Daga cikin 'yan Kungiyar Comr.Sabo Muh'd na rasuwar Kaninsa Wanda yau Yake cika kwana 3 da Rasuwa. Allah masa Rahama.

07/05/2026

MASHA ALLAH 💥

"Sanata Shehu Buba Umar mai wakiltar Bauchi ta Kudu, shine Sanata na biyu cikin jerin sanatoci da s**a fi hidimtawa al’ummar mazaɓarsu, a faɗin Arewacin Najeriya."

- Inji Garus Gololo

07/05/2026

WANNAN GASKIYA NE Hon. KUNDAK.

06/05/2026

BAUCHI STATE YOUTHS POLITICAL ALLIANCE SUN GABATAR DA TARO DOMIN BADA TALLAFI WA MEMBOBIN KUNGIYAR.......

Wata kungiya mai goyon bayan Sanata Shehu Buba Umar sunyi tattaka Zuwa Gidan Sanatan domin Jaddada goyon bayansu (Endorsement) Wanda Sanatan ya Basu kudin Achaba Wanda Yau s**a kudin cikin Nitsuwa........

05/05/2026

Sanata Shehu Buba Umar yayi hira da manema labarai bayan ya mayar da form din takararsa.

Allah yayika Gwamnan Jihar Bauchi 2027.

Address

Bauchi

Telephone

+2348158383858

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujaddadi TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share