10/06/2026
Mai Girma Rt. Hon. Auwal Muhammad Jatau ya karɓi lambar yabo a madadin Mai Girma Sanata Bala Abdulkadir Muhammad
Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Auwal Muhammad Jatau, ya karɓi Lambar Yabo ta Ƙwarewa da Gagarumar Gudunmawa (Award of Excellence and Meritorious Service) a madadin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, CON, Kauran Daular Usmaniyya, daga Ƙungiyar Daliban Jinya da Ungozoma ta Jihar Bauchi (State Association of Student Nurses/Midwives, Bauchi State Chapter).
An bayar da wannan lambar yabo ne domin girmama irin gudunmawar da Gwamnan ya bayar da kuma jajircewarsa wajen bunƙasa harkokin lafiya, ilimin jinya da ungozoma, tare da ƙarfafa matasa a faɗin Jihar Bauchi.
An miƙa lambar yabon ne a yayin wani taro da ƙungiyar ta shirya domin karrama mutane da s**a taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban harkokin jinya da ungozoma da kuma tallafa wa cigaban ɗalibai a wannan fanni a jihar.