23/01/2016
KYAUTAR BUDURCI "1" ....Ra'uf,Rabi'u, da Ridwan Yan uwan juna ne,uwar su daya ubansu ,ra'uf ne babba ,sai rabi'u sai ridwan ,yan asalin jihar misau ne ,sunyi karatun boko da arabi,amma ra'uf da rabi'u sun fi yin xurfi a boko,yayin da ridwan ya maida hankali a gonarsu ta gado ,domin yana gama secondary yayi aure ,ya shachi bangare a gdansu ya xaune da matarsa hauwa ,bayan shekara uku da aurensu su ka haifi 'ANWAR' , a lokacin rabi'u yayi aure da matars ramla ,bayan ya samu aiki a NNPC ,shima ya tare birnin abuja ,shekara biyu da auransu s**a haifi 'ANAS', Rau'f baban boko shi medicine ya karanta ,shine dai auren nasa daga baya baya , bayan kuma shine babba,ya k**alla karatunsa ya samu zama consultant a asibitin AKTH ,ya tamfatsa gdansa a darmanawa ya tare da matarsa yar asalin kuwait' girman kano amma mai suna 'lubna'........zuwa yanxu anwar na da kanne uku adam,basma da bahijja ,yayin da anas yake da kanwa guda daya aisha .......ra'uf,rabi'u ,ridwan dukkansu suna yin zumunchi mai tsafta ......... Duk da kowa garin da yake daman , ra'uf da lubna sai da s**a shekara biyar da aure ALLAH ya azurta su ya mace ,ranar suna aka sa mata suna 'zARINA' ........daga kanta lubna bata qara haihuwa ba,duk wani so da gata sai s**a dorawa tilon yar su zarina.........