13/04/2026
Comrade Sabo Mohammed, masharhanci kan al’amuran yau da kullum a Bauchi, ya bayyana cewa sauya sheƙar siyasa a Najeriya abu ne mai cike da haɗari, yana mai cewa duk wani mataki da ɗan siyasa zai ɗauka dole ne ya yi la’akari da irin wannan kasada.
Ya bayyana haka ne a cikin shirin A Idon Makwarwa na Albarka Radio, inda ya ce, “Siyasa kasada ce; zuwa jam'iyyar APC da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yake yunkurin yi ma kasada ne gare shi da mutanensa, har ma da waɗanda za su karɓe shi, domin ba wanda ya san abin da zai faru a siyasar Najeriya.”
Sabo Mohammed ya yi tsokaci kan burin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, inda ya ce idan da gaske yana son yin irin tasirin da wasu shugabanni s**a yi, musamman irinsu Rabi'u Kwankwaso, ya kamata ya bi wata hanya ce dabam. “Idan yana son kwaikwayon irin tasirin da aka gani a wasu jihohi kamar yadda Rabi'u Musa Kwankwaso yayi a jihar Kano, to ya kamata ya bar manyan jam’iyyun da ke cike da rigingimu ya koma kananan jam’iyyu ya gina su,” inji shi.
Ya ƙara da cewa hakan na iya zama babbar nasara a siyasance idan aka yi daidai. “Idan ya yi haka, zai iya zama political victory, domin zai samu cikakken iko da jagoranci ba tare da cikas ba,” a cewarsa.
Masharhancin ya kuma bayyana cewa manyan burikan gwamnan na iya takaita ne ga harkokin cikin gida. “Abin da ya rage masa shi ne kafa gwamna a Bauchi ko kuma ya zama sanata a Bauchi ta Kudu idan yana son taka rawa a matakin ƙasa,” inji shi.
A ƙarshe, Sabo Mohammed ya ce wannan hanya na iya ba wa gwamnan dama mai yawa fiye da shiga jam’iyya mai cike da rikice-rikice, musamman idan yana da goyon bayan jama’a a jihar Bauchi. “Idan yana da mutanensa da goyon bayan al’umma, wannan hanya ce mafi sauƙi da za ta ba shi cikakken iko da damar cimma burinsa,” inji shi.