Waziri aku

Waziri aku LABARAN NISHADI
••••••••••••••••••••••••••••

04/11/2023

Amincin Allah ya tabbata a gare ku, ya ku mabiya wannan shafi, da fatar kuna cikin ƙoshin lafiya.

Ina godiya ƙwarai da kulawarku, masu tambaya a Facebook da masu bugo waya domin jin halin da muke ciki.

In sha Allahu nan ba da jimawa ba, za mu ci gaba da labarinmu kamar yadda aka saba.

Na gode.

Bukar Mada
4/11/2023

28/09/2023

Allah ka kara rufamana asiri duniya da lahira ka shiryar damu bisa tafarki ma daidaici

12/10/2022

Slm

15/09/2020

🎃YAR ♡ TALAKAWA🎃

Bismillahil rahmanil rahim"

Tafe nake a cikin wata kasuwar fruits(kayan marmari),nazo wuce wata rumfa,mai dauke da kayan marmari kala kala, wata kyakkyawar yarinya na hango a ciki, sanye take da wasu kodaddun atamfa riga da skirt,yarinyar ba zata wuce shekaru sha shidda ba, sai tsalle take tana fadin, kuzo ku siya, namu sunfi zaki, tana maganar fuskar ta dauke da murmushi,kumatun ta sun lotsa, mutane dayawa s**a tsaya a wurin suna kallon ta,kwanin sha'awa, gata kyakkyawa, ta dauko lemu,ta dauko alaba da sauran fruits din, tana fadi musu anfanin su,dan kawai su siya.Ni afrah nace bari na bi wannan yarinya mai siyar da kayan marmari, dan kwaso wa masoyana labari.Wani mutuni na gani ya kira ta ciki, yarinyar na murmushin mai kara mata kyau, tace ya habu har zamu tashi ne, naga akwai sauran jama'a a kasuwar, mu dan kara jira kaji, ya habu ya kalle ta yace NI'IMATU, ke bakya gajiya ne , tun safe k**e tsalle tsallen nan, niimatu ta dara, ta kai wa ya habu naushi a hannu, ni ban gaji ba Allah, mudan kara jimawa kaji, ya habu yayi dariya, ke kam da namiji ce , da anyi jarumi.Niimatu ta daure fuska, ohh ni yanzu ba jaruma bace ashe ko? Ta turo masa dan karamin bakin ta, ya habu yadan dungurar mata da kai, yace a tsalle tsallen k**e jaruma, ya wuce waje abunsa, niimatu taja tsaki, sannan ta murmusa itama ta bishi wajen. Umma !umma! Ina k**e gamu mu dawo, umma ta fito cike da fara'a, niimatu tayi saurin ajiye ledar hannunta,tayi wurin umman ta rungume ta, umma tayi murmushi, niimatu bakya girma ko?, niimatu tayi murmushin ta, tana kallon umman tace, umma idan dai a gaban kine ni har yanzu yarinya ce karama, koda na haifi yara dari ne, umma tayi dariya , ya habu ya karaso ciki, yace umma sannu da gida?, umma tace ko keda sannu habu.Sunyi wanka sun ci abinci, suna zaune dan tsakar gidan su, wanda ko siminti babu,ga ginin gidan duk ya lalace duk da na bulo ne, amma da yake ya tsofa, duk ya zaizaye.Ya habu yasa hannu cikin aljihun sa, ya fiddo wasu yan kudi, ya mikawa umman, ga wannan nasan malam sahabi yazo, umma tace yazo kuwa dazun da rana, dama yace gobe idan munsan bamu da kudin hayan , toh kada mu sake ya iske mu anan, ya habu ya girgiza kai, Allah yana sane damu, kuma mun gode masa, daya barmu da ranmu da kuma lafiyar mu ,umma tace aini har yanzu ina nan ina wa bawan Allah nan daya baka rumfa , kuma ya baka kudin jarin nan addu'a, dan ba karamin taimakon mu yayi ba ,Ya habu yace nima ina masa addu'a har yanzu, umma.Niimatu dake kwance kanta bisan cinyan umma, tana barci,sai munshari take, tana juye juye ,ya habu ya tafka mata bugu a baya, kee uwar munshari tashi ki koma daki. Niimatu ta mike ta kura masa ido tana smiling, ya habu yaja tsaki, ke wai bakya gajiya da murmushi ne, kumatun ki baya gajiya?, umma tace kyele ta habu ta huta, ba karamin kokari take ba, niimatu tace nifa ba barci nake ba yaya, kuma yaushe nayi munshari?, ya habu ya mike yace umma sai da safe, ke kuma , ya nuna niimatu, saura kiyi ta barci, kada ki tashi ki shirya da wuri, niimatu ta washe baki, ta nuna kanta nifa jaruma ce yaya.... ya habu yayi dan tsaki ya fice abunsa, dan idan zai biye wa niimatu bazai samu barcin kirki ba....

27/08/2020

*YAR TALLAH *

*CHAPTER 1*

DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07039443260

Tafe tAke tana rusa kuka wiwi,,,,,wiwi
Duk ta hada miyau majina da hawaye ta dame fuska gaba
daya
Rungume take da tiren tallan tata wanda ba komai a cikinsa
sai ihu take kwararawa tana kiran wayyo kudina wayyo ni
kudina
Mutane sai kallonta sukeyi masu tausayi daga cikinsu su
kirata suji abinda ya faru su lallasheta ta tafi
A haka taita saqawa ta lunguna harta iso layin gidansu
Tunda ta iso layin rabi,u wanda bai wuce dan kimanin
shekara goma sha huduba kejiyo sautin kukanta yana duqe
yana faman wanke wanke
Yai niyyar miqewa karaf s**ai ido hudu da inna laure
Ta watsa masa wani irin kallo simi simi ya koma yaci gaba
da wanke wanken
Tace munafuki dan iska wlh ka sake tashi baka gama
wanke wankennaN ba saina karya maka qafafu
Ta qara jan tsaki ta hankade labule ta shige Daki
Rabi,u yai saurin tsame hannunsa daga wanke wanken ya
kwasa yai waje da gudu
A bakin kofar zauren s**ai kicibus yace waya tabakine
saude?
Ta qara fashewa da wani kukan wanda yafi nada sauti
Rabiu ya qara janta jikinsa kiyi haquri saude fadamin meke
faruwa?
Tadan sassauta da kukan tace kudina yaya kudin tallah na
wani ya kwaceminsu
Rabiu ya dafe kirji ido waje yace garin yaya saude?
Kinsan halin inna laure kuma dukanki zatayi
Ta qara fashewa da kuka wayyo yaya dan allah ka roqeta
karta dakeni
Ya danyi jimm kiyi haquri saude babu yaddah zan iya kixo
muje kawai ta dakekin
Ta qanqameshi wayyo yaya wlh yankani zatayi
Idanunsa s**a kawo kwallah ya cije yace zo muje saude
insha allahu bazata dokekiba kinji?
Kai kawai ta daga masa tana share hawaye yaja hannunta
s**a shiga ciki
Tsaye take a kofar daki da alamun ta cika ta tumbatsa jira
kawai take a tabata ta bashe
Saude ta qara fashewa da kuka wayyo allah na wlh yaya
dukana zatayi
Inna laure ta zaburo tayo kansu
In dokeki don ubanki laifin me kikayi?
Hala kin dawomin da sauran raguwar alalen ne ko?ta fada
lokacin data shaqo wuyanta
Ina kudun suke in gani?
Ta qara

Alhamdulillah
06/05/2014

Alhamdulillah

Address

Bauchi
BAUCHISTATE

Telephone

+2347039443260

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Waziri aku posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category