23/11/2025
ABU YA ZO KARSHE: SANATA SHEHU BUBA UMAR YA KAI DAUKI GA MAKARANTAR ISLAMIYYAR DA TA SHAFE SHEKARA 26 BA TA KAMMALA BA.
__________
Mai girma Sanata na Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya ɗauki nauyin kammala ginin makarantar Islamiyya da ke Unguwar Yalwan Makaranta, cikin Karamar Hukumar Bauchi, wacce ta shafe shekaru 26 tun daga 1999 ana aiki ba tare da kammalawa ba.
Sanatan ya shiga aikin ne bayan korafe-korafen da al’ummar yankin s**a kai masa, inda s**a bayyana irin dogon jinyar da dalibai da malamai ke yi saboda rashin kammala ginin makarantar.
A halin yanzu, aikin na ci gaba da tafiya cikin sauri, domin tabbatar da cewa yara da matasa za su samu ingantaccen wurin karatun addini cikin girmamawa da kwanciyar hankali.