23/09/2022
DALILAI (6) DA S**A SANYA ZANYI AIKI TUKURU DOMIN GANIN NASARAR PETER OBI NA JAM'IYYAR LABOUR
Ni dan Najeriya ne kamar kowannen ku, wanda ya damu da halin da Kasar nan take chiki sakamakon zalunchi, rashin tsaro da kuma rashin kwarewar Shugabanchi, wanda ya samo asali daga Shugabanni marasa kishi da tausayi.
Inada buri kamar sauran Jama'a, na ganin na gudu a Najeriya zuwa wata Kasa domin samun ingantachchiyar rayuwa, in har wadannan kashe kashe s**a chigaba a Arewa, duk da guduwa bai taba zama buri na ba, ballantana rayuwa a wajen da babu 'yan uwa da abokaina.
Wannan yasa nakeso, naga Najeriya ta samu chigaba, ta zama Kasar da zamuyi alfahari da'ita. Wannan yasa nayi alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin chigaban wannan kasa, sai dai hakan ba zai yiwu ba sai mun samu Shugaba kwararre kuma adali. Bayan tantanche 'yan takara danayi chikin nutsuwa, nagano chewa, Mr Peter Obi shine mutumin da zai iya kaiwa Kasar mu tudun mun tsira, lura da dalilai kamar haka:
1. Peter Obi shine mutumin da kwarewar sa ta bayyana a bangaren gudanar da mulki, wanda hatta sauran 'yan takara basa musun hakan. Wannan yasa a zaben 2019, Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi ya zame masa mataimaki, haka Kwankwaso shima yayi kokarin Peter Obi ya zame masa Dan takaran mataimaki a bana. Peter Obi ya samu wannan farin jini ne, sakamakon sanin shi kwararre ne a harkar mulki da rikon amana.
2. Muna bukatar zaben Peter Obi, domin kawo karshen siyasar kabilanchi. A 2015 mafi yawan mu, mun zabi wanda muke ganin zai taimaki yankin mu, addinin mu da kuma kabilar mu, wanda hakan bai sa mun tsallake rashin tsaro da tsadar rayuwa ba. Duk da kuwa kabilar mu, addinin mu da yankin mu dayane da Shugaban Kasa.
Ta tabbata chewa, wadannan mutanen, sun damu da addini da kabila ne a lokachin da suke neman kuri'a ko kuma neman kariya daga laifukan su. Wannan yasa, ya zama wajibi a wannan karon, mu fifita kwarewa da amana, sama da banbanche banbanche dake tsakanin mu, da basu amfane mu da komai ba.
3. Zaben Peter Obi a matsayin Shugaban Kasa daidai yake da juyin juya hali, wanda zai dawo da mulki ga talakawa. Rashin girmamawa da sauran 'yan takara suke nuna mana, mu talakawa a bayyane yake, wannan yasa suke alfahari da tasirin Jam'iyyun su, kai kache ba'a dimokradiyya muke ba. Zaben Peter Obi zai karfafa dimokradiyya ya kuma tabbatar wa kowa, chewa talakawa ne suke da fada aji ba tasirin Jam'iyyu ba. Zai kuma daga darajar talakawa ta yanda Shugabanni zasu gane, talaka shine mai wuka da nama.
4. A bayyane yake, chewa bamason rabuwar Kasar mu Najeriya, duk da kuwa muna sane da nuna fifiko da akeyiwa wasu 'yan kasa, wanda yasa, ya kamata muyi duk abinda ya dache wajen kwantar da hankali, zaman lafiya da hadin kan Kasar mu. Zaben Peter Obi a matsayin Shugaban Kasa zai farfado da kauna da hadin kai a tsakanin mu 'yan Najeriya.
5. A bayyane yake, mutanen da suke PDP jiya, sune APC a yau, kuma sune suke zagaye zagaye a tsakanin wadannan Jam'iyyu, wannan ya kamata ya bude mana idanu mu fahimchi chewa, wadannan mutane sune matsalar Kasar mu, basu da kishi da kuma gogewa na cheto wannan Kasa. Muna bukatar sabbin jini, masu ilimi, matasan da zasu iya chire kitse a wuta, game da matsalolin karni na 21, wanda wannan shine abinda muke tsammani daga guguwar Peter Obi.
6. Muna bukatar Shugaba mai jini a jika, wanda duniya take martabawa, wanda yasan halin da duniya take chiki, ba wanda zai dogara da labarun karya da za'a bashi ba. Babu shakka, Peter Obi shine ya dache da irin mutumin da Kasar mu take bukata saboda nagartar sa.