31/01/2022
Hadin gwuiwa don cigaban mazabar tarayya na Darazo/Ganjuwa
Cikin amincewar Allah SWT jiya Gwamnatin Jahar Bauchi, ofishina da al'umman mazabar Darazo/Ganjuwa sun shiga hadin gwuiwa don inganta rayuwar al'umma a fannin ilimi, kiwon lafiya da inganta masarautun mu.
Asibitocin da muka gina su ta gidauniyar MMS foundation a Sade, Gabarin, Soro da Miya na mata da kananan yara, Insha Allahu zasu kasance masu bada services na ultra sound scanning, genotype test, sayar da magunguna, karbar haihuwa da makamantan su akan farashi mai sauki.
Ambulances guda 6 da muka saya (outside the (national budget) insha Allahu zasu kasance masu conveying mata masu haihuwa, marassa lafiya da kananan yara zuwa asibitocin guda 4 daga dukkan lungu da sako na mazabar Darazo/Ganjuwa. Zasu yi aiki ne tare da mata masu aikin sa kai 441 da aka basu training wajen wayar da kan mata akan amfanun awu, rigakafi da yin karatun boko dana addini.
Makarantun mu na Gifted Senior Secondary Schools a Sade da Soro zasu kasance masu bada foundation da preparing yaran mu don koyan STEAM courses a makarantun gaba da sakandare. Uniform zai kasance kyauta ne a wannan makarantu Insha Allahu. Special Primary School a garin Lanzai kusa da iyakar Jahar Bauchi da Yobe kuma makarantan primary ne na marayu yan gudun hijra da s**a rasa iyayen su.
Wadannan makarantu da asibitoci sun samu kyautan kudi N7,000,000 don fara aiki. sannan an musu provision a "Constituency project" component na kasafin shekarar 2022 na N3million kowanne, don tabbatar da wanzuwar gudanarwan su.
Doriya akan sabunta gidajen masu gundumomin Kubi da Konkiyel, mun samar da motoci wa dukkan masu girma, Hakiman da muke dasu a mazabar Darazo/Ganjuwa domin rage musu dawainiyar zirga zirga.
Ina mai amfani da wannan damar wajen mika godiyan al'umman da nake wakilta wa Mai Girma, Gwamnan Jahar Bauchi, Sen. Bala Abdulkadir Mohammed, CON (Kauran Bauchi) wajen bamu damar kawo wannan gudumawa a wadannan fannoni masu muhimmanci na rayuwar mu. Muna godiya musamman akan bamu filin gina makarantun Gifted Secondary Schools na Darazo da Kafin Madaki da Mai Girma Gwamna yayi da kuma hadin kai da ma'aikatun ilimi da kiwon lafiya suke bamu.
Muna godiya wa Kakakin Majalisar Tarayya, Rep. Femi Gbajabiamila akan shawarwari da gudumawan da ya bayar wajen samun nasaran wannan hadin gwuiwa.
Ina kira ga al'umman mazaban mu da akayi domin su da su rungumi wadannan ayyuka don cin gajiyar su.
Ubangiji SWT Ya kasance tare damu cikin taimakonSa da agajinSa.