13/03/2026
Gidauniyar Professor Pantami Ta Kaiwa Jam'iyyar APC Ta Jihar Gombe Kyautar Naira Miliyan 10,000,000, Da Macaroni Katon Dubu 1,000, Na Azumin Ramadan Da Kuma Azumin Lenten Wadanda Dukkansu Biyu Ake Yi A Yanzu
Idan baku manta ba a kwanakin baya gidauniyar Professor Isa Ali Pantami ta raba kayayyakin abinci fiye da buhu 12,500 da kuma kuɗi Naira miliyan 33,750,000 ga malaman Addini a jihar Gombe, a cikin wannan watan na Ramadan.
A jiya Alhamis tawagar wakilan Professor Isa Ali Pantami, karkashin jagorancin Alhaji Ahmad Abubakar Walama, tsohon Kwamishina mai kula da harkokin kananan hukumomi da Masarautu kuma tsohon shugaban Ƙaramar hukumar Dukku (sau biyu) ya jagoranta, da sauran manyan tawaga ta Dattawa, malamai da matasa.
Tawagar ta ziyarci ofis din jam'iyyar, inda s**a kai kyautar Naira miliyan 10,000,000, da Macaroni Katon dubu 1,000, domin azumin Ramadan da kuma Azumin Lenten wadanda dukkansu biyu ake yi a yanzu.
Tawagar ta samu tarba mai kyau a hedkwatar APC ta jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam'iyyar ta jiha Mohammed Dantata Ndus, wanda ya samu wakilcin mataimakinshi Abdullahi Baba Abuja da Sakataren jam'iyya da mambobin Kwamitin zartarwar Jam'iyya na jiha.
Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya shafe shekaru da dama yana tallafawa jama’a a lokacin watan Ramadan, inda adadin tallafin yake sauyawa shekara bayan shekara.