26/07/2025
DA DUMI-DUMI: Hukumar DSS Ta K**a Sultan Gali Kan Bidiyon AI Dake Nuna Shugaba Tinubu Ba Lafiya
A jiya ne jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) s**a cafke wani matashi mai suna Sultan Gali a Kano bisa zargin wallafa bidiyon da ke nuna shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cikin rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa bidiyon da aka wallafa na amfani da fasahar AI ne (AI-generated video), inda aka yi amfani da wani tsohon bidiyo na Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da aka gyara aka maye gurbin fuskarsa da ta Tinubu. Wani mai amfani da TikTok ya bude asusun da suna “Bola-Asiwaju” ya wallafa bidiyon, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
DSS ta bi sawun Sultan daga Kano zuwa Abuja inda aka k**a shi tare da gurfanar da shi a gaban kotun majistare. Har zuwa yanzu dai ba a saurari bukatar belinsa ba, kuma an tura shi gidan gyaran hali na Keffi.
Masana tsaro da masu sharhi kan harkokin siyasa na bayyana damuwa, suna cewa k**ata irin wannan kan bidiyon da ba gaskiya ba yana nuna rashin iya bambance hakika da fasahar zamani a tsakanin hukumomin tsaro.
Wasu na dariya da cewa, "Idan haka ne, to kamun Bello Turji zai fi sauki." K**ar yadda Barista Nuhu Dantani ya wallafa a shafin sa na Facebook.