17/01/2026
TSOHUWAR AJIYA: Magana Mai Ratsa Zuciya Daga Bakin Marigayi Sheik Ja'afar Game Da Halin Da Nijeriya Take Ciki
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Malam ya ce "Kowa àźzalumi wannan hali da muke ciki ba fa Allah zai kawo Mala'iku ba ne su gyara, mune za mu gyara mu Bil'adama"
Abinda ya faru na matar nan da 'ƴa 'ƴanta da aka ka*she da rana tsaka a jihar Kano, sai ya tabbatar min da maganar Malam, musamman wacce ya ce "Idan Allah Ya yi ka a Nijeriya, tabbas Ya so Ya jarrabe ka" gashinan Kuwa muna gani.
Komai ya faru a Arewa ba a ɗaukarsa da muhimmanci, abubuwa da yawa idan s**a faru saidai ayi mamaki, komai aka yiwa 'yan Arewa daga su manta Sai kawai suyi mamaki, tabbas wannan Rayuka nasu suna buƙatar Adalci, hankali bazai kwanta ba, rayuwa bazatayi daɗi ba, matukar za'a riƙa ka*she rayukan Musulmi, musamman waɗanda basuji ba, basu gani ba, wannan abu bai dace da Kano ba, baidace da kanawa ba, kuma bazai taɓa zama abin mantawa ba, Allah Yaji ƙansu.
Malam Ya ƙara da cewa "Ba mu kaɗai muke raye ba a duniya, a Afrika kaɗai ƙasashe nawa ne? Dan me muka zama daban? A duniya ƙasashe nawa ne? Dan me (Najeriya) muka zama daban? Dan me sauran suke tafiya a tsari, amma mu Bamuda tsari?
Dan me daidai da waya ta hannu mutumin Nijar sai ya Buga cikin kwanciyar Hankali, amma kai ɗan Najeriya Baka bugawa cikin kwanciyar Hankali? Tambayar marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam kenan.
Muna fatan Allah Ya yi wa Malam Rahama, su kuma Allah Ya jiƙansu, amin.