Dan Arewa Media

Dan Arewa Media Zauren siyasa da wayar da kan al’umma a Arewacin Najeriya.

Mun mayar da hankali kan:
- Labaran siyasa
- Nazarin gwamnati da shugabanci
- Zaɓe da dimokuraɗiyya
- Bincike kan al’amuran ƙasa
- Wallafa Muradan al’umma

09/06/2026

Fitar Lado dan marke daga wajen taron

09/06/2026
Jam’iyyar PDP ta bayyana Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe domin shiga zaɓen shekarar 2...
26/05/2026

Jam’iyyar PDP ta bayyana Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe domin shiga zaɓen shekarar 2027.

Sanarwar ta jawo martani daga sassa daban-daban na al’umma, inda wasu ke bayyana hakan a matsayin wani sabon salo na siyasa da jam’iyyar ke shirin gabatarwa a jihar.

Prof. Pantami, wanda ya yi fice a fannin ilimi da harkokin gwamnati, ya taɓa rike mukamai daban-daban a matakin ƙasa, lamarin da ya sa masu sa ido ke kallon takararsa a matsayin wacce za ta ƙara zafafa fafatawar siyasar Gombe kafin babban zaɓen 2027.

Ana sa ran jam’iyyun siyasa da sauran ‘yan takara za su ci gaba da bayyana shirye-shiryensu yayin da lokacin zaɓe ke ƙaratowa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin Arewa ne ke da babban tasiri wajen zaɓar wanda z...
18/05/2026

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin Arewa ne ke da babban tasiri wajen zaɓar wanda zai zama shugaban kasa a Najeriya ta hanyar yawan kuri’un da suke da su.

Atiku ya nuna takaicin sa kan yadda wasu daga cikin ‘yan Arewa ba su fahimci irin wannan karfin ba da suke da shi, yana mai cewa maimakon su tsaya tsayin daka wajen kare muradun yankin su, amma suke nuna biyayya ga wasu da bai kamata su fifita ba.

An fara ganin alamun sabuwar takaddama a siyasar jihar Kogi bayan da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya bayyana ciki...
18/05/2026

An fara ganin alamun sabuwar takaddama a siyasar jihar Kogi bayan da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya bayyana cikin jerin ‘yan takarar da jam’iyyar APC ta tantance domin fafatawa a zaben fidda gwani na kujerar Sanata.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ta amince da mutane 16 da za su shiga zaben, bayan kammala tantancewa da duba cancantar masu neman takarar.

Shigar Yahaya Bello cikin wannan fafatawa ya kara jan hankulan masu bibiyar siyasa, musamman ganin irin tasirin da yake da shi a jihar tun bayan kammala wa’adin sa na mulki.

Masana harkokin siyasa na hasashen cewa zaben fidda gwanin na APC zai kasance daya daga cikin zabukan cikin gida mafi zafi a jihar, duba da yadda manyan ‘yan siyasa ke kokarin karbe iko da tasiri a yankunan su.

Ana sa ran zaben da za'a gudanar ba da jimawa ba zai kara bayyana inda akalar siyasar Kogi ta dosa kafin babban zaben 2027.

17/05/2026

Ahmed Saleh Junior yayi martani mai zafi ga gwamna Raɗɗa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Ahmad Aminu Yar’adua, ya shiga jerin manyan ‘yan siyasar da s**a nuna a...
15/05/2026

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Ahmad Aminu Yar’adua, ya shiga jerin manyan ‘yan siyasar da s**a nuna aniyar su ta neman kujerar gwamnan Jihar Katsina a babban zaɓen shekarar 2027, bayan da ya sayi fom ɗin tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Rahotanni sun bayyana cewa matakin da Alhaji Ahmad Aminu Yar’adua ya ɗauka na sayen fom ɗin takara ya ƙara dumama harkokin siyasa a jihar Katsina, musamman ganin yadda yake da ƙwarewa da gogewa a harkokin mulki da gudanar da gwamnati.

Alhaji Ahmad Aminu Yar’adua, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar jihar da s**a daɗe suna taka rawa wajen ci gaban siyasa da gudanarwar gwamnati. Masu bibiyar al’amuran siyasa na ganin fitowarsa takara a ƙarƙashin ADC zai kawo sabon salo da gasa a siyasar jihar kafin zaɓen 2027.

Wasu magoya bayan jam’iyyar ADC sun bayyana farin cikin su kan matakin da tsohon sakataren gwamnatin ya ɗauka, inda s**a ce suna da yaƙinin cewa gogewar sa da fahimtar sa kan harkokin mulki za su taimaka wajen samar da shugabanci nagari idan har ya samu nasarar lashe zaɓen.

A gefe guda kuma, masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa shigowar Ahmad Aminu Yar’adua cikin tseren neman kujerar gwamna zai iya sauya yanayin siyasar jihar Katsina, musamman a daidai lokacin da jam’iyyu daban-daban suke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ana sa ran nan gaba kaɗan ɗan takarar zai bayyana manufofin sa da tsare-tsaren da yake da su domin ci gaban Jihar Katsina da walwalar al’ummar jihar idan har aka ba shi dama ya jagoranci jihar.

Yar takarar kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya, Hajiya Amina Lawal Rafin Dadi, ta maida fom ɗin tsay...
14/05/2026

Yar takarar kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya, Hajiya Amina Lawal Rafin Dadi, ta maida fom ɗin tsayawa takara a yau Alhamis, 14 ga watan Mayu, 2026, ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Maida fom ɗin na daga cikin muhimman matakan da ke nuna aniyar Hajiya Amina Lawal Rafin Dadi ta shiga takarar kujerar Sanata domin wakiltar al’ummar Katsina Central a babban zaɓe mai zuwa.

Taron ya samu halartar magoya baya da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ADC, inda s**a bayyana goyon bayansu tare da fatan samun nasara a tafiyar siyasar tata.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin shigar Hajiya Amina Lawal Rafin Dadi cikin takarar zai ƙara armashi a siyasar mazabar Katsina ta Tsakiya.

Address

Wuse Zone 2
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Arewa Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share