Arewa For Asiwaju

Arewa For Asiwaju Relief Is Coming.....

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) Na Alhinin Sanar Da Rasuwar Kakakinta Na Farko Alh Suleiman Abdulazeez Ƙungi...
20/05/2026

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) Na Alhinin Sanar Da Rasuwar Kakakinta Na Farko Alh Suleiman Abdulazeez

Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) cikin matuƙar alhini da jimami take sanar da rasuwar Alhaji Suleiman Abdulazeez, ɗaya daga cikin waɗanda s**a assasa ƙungiyar tare da kasancewa kakakinta na farko.

Rasuwar marigayin ta zo a matsayin babban rashi ga Arewa da Najeriya baki ɗaya, domin kuwa ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu fafutukar ganin an samu adalci, ilimi, zaman lafiya da gyaran al’umma a Arewacin Najeriya. Har zuwa ƙarshen rayuwarsa, marigayi Suleiman Abdulazeez ya ci gaba da kasancewa murya mai ƙarfi wajen kare gaskiya, tsayawa ga waɗanda ake zalunta, da kuma fafutukar cigaban Arewa tare da haɗin kan ƙasa.

A matsayinsa na kakakin farko na CNG kuma tsohon kakakin Northern Elders Forum, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana matsaloli da ƙalubalen da s**a shafi Arewa da Najeriya baki ɗaya. Cikin hikima, jarumtaka da kishin ƙasa, ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaƙi da jahilci, rashin tsaro, talauci, rashin adalci da duk wani abu da ke hana cigaban al’umma.

Marigayi Suleiman Abdulazeez ya shahara da tawali’u, sauƙin kai, gaskiya da rayuwa mai cike da sadaukarwa duk da irin gagarumar gudummawar da ya bayar ga al’umma. Ya kasance mai cikakken yaƙinin cewa ilimi da wayar da kai su ne manyan hanyoyin da za su ceto Arewa daga talauci, jahilci da koma baya.

CNG tana alfahari da irin rawar da ya taka wajen kare muradun Arewa, mutunta da kare martabar masarautar Zazzau, tare da ƙoƙarin gina al’umma mai cike da adalci, ɗa’a da haɗin kai.

Hakika rasuwarsa ta haifar da babban gibi wanda zai yi matuƙar wahalar cikewa. Arewa ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun muryoyinta masu kishin jama’a, masana masu hangen nesa da jajirtattun ’yan kishin ƙasa.

Yayin da muke alhinin wannan babban rashi, muna ci gaba da tuna kyawawan halaye da rayuwar sadaukarwa, mutunci da hidimar al’umma da marigayin ya rayu a kai. Tarihinsa da gudummawarsa za su ci gaba da zama abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da dama, ’yan uwa, abokan arziki da dumbin masoya a faɗin Najeriya.

Ƙungiyar CNG tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalansa, abokan aikinsa, al’ummar masarautar Zazzau, mambobin Northern Elders Forum, da ɗaukacin ’yan Najeriya da wannan babban rashi ya shafa.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yawaita masa rahama, Ya saka masa da Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.

Sa Hannu:
Comrade Jamilu Aliyu Charanchi
National Coordinator
Coalition of Northern Groups

Tsohon ɗan takarar Majalisar Jiha na Ƙaramar Hukumar Kabo a shekarar 2023, Hon. Rabi'u Sayyadi Kazode, ya fice daga jam’...
23/04/2026

Tsohon ɗan takarar Majalisar Jiha na Ƙaramar Hukumar Kabo a shekarar 2023, Hon. Rabi'u Sayyadi Kazode, ya fice daga jam’iyyar PDP.

Tun a ranar Litinin 20/4/2026 tsohon ɗan takarar ya bayyana ficewarsa daga tsohuwar jam'iyyar tasa, inda ya miƙawa shugaban jam'iyyar PDP a mazaɓarsa ta Masanawa takardar ficewar ta sa.

Yayin ficewar ta shi, ya godewa jagororin PDP dake mazaɓarsa, haka kuma ya jaddada cewa yanzu lokaci yayi tunda wasu tsirarun mutane sun rusa PDP, to dole mu tafi gidan da zamu ceci yankinmu da jiharmu baki ɗaya.

Daga karshe ya godewa dukkan masoyansa da magoya bayansa fiye da mota hamsin da s**a masa rakiya zuwa mazaɓarsa, inda ya shelanta musu komawarsa APC tare da umartar mabiyansa baki daya da su koma mazabunsu su yankin katin jam'iyyar APC don tunkarar zaɓen 2027 insha Allah.

Katafila Sarkin Aiki!Sabbin hotunan mai girma gwamna kenan da aka dauka ranar Talata, yayin da yake sauraron koken al'um...
17/04/2026

Katafila Sarkin Aiki!

Sabbin hotunan mai girma gwamna kenan da aka dauka ranar Talata, yayin da yake sauraron koken al'ummar jihar Kano.

Ku yi watsi da dukkan hotunan da ake yaɗawa, mai girma gwamna na cikin ƙoshin lafiya yana cigaba da zubowa Kanawa aiki ba dare ba rana.

Daga Arewa Insider

Babban taron Maritime ya fara gudana yanzu haka a Abuja.
09/04/2026

Babban taron Maritime ya fara gudana yanzu haka a Abuja.

Babbar Magana: Hon. Nafiu Bala Gombe tare da tawagarsa sun fito zanga-zanga suma a yau cikin babban birnin tarayya Abuja...
09/04/2026

Babbar Magana: Hon. Nafiu Bala Gombe tare da tawagarsa sun fito zanga-zanga suma a yau cikin babban birnin tarayya Abuja.

Yayin zanga-Zangar da suke gudanarwa sun bayyana cewa sun fito ne domin su yi kira ga David Mark, Atiku, Amaeci, Kwankwaso, Obi, da kuma Aregbesola da s**a gudanar da zanga-zanga a jiya su bar musu jam’iyyarsu ta ADC tare da barin su domin su samu damar tafiyar da harkokinsu cikin aminci.

Shin me kuke tunanin suna so?

Ƙungiyoyin fararen hula daga Arewacin Najeriya da kuma kudancin kasar nan sun jaddada kiran cewa dole Elrufa'i ya fuskan...
26/02/2026

Ƙungiyoyin fararen hula daga Arewacin Najeriya da kuma kudancin kasar nan sun jaddada kiran cewa dole Elrufa'i ya fuskanci dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, babu wani tsohon shugaba da yafi karfin doka ko waye shi.

Abubuwan daya aikata lokacin da yake kan karagar mulki tun daga kwace kadarorin al'umma, take hakkin dan'adam, k**a mutane ba gaira ba dalili, ya zama dole yanzu ya fuskanci hukuncin abinda ya aikata.

Daga Nura Jamilu
Shugaban masu rajin kare demokradiyya na Kaduna

Ina Ka Ke Lokacin Da El-Rufai Ke Gallazawa Mutane Da Sace Dukiyar Al'ummar Jihar Kaduna ~ KVU Ta Caccaki Atiku Abubakar ...
25/02/2026

Ina Ka Ke Lokacin Da El-Rufai Ke Gallazawa Mutane Da Sace Dukiyar Al'ummar Jihar Kaduna ~ KVU Ta Caccaki Atiku Abubakar

Ƙungiyar Kaduna Voices United (KVU), wadda ta yi fice wajen tabbatar da anyi gaskiya, riƙon amana da adalci a harkokin mulki, ta yi martani kan kalaman da Atiku Abubakar da yayi dangane da tsare tsohon gwamnan Kaduna State, Nasir El-Rufai.

KVU ta bayyana cewa duk da cewa damuwa kan lafiyar El-Rufai abu ne mai muhimmanci, akwai tambaya kan dalilin da ya sa irin wannan ƙwazo wajen neman gaskiya da rikon amana bai bayyana ba a lokacin da yake kan mulki, lokacin da ake ta zarge-zargen sa da cin hanci, tauye haƙƙin jama’a da kuma amfani da iko wajen tsoratar da masu adawa. A cewarsu, nuna damuwa yanzu kaɗai na iya zama misali na son zuciya da rashin daidaito a siyasa.

Ƙungiyar ta jaddada cewa El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume masu tsanani daga Department of State Services (DSS), wanda ya shigar da ƙara uku a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Tuhume-tuhumen sun shafi zargin sa da yin satar bayanan waya ba bisa ƙa’ida ba, rashin kai rahoton bayanan da aka ce ya samu, da kuma jefa tsaron ƙasa cikin haɗari, zarge-zargen da s**a samo asali daga wata hira da ya yi a tashar Arise TV inda ya yi iƙirarin samun damar sauraron wayoyin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Haka kuma, yana ƙarƙashin bincike daga Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) kan zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a da s**a kai kimanin naira biliyan 432, ciki har da kuɗaɗen da ake alaƙantawa da wasu manyan ayyuka k**ar na layin dogo na Kaduna. Bugu da ƙari, Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) na bincike kan zargin cin zarafin ofis da kuma take dokokin saye da bayar da kwangila.

KVU ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge ba ƙananan batutuwa ba ne, domin sun shafi tsaron ƙasa, dukiyar jama’a, da kuma amincewar al’umma ga shugabanci. Don haka, ƙungiyar ta yi gargadin cewa yunƙurin wanke El-Rufai daga waɗannan matsaloli kafin kammala bincike da shari’a zai iya tauye tsarin dimokuraɗiyya da ƙa’idar cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta tabbatar da bin doka da oda wajen tsarewa da shari’ar El-Rufai, tare da bayyana gaskiya game da halin da yake ciki. Sun kuma yi kira ga shugabannin siyasa da su guji nuna son kai, su fifita gaskiya da adalci sama da alaƙar siyasa, domin tabbatar da cewa Najeriya ta samu shugabanci mai tsafta da rikon amana.

Sa hannun
Yusuf Dama'i
Secretary KVU

Ka Daina Siyasantar Da Harkokin Tsaron Kasa ~ Martanin Nigerian Unite Ga Atiku Abubakar Kalaman Atiku Abubakar na cewa i...
24/02/2026

Ka Daina Siyasantar Da Harkokin Tsaron Kasa ~ Martanin Nigerian Unite Ga Atiku Abubakar

Kalaman Atiku Abubakar na cewa idan wani abu ya samu tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai gwamnatin tarayya za a ɗorawa laifi ko alhakin haka, ya nuna wani salo na siyasa da muka saba gani a Najeriya, siyasar neman tausayin jama'a domin kauce wa fuskantar shari’a. Irin wannan magana k**ar yunƙuri ne na matsa lamba ga hukumomi, maimakon a bar doka ta yi aikinta.

Sai ɗan siyasa ya gama satar dukiyar ƙasa yayin da yake karagar mulki, amma da zarar hukumomi sun fara bincikensa sai ya bijiro da rashin lafiya don kaucewa tuhuma, to wannan wasan kwaikwayon dole yazo karshe a wannan lokacin. Domin wannan kiran na ka a wannan lokacin ba komai illa neman mafaka ta siyasa don biyan bukatar kanku bakomai ba.

A ƙasarmu, ya zama ruwan dare duk lokacin da ake tuhumar ‘yan siyasa, sai su bayyana kansu a matsayin marasa lafiya domin neman beli ko sassauci. Amma da zarar sun samu damar fita, sai mu gan su suna halartar taruka, suna tafiya ko’ina cikin ƙoshin lafiya. Wannan dabi’a ta sa jama’a s**a fara tambayar gaskiyar ikirarin rashin lafiyar da ake yi a irin waɗannan lokuta.

Saboda haka, a yanzu ba daidai bane yayin da Elrufa'i ke fuskantar tuhuma daga hukumomi a bijiro da maganar rashin lafiya don nema masa bail, wannan cin dunduniyar doka ne, haka kuma kashe goben ƙasa ne.

Idan akwai tuhuma a kan El-Rufa’i, abin da ya dace shi ne ya fuskanci shari’a k**ar kowane ɗan ƙasa. Babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma babu wanda ya k**ata a ba shi kariya ta siyasa domin guje wa bincike ko tuhuma. Adalci ba ya aiki da barazana ko tausayi, yana aiki ne da gaskiya da hujja.

Lokaci ya yi da za a daina amfani da lafiyar mutum a matsayin garkuwa ta tserewa fuskantar tuhuma a gaban kuliya manta sabo. Najeriya za ta samu ci gaba ne kawai idan muka yarda cewa kowa babba ko ƙarami dole ya amsa idan an tuhume shi. Doka ta fi kowa, kuma dole ta yi aiki akan kowa.

A cikin hotunan nan dake kasa za ku ga yadda yan siyasa ke rainawa mutane hankali a duk lokacin da suke fuskantar tuhuma daga hukumomi a kasar nan.

Sa hannun
Mustapha Basiru
Shugaban Nigerian Unite

Ƙungiyoyin Matasa Daga Jihar Kaduna Sun Yi Kira Ga EFCC Da Su Binciki Elrufa'i Haɗakar ƙungiyoyin matasa daga jihar Kadu...
16/02/2026

Ƙungiyoyin Matasa Daga Jihar Kaduna Sun Yi Kira Ga EFCC Da Su Binciki Elrufa'i

Haɗakar ƙungiyoyin matasa daga jihar Kaduna sun yi ƙawanya a hukumar EFCC yau yayin da tsohon gwamnan jihar ke karɓar gayyatar da hukumar tayi masa kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa.

Matasan sun bayyana cewa, ya zama wajibi tsohon gwamnan ya tsaya ya fuskanci tuhume-tuhumen da ake masa, kar ya mayar da abun siyasa, domin babu wanda yafi karfin bincike idan ana tuhumarsa.

Matasan sun jaddadawa EFCC cewa, dole a gudanar da bincike mai zurfi akansa, idan har ba shi da laifi su sallameshi, amma idan aka sameshi da laifi to a hukunta shi k**ar yadda hukumar take hukunta kowa.

Daga Muhammad Abdullahi
Shugaban kungiyoyin matasan jihar Kaduna

Kogunan Gusau Shine Amsa A Jihar Zamfara 2027A yau Jihar Zamfara na bukatar shugaba nagari, mai hangen nesa, mai tausayi...
09/02/2026

Kogunan Gusau Shine Amsa A Jihar Zamfara 2027

A yau Jihar Zamfara na bukatar shugaba nagari, mai hangen nesa, mai tausayi ga talaka, kuma wanda ya san halin da al’umma ke ciki.

Ba kowa ba ne zai iya ɗaukar wannan nauyi, sai mutumin da Allah ya horewa baiwa da basira, kwarewa, da kuma kishin jama’a. Daga cikin irin wadannan mutane, sunan Kogunan Gusau ya fito fili ba tare da shakka ba.

Kogunan Gusau mutum ne da ya shahara wajen taimakon jama’a, gina al'umma, da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun al’umma. Tarihinsa ya nuna cewa shi shugaba ne mai sauraron jama’a, wanda ke da fahimtar matsalolin tsaro, tattalin arziki, ilimi da walwalar al’umma. Ba wai kawai a iya magana ya tsaya ba, faɗa da aikatawa sunanshi.

A tsawon lokaci, Kogunan Gusau ya nuna jajircewa, hakuri da kwarewa a harkokin shugabanci da siyasa. Yana da fahimta mai zurfi game da jihar Zamfara daga karkara zuwa birane, kuma yana da zuciyar haɗa kan jama’a ba tare da nuna bambanci ba. Wannan shi ne irin shugabancin da Zamfara ke nema a wannan lokaci mai muhimmanci.

Muna kira gare ka, Kogunan Gusau, da ka amsa kiran al’umma. Ka tsaya ka fafata domin karɓar kujerar Gwamnan Jihar Zamfara a 2027 insha Allahu, domin mutane da dama sun yarda kai ne mutumin da ya dace da wannan aiki.

Zamfara na bukatar shugaba mai tsoron Allah, gaskiya, hangen nesa da kuma karfin gwiwar kawo sauyi, kuma wadannan siffofi suna tare da kai.

Allah Ya taimaka, Ya ba da nasara, kuma Ya sanya abin da ya fi alheri ga Jihar Zamfara da al’ummarta.

An Jaddada Jagoranci Nagari Da Yaƙi Da Shan Miyagun Ƙwayoyi a Babban Taron Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya "CNG" a...
16/01/2026

An Jaddada Jagoranci Nagari Da Yaƙi Da Shan Miyagun Ƙwayoyi a Babban Taron Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya "CNG" a Sakkwato

Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ɓangaren ɗalibai ta samu gagarumar nasara wajen shirya laccar bai ɗaya da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato.

An gudanar da laccar ne ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba HRH Farfesa Sambo Wali Junaid (Wazirin Sakkwato), inda manyan masu jawabi s**a yi jawabai masu armashi kan batutuwa masu muhimmanci da s**a shafi kyakkyawan jagoranci nagari, illolin shan miyagun kwayoyi, da kuma mummunan tasirin "Hate speech" a makarantun gaba da sakandare da ma al’umma baki ɗaya.

Taron ya samu halartar ɗalibai masu yawa daga fannoni daban-daban, abin da ke nuna yadda matasa ke da ƙwazo da sha’awar rungumar kyawawan ɗabi’u, haɗin kai da jagoranci nagari.

Hakika, laccar ta ilmantarwa ta kuma yi tasiri sosai, inda ta haɗa zukatan matasa masu burin gina kyakkyawar makoma mai ɗorewa da ci gaban al’umma.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa For Asiwaju posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Arewa For Asiwaju:

Share