22/10/2021
*GIDA DUBU YOUTH FORUM DUTSE*
21-10-2024
_GIDA DUBU YADI SECURITY PATROL AND GUARD_
*Assalamu Alaikum*
```Yau kusan sati uku (3) kenan da kafah qungiyar sintiri a unguwar gida dubu,maqasudin kafa wannan qungiya shine don a dinga saka idanu da kuma kawo qarshe aikata wasu dabi'u da basu kamata su dinga faruwa ba a wannan unguwa ta gida dubu. Kwamitin dattawa na wannan unguwa da kuma qungiyar matasa ta wannan unguwa sunyi iya bakin iyawar su don ganin wannan abu ya tabbata,kuma alhamdulillahi aka samu hadin kai daga dukkan mazauna unguwar gida dubu dama wanda su rabarta.
Alhamdulillah bayan fara wannan aiki na sintiri wanda da daddare yafi qarfi inda ake farawa daga 12:00am (Na dare) zuwa 5:000am (Na asuba) shige da fice yana tsayawa cak a cikin wannan unguwa a tsakankanin wannan lokaci idan ba tare da wani dalili karbabbe ba. Al'ummar wannan unguwa sheda ne tunda aka fara gudanar da wannan aiki an samu canji sosae wajen tabbatuwar tsaro a cikin wannan unguwa wanda kuma ba qaramar nasara ba ce da endai aka dore da hakan sai unguwar gida dubu ta zama ta daban, sai mun zama abin kwatance da koyi ga sauran unguwanni insha Allahu
Babu abin daya kamata a yanzu illah mu taya masu gudanar da wannan aiki da addu'a,sannan aci gaba da basu hadin kai yadda ya kamata da kuma gudumawa ta kowane fanni. Domin sun sadaukar da kansu,lokacin su, da duk wata wal walar su suna qoqarin kare mana unguwa,dukiyoyi harma da rayuka a yayin da da kowa yake shan baccin sa. Allah ya saka musu da mafificin alkhairi, Allah ya kare mu ya kuma tsare mu daga dukkan wani sharri ameen.
A qarshe zanyi amfani da wannan dama kamar yadda ake ta sanarwa a masallatan mu cewa yan sintirin nan namu suna amfani da kayayyakin aiki kamar su UNIFORM, TOCH LIGHT, GORA, WHISTLE, DORINA, Etc. Wanda wadannan kaya ana da qarancin su qwarai da gaske..Wannan tasa ake ta sake neman taimako dai daga al'umma duk wanda yake da halin taimakawa da daya daga cikin wadannn