15/01/2023
Na fi gamsuwa da alkalancin Dr. Marzuq Ungogo
Muhawarar ‘Yan Takarar Gwamnan Kano: Fashin Ba’ki
Marzuq Ungogo, PhD
Muhawarar ‘yan Takarar Gwamnan Kano da BBC Hausa ta shirya kuma ta gabatar a yau ta mutu’kar ‘kayatar. Kwalliya ta biya ku’din sabulu domin muhawarar ta haska mana kowanne ‘dan takara, kaifin basirarsa, shirye-shirye da iya magana. Ga nawa fashin baqin.
1. Sha’aban Shara’da ya nuna bajintar fahimtar matsalolin al’umma da kuma kaifin basirar fito da hanyar gyara. Tabbas zaman Sha’aban a Abuja, gwagwarmayar da ya yi a Kano, da kuma ‘kasashen kewaye da ya zagaya ba su zube a banza ba.
2. Salihu Tanko Yakasai: shi ma ya nuna karsashi irin na Sha’aban, wajen fitar da al’kalumma da zayyana hanyoyin gyara na zamani. Sai dai kuma kash.…. Sha’aban ya yi masa fintinkau.
3. Muhammad Abacha: Biyun ‘daya, ko dai Abacha bai kai sauran ‘yan takara shiri ba ko kuma bai kai su hikimar zance ba. Abacha bai nuna wata bajinta ba wajen fahimtar matsalar talakan Kano ba, bai nuna sanin makamar aiki ba, sannan bai nuna karsashi ba.
4. Abba Kabir Yusuf: Abba ya nuna sanin makamar aiki sai dai duk aikin da ya bayyana zai yi to ba sabon abu ba ne. Abba maganarsa yawanci a kan ci gaba da ‘ko’karin Kwankwaso ne. Abba ya ci alwashin da’kile rashawa. Abba ya tafka kuskuren barin muhawara ana cikin yi. Tabbas uzurinsa a Kaduna bai kai muhawarar nan muhimmanci ba.
5. Nasir Gawuna: Ya fi kowa nuna sanin gwamnati, matsaloli da hanyoyin da an gwada su ba su ‘bulle ba. Abun mamaki sauran ‘yan takara idan s**a ce za su yi abu, Gawuna sai ya ce ai sun gwada hakan tuntuni. Gawuna dai ya nuna zai ci gaba da aiyuka ma su kyau gwamnonin Kano guda uku da s**a gabata musamman ma Ganduje. Ya kuma jaddada zai gyara kura-kuren gwamnatocin baya tun da ya sansu.
‘Dauraya
1. A ‘kwarewa da cancanta, Gawuna ya fi Abba. Sai dai ba wani abun birgewa ba ne ya yi ta maimaita zai ci gaba da aiki ko salon Ganduje.
2. Matsalar Abba dogaro da yawa a kan Kwankwaso. Tambayar shine idan s**ai fa’da, ya za a yi?
3. Sha’aban na da duk abin da Salihu Tanko ke da shi. Amman Salihu shi kuma ya gaza Sha’aban.
4. Muhammad Abacha bai shirya ba.
Daga ‘karshe:
Mutane za su yi iya shahada su zabi Gawuna ko Abba. Ba dole su cika alqawarin ci gaba da aikin Kwankwaso ko Ganduje ba kamar yadda s**ai alqawari. Sai dai duk su biyun su na da nagarta da kishin Kano. Akwai alamun za su yiwa al’umma aiki.
Duk wanda ya ci za’be ya kirawo Sha’aban da ‘Dawisu su taimake su wajen aiki. Abacha ya je ya ci gaba da kasuwancinsa da taimakon al’umma.