Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group

  • Home
  • Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group

Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group Official Page Of Abba Ka Cika Gwarzo 4+4
In Sha Allah Kano Political Support Group

✊✊✊
18/05/2026

✊✊✊

🔥 Kaitsaye daga Ƙaramar Hukumar Rano wajen ƙaddamar da takarar Sen.SSen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D yayin da Mai Girma G...
18/05/2026

🔥 Kaitsaye daga Ƙaramar Hukumar Rano wajen ƙaddamar da takarar Sen.SSen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D yayin da Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya halarta domin nuna goyon baya da haɗin kai.

Al’umma sun fito domin nuna ƙauna da biyayya ga shugabanci nagari. Muna addu’a Allah Ya sanya ayi taro lafiya, a tashi lafiya, Ya kuma ba da nasara baki ɗaya. 🤲👏

First Lady ta Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Maryam Abba Kabir Yusuf, tare da First Lady ta Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, H...
18/05/2026

First Lady ta Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Maryam Abba Kabir Yusuf, tare da First Lady ta Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Hafsat Murtala Sule Garo, mata ne masu daraja, natsuwa da kishin cigaban al’umma.

Hakika suna nuna ƙoƙari da jajircewa wajen ganin Jihar Kano ta samu cigaba mai ɗorewa, musamman ta fuskar walwala, haɗin kai da tallafawa al’umma.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su nasara a dukkan lamuransu, Ya ƙara musu lafiya, hikima da albarka wajen gudanar da ayyukan alheri. Amin.

18/05/2026

Hon. Engr. Sagir Ibrahim Koki 🙌💔🙌

Abba Kabir Yusuf 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group 🙌💔🙌
18/05/2026

Abba Kabir Yusuf 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group 🙌💔🙌

Shugabancin kungiyar: Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group ya gudanar da zama na musamman ...
17/05/2026

Shugabancin kungiyar: Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group ya gudanar da zama na musamman domin tattauna shirye-shiryen babban taron kungiyar mai taken:

“Abba Ka Cika Gwarzo 10K Members Mega Rally”

In Shaa Allah, za a gudanar da wannan gagarumin taro bayan Babbar Sallah, inda kungiyar za ta hada dubban magoya: baya domin nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin Mai Girma Gwamnan Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf.

Haka kuma, kungiyar ta fara shimfiɗa harsashi tare da tsara dabarun neman kuri’u miliyan 2 domin tabbatar da nasarar Mai Girma Gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Kungiyar ta jaddada aniyarta ta cigaba da wayar da kai, hada kan matasa da al’umma, tare da kara karfafa goyon baya daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Allah ya taimaki Mai Girma Gwamna
Allah ya tabbatar da nasara
Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah ✊

All Progressives Congress Ta Tabbatar da Abubakar Kabir Abubakar a Matsayin Ɗan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai ta Bic...
17/05/2026

All Progressives Congress Ta Tabbatar da Abubakar Kabir Abubakar a Matsayin Ɗan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai ta Bichi

Honarabul Abubakar Kabir Abubakar ya zama zaɓaɓɓen ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) guda ɗaya tilo domin neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Bichi Federal Constituency a zaɓen shekarar 2027.

A ranar Asabar, 17 ga Mayu, 2026, jam’iyyar APC ta fara gudanar da zaɓukan fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Wakilai a faɗin ƙasar nan, inda Hon. Abubakar Kabir Abubakar ya samu nasara bayan shugabannin jam’iyyar APC na dukkanin wards 11 na Bichi Federal Constituency s**a amince da shi a matsayin ɗan takara ba tare da hamayya ba.

Da yake jawabi yayin taron tabbatarwar, Bola Ahmed Tinubu wanda wakilinsa shi ne mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana wakilcin Abba Bichi a matsayin mai kusanci da al’umma, mai sauraron jama’a tare da kawo ayyukan ci gaba, musamman ayyukan mazabu da shirye-shiryen tallafawa matasa.

Masari ya bayyana cewa duk da APC na gudanar da zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasa, mazabar Bichi tana daga cikin wuraren da s**a fi jan hankali saboda ayyukan ci gaba da kuma kyakkyawar alaƙar da ɗan majalisar ke da ita da al’umma.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan APC ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf; Hon. Sada Soli mai wakiltar mazabar Jibia/Kaita; da Ministan Gidaje da Raya Birane, Engr. Mu’azu Rabi’u Darma, tare da sauran shugabannin jam’iyya.

Sauran waɗanda s**a halarta sun haɗa da Manajan Darakta na Hadejia Jama’are River Basin Development Authority, Rabiu Suleiman Bichi; tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi; Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi; shugabannin mata; shugabannin matasa; da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Kano.

A jawabinsa, Abba Kabir Yusuf ya yaba da irin wakilcin da Hon. Abubakar Kabir Abubakar ke yi tun bayan zaɓensa zuwa Majalisar Wakilai a shekarar 2019.

“Ina yaba wa Hon. Abubakar Kabir Abubakar bisa kyakkyawan wakilci da yake yi. Tun daga shekarar 2023 nake addu’ar samun damar yin aiki tare da shi domin cigaban Bichi da Jihar Kano,” in ji Gwamna Yusuf.

Ya kuma bayyana ayyukan mazabarsa a matsayin abin a yaba, musamman a bangaren tallafawa matasa da ayyukan ci gaban al’umma.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Bichi da su sake zaɓen Abubakar Kabir Abubakar a zaɓen 2027, yana mai bayyana ƙwarewarsa da jajircewarsa wajen hidimtawa jama’a.

Tun da farko a jawabinsa, Abubakar Kabir Abubakar ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa samun damar zama ɗan takarar APC na mazabar Bichi, tare da alƙawarin ci gaba da aiki domin ci gaban al’ummar mazabar idan aka sake zaɓensa a 2027.

Abubakar Kabir, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, ya sake jaddada ƙudirinsa na cigaban Ƙaramar Hukumar Bichi.

Ya kuma yaba wa Bola Ahmed Tinubu bisa ayyukan manyan tituna da ake gudanarwa a Arewacin Najeriya da Jihar Kano, ciki har da aikin hanyar Kano–Daura, Abuja–Kaduna–Kano, da Kano–Maiduguri.

Har ila yau, ya yaba da shirin aikin layin dogo na Kano Metropolitan Rail Service na naira tiriliyan ɗaya, wanda ake sa ran zai inganta sufuri, bunƙasa tattalin arziki da rage cunkoson ababen hawa a birnin Kano.

Hon. Abubakar Kabir Abubakar ya tabbatar da cewa al’ummar Ƙaramar Hukumar Bichi, mai sama da masu kaɗa ƙuri’a 300,000, za su ci gaba da mara wa Bola Ahmed Tinubu da APC baya domin samun nasara a zaɓen 2027.

KAI TSAYE DAGA TARAUNI ✌️💙Kai tsaye daga Ofishin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Karamar Hukumar Tarauni ya...
16/05/2026

KAI TSAYE DAGA TARAUNI ✌️💙

Kai tsaye daga Ofishin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Karamar Hukumar Tarauni yayin gagarumin taron tabbatar da Hon. Nasiru Ja’o’ji a matsayin wanda zai wakilci Jam’iyyar APC domin neman Kujerar Majalisar Tarayya a zaben 2027.

Taron ya gudana cikin lumana da hadin kai, inda dukkan ‘yan takara, shugabanni da masu ruwa da tsaki s**a bayyana cikakkiyar amincewa da goyon baya ga Hon. Nasiru Ja’o’ji domin cigaban al’ummar Tarauni.

Haka zalika, taron ya samu halartar wakilan Independent National Electoral Commission (INEC) domin shaida da tabbatar da sahihancin zaman kamar yadda doka ta tanada.

Muna addu’ar Allah SWT Ya bada nasara, Ya sanya alheri, zaman lafiya da cigaba mai dorewa ga Jam’iyyar APC da daukacin al’ummar Karamar Hukumar Tarauni baki daya. 💪🗳️🔥

KIRU/ BEBEJI SAI MALIYA 🥰💕✌️Kai tsaye daga Garin Kiru, inda aka gudanar da gagarumin taron tabbatar da Hon. Abdulmumin J...
16/05/2026

KIRU/ BEBEJI SAI MALIYA 🥰💕✌️

Kai tsaye daga Garin Kiru, inda aka gudanar da gagarumin taron tabbatar da Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa a matsayin wanda zai wakilci Kananan Hukumomin Kiru/Bebeji domin neman Kujerar Majalisar Tarayya karkashin tutar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Taron ya samu halartar dubban magoya baya, shugabannin jam’iyya, matasa da dattawan yankin, inda aka nuna cikakken goyon baya da amincewa ga jagorancin Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa.

Al’umma sun bayyana cewa sun gamsu da irin ayyukan ci gaba da wakilci nagari da Hon. Kofa yake yi, tare da bayyana shi a matsayin zabin al’umma domin cigaban Kiru/Bebeji.

Allah ya bada nasara, ya tabbatar da alheri ga jiharmu da kasa baki daya. APC sai nasara! 💪🔥

AlhamdulillahKai tsaye daga Bichi yayin taron tabbatar da ɗan takarar Majalisar Tarayya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bi...
16/05/2026

Alhamdulillah

Kai tsaye daga Bichi yayin taron tabbatar da ɗan takarar Majalisar Tarayya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, a matsayin wanda dukkan ‘yan takara da jagororin Jam’iyya s**a amince ya wakilci All Progressives Congress a zaɓen shekarar 2027.

Taron ya samu halartar wakilan Independent National Electoral Commission domin shaida tare da tabbatar da sahihancin zaman cikin lumana da adalci.

Muna roƙon Allah SWT Ya ba mu nasara, Ya sanya alheri, haɗin kai da cigaba ga Jam’iyyar APC da al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Address

Zoo Road

700001.

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba Ka Cika Gwarzo 4+4 In Shaa Allah Kano Political Support Group posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your organization to be the top-listed Government Service?

Share