03/05/2026
An kammala cika fom din Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi na takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi karo na biyu a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar APC.
A yau Asabar, Maigirma Shugaban Jam'iyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Mohammed Kana Zuru (Ganuwan Zuru) da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Mohammed BK (Dujiman Gwandu) sun jagoranci cika fom ɗin Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) wanda aka fara jiya Juma'a kuma aka kammala yau Asabar 02/05/2026.
An samu wakilci na kowace Mazaɓa daga Mazaɓu 225.
Muna fatar ALLAH ya baiwa Maigirma Gwamna Nasara
✌️✌️✌️✌️✅️✅️✅️✅️