Zadawa tafi jam'iya

Zadawa tafi jam'iya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zadawa tafi jam'iya, Political organisation, ZADAWA town, misau local Gov't area bauchi state, Zadawa.

21/03/2026
16/03/2026

Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) reshen Jihar Bauchi ta yi kira ga dukkannin ‘yan siyasa da sauran al’ummar jihar da ke da sha’awar shiga siyasa da su rungumi jam’iyyar domin bada gudunmawa wajen ci gaban jihar.

A cikin wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar na jihar Bauchi, Hon. Abdurrahman Yusuf Mu’azu (Sardaunan Boto) ya sanya wa hannu ranar 15 ga watan Maris, 2026, jam’iyyar ta bayyana cewa ƙofofinta a buɗe suke ga duk wanda ke da kyakkyawar manufa da burin kawo ci gaba ga Jihar Bauchi.

Sanarwar ta ce jam’iyyar ta kuma buɗe damar bai wa masu sha’awar tsayawa takara karkashin tikitin jam’iyyar a kowane mataki, ba tare da la’akari da mukamin da suke son nema ba, matuƙar suna da niyyar gaskiya ta kawo sauyi mai ma’ana da ci gaba ga al’umma.

Jam’iyyar ta jaddada aniyarta na kasancewa dandali mafi inganci da nagarta wajen tafiyar da manufofin da za su kawo cigaba, bunkasa tattalin arziki da kuma kyakkyawan sauyi a Jihar Bauchi.

A wani bangare na kokarin fadada damar shiga jam’iyyar, PRP ta sanar da kaddamar da wani sabon tsarin yin rajista ta yanar gizo, inda masu sha’awar shiga jam’iyyar za su iya yin rajista cikin sauƙi ta hanyar ziyartar shafin prpng.org daga duk inda suke.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan sabon tsari na zamani yana nuna kudirin jam’iyyar na inganta gaskiya, hada kai da kuma rungumar fasahar zamani a harkokin siyasa.

Jam’iyyar ta kuma mika godiyarta ga shugabannin jam’iyyar a matakin kasa, musamman Shugaban jam’iyyar na kasa, Malam Falalu Bello, bisa samar da wannan sabon tsarin da ya dace da zamani domin sauƙaƙa harkokin rajista ga ‘ya’yan jam’iyyar.

A karshe, jam’iyyar ta yi kira ga dukkan ‘yan siyasa da sauran al’ummar Jihar Bauchi da ke da sha’awar shiga siyasa da su yi amfani da wannan dama ta yin rajista tare da zama cikin sahun masu tsara makomar jihar.

Jam’iyyar ta ce hadin kai, sadaukarwa da siyasa mai nagarta su ne ginshikin gina Jihar Bauchi mai inganci.

16/03/2026

Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo sakamakon karo da wani abu a kan hanyarsa.

assalam barka da safiya
12/03/2026

assalam barka da safiya

Address

ZADAWA Town, Misau Local Gov't Area Bauchi State
Zadawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zadawa tafi jam'iya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share