PDP Digital Media Concern

PDP Digital Media Concern Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from PDP Digital Media Concern, Government Organization, Bauch state Yan doka Road, Bauchi.

LABARAI KAN RIKICIN PDP DA RAWAR INECMuna son jawo hankalin ‘yan Najeriya kan wasu abubuwa masu tayar da hankali da wasu...
22/03/2026

LABARAI KAN RIKICIN PDP DA RAWAR INEC

Muna son jawo hankalin ‘yan Najeriya kan wasu abubuwa masu tayar da hankali da wasu ‘yan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da ke nuna rashin haɗin kai suke aikatawa, waɗanda ake zargin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) kuma abokin hulɗar Bola Ahmed Tinubu ne ke jagoranta, domin kokarin rusa tsarin doka da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada.

Ya kamata a fayyace ba tare da wata shakka ba cewa:

Hukuncin baya-bayan nan na Kotun Ɗaukaka Ƙara (Court of Appeal) ya soke abin da ake kira taron Ibadan (Ibadan convention), tare da tabbatar da dakatarwar wasu mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (National Working Committee – NWC). Wadannan mutane, bisa doka da kundin tsarin PDP, ba su da wata hurumi ko ikon shirya ko shiga duk wata harkar jam’iyya.

Haka kuma, kotun ta ladabtar da wani lauya na PDP da aka dakatar, saboda yin aiki a madadin jam’iyyar ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke ƙara tabbatar da cewa dole ne a mutunta doka da kundin tsarin jam’iyya a kowane lokaci.

KAN SHUGABANCI DA HALALCI
Kundin tsarin PDP ya bayyana a sarari cewa:

A irin wannan yanayi, alhakin shugabanci yana hannun Kwamitin Amintattu (Board of Trustees), wanda ke karkashin jagorancin Adolphus Wabara.
Wannan kwamiti har yanzu yana nan daram, ana ganinsa a hukumance, kuma ya riga ya fara kokarin sasanta bangarori domin samar da fahimtar juna.

Saboda haka:
Babu gibin shugabanci a PDP
Babu wani dalili da zai ba da hujjar kafa wasu majalisu ko tsarin da ba su dace da doka ba

Duk wani yunkuri na kafa bangarori (factions) sabawa kundin tsarin jam’iyya ne, ba shi da inganci, kuma yana da manufar ta siyasa a ciki.

TAMBAYOYI GA INEC
Muna kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta gaggauta bayyana matsayinta a fili:

Mene ne matsayin shugabancin PDP a hukumance?

Shin ayyukan wadannan bangarori suna da sahalewa ne ko kuwa ba bisa ka’ida ba ne?

Shin INEC ta amince ko ta yi rajistar wata sabuwar jam’iyya da ke da alaka da wadannan da ke nuna rashin jin dadi?

‘Yan Najeriya na da hakkin sanin gaskiya. Yin shiru daga bangaren INEC na haifar da damuwa da kuma sanya shakku a zukatan jama’a.

SABANI A MATSAYIN INEC
Yana da muhimmanci a bayyana cewa, a shafin hukuma na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), har yanzu ana nuna shugabancin PDP na karshe da aka amince da shi a karkashin Shugaban Jam’iyya na riko, Umar Iliya Damagum.

Wannan ya haifar da tambaya mai muhimmanci:
Idan har bayanan INEC na hukuma suna nuna wannan shugabanci, me ya sa ake ganin hukumar tana sa ido ko kuma tana amincewa da ayyukan wani tsari na rikon kwarya da aka kafa ba bisa ka’ida ba?

Ba zai yiwu INEC ta rika daukar matsayi biyu a lokaci guda ba. Ba za ta iya nuna wani matsayi a hukumance, amma a aikace ta yi wani abu dabam ba.

Dole ne INEC ta kasance mai zaman kanta kuma mai adalci — ba kayan aiki na wata jam’iyya mai mulki ba.

KARIN MUHIMMIYAR TAMBAYA GA INEC
Har ila yau, muna tambayar wata muhimmiyar tambaya:
Shin yanzu INEC tana kafa wani sabon tsari ne inda duk wani dan jam’iyya da bai gamsu ba zai iya kafa bangare, ya dauki iko, sannan ya yi tsammanin INEC za ta amince da shi ko ta kula da ayyukansa?

Idan haka ya zama al’ada, hakan na nufin ana halasta rikici tare da rusa tsarin dimokuradiyya na cikin gida na jam’iyyu.

Jam’iyyun siyasa suna tafiya ne bisa kundin tsarinsu da dokokin kasa — ba bisa bukatun kai tsaye ko ra’ayin mutum daya ba. Bai kamata INEC ta haifar ko ta karfafa yanayi da zai sa saba doka ya zama abin da aka saba ba.

SAKON KARSHEN DA YA KE DA KARFI
INEC dole ta fito fili:
Ba za ta halasta abin da ba bisa ka’ida ba a yau, sannan ta ce tana kare dimokuradiyya gobe ba.

KIRA GA SAURAN JAM’IYYUN SIYASA
Muna kira ga sauran jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista a Najeriya da kada su yi shiru kan wannan lamari. Yin shiru a irin wannan lokaci ba nuna tsaka-tsaki ba ne — nuna goyon baya ne kai tsaye.

Yawancin wadannan jam’iyyun suna da shari’o’i a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da Babbar Kotun Tarayya. Ya kamata su fahimci cewa abin da ke faruwa ga PDP a yau, zai iya faruwa ga kowace jam’iyya gobe.

Wannan batu ba na jam’iyya daya kadai ba ne, batu ne na kare dimokuradiyya, bin doka, da mutuncin cibiyoyi.

Muna kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su tashi tsaye, su wuce bambancin ra’ayi na siyasa, su kare sararin dimokuradiyya.

Raunin jam’iyya daya, raunin dukkan jam’iyyu ne!

MATSAYINMU NA KARSHE
Muna gargadin duk wani yunkuri na kokarin raunana PDP domin biyan bukatun wasu na siyasa daga waje. ‘Yan Najeriya na kallo.

Jam’iyyar People’s Democratic Party har yanzu babbar jam’iyya ce mai karfi, kuma babu wani mataki na cin amana daga ciki ko tsoma baki daga waje da zai iya rusa tubalinta.

K. Media

Sanarwar (Communiqué) da aka fitar a ƙarshen Taron Gaggawa na Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar Peoples Democratic P...
11/03/2026

Sanarwar (Communiqué) da aka fitar a ƙarshen Taron Gaggawa na Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yau Laraba, 11 ga Maris, 2026, wanda Shugaban BoT, Adolphus Wabara, PhD, ya gabatar.

Bayan nazari mai zurfi kan dukkan batutuwan da s**a shafi shugabancin jam’iyyar PDP, musamman dangane da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da aka yanke ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026, Kwamitin Amintattu (BoT) ya gudanar da taron gaggawa na faɗa-ɗa a ranar Talata 10 da Laraba 11 ga Maris, 2026, inda aka cimma matsaya kamar haka:

1. Kwamitin Amintattu (BoT) bai amince da hukuncin Court of Appeal of Nigeria ba wanda ya soke Babban Taron Ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar daga 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025, wanda ya samar da Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki. Kwamitin na jiran shawarar lauyoyinsa kan matakin da za a ɗauka gaba.

2. BoT ya nuna damuwa matuƙa kan rikice-rikicen shugabanci na cikin gida da sabani da s**a kai ga kai ƙara a kotu, lamarin da ke haifar da illa ga haɗin kai da kuma tafiyar da jam’iyyar yadda ya kamata a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a ƙasar.

3. Duk da haka, BoT ya amince da damar da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Ibadan ta bayar domin a samu sulhu da sasanci a cikin jam’iyyar.

4. BoT ya kuma lura da sha’awa da burin mambobin jam’iyyar da ke son tsayawa takara a mukamai daban-daban a zaɓen 2027.

5. Da yake sane da cewa BoT shi ne ginshiƙin tunanin jam’iyya kuma na uku mafi girman hukuma a cikin PDP, kwamitin ya kuduri aniyar ɗaukar matakai cikin gaggawa domin sasanta duk masu ruwa da tsaki, kawo ƙarshen duk wata takaddama, tare da dawo da jam’iyyar cikin koshin lafiyar siyasa, musamman domin ta iya tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

6. BoT ya kafa Kwamitin Musamman da zai fara nan take tuntubar ƙungiyoyin lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da sulhu da sasanci a cikin jam’iyyar.

7. BoT ya yaba da goyon baya, aminci da haɗin kan ‘yan Najeriya ga jam’iyyar PDP, wanda hakan ya ƙara bayyana ta hanyar rajistar sabbin mambobi ta yanar gizo (e-registration) da ake yi a faɗin ƙasar. Rahotanni daga wurare daban-daban na nuna cewa ana samun rajistar mambobi a cikin miliyoyi a kowace rana. Wannan babban yawaitar shiga jam’iyyar duk da ƙalubalen da ake fuskanta na nuna cewa PDP har yanzu ita ce jam’iyyar da mafi yawan ‘yan Najeriya ke so gabanin zaɓen 2027.

8. Don haka BoT na kira ga dukkan shugabanni da mambobin jam’iyyar da su ajiye duk wata bukata ta kashin kai ko ta ƙungiya, su haɗu wuri guda a matsayin iyali ɗaya domin kare muradun jam’iyyar da kuma jin daɗin miliyoyin ‘yan Najeriya da suke ɗora fatansu kan PDP.

9. BoT ya yaba da ƙoƙarin gwamnonin jam’iyyar; Bala Mohammed, gwamnan Jihar Bauchi State, da kuma Seyi Makinde, gwamnan Jihar Oyo State, saboda jajircewarsu da goyon bayansu ga jam’iyyar da kuma jin daɗin ‘yan Najeriya.

10. BoT, bisa tanadin Sashe na 32 na Kundin Tsarin Mulkin PDP (wanda aka gyara a 2017), ya amince baki ɗaya da naɗin Babangida Aliyu a matsayin Sakataren Kwamitin Amintattu (BoT).

11. BoT na roƙon ‘yan Najeriya da kada su karaya ko su yanke ƙauna, su ci gaba da kasancewa da fata yayin da PDP ke aiki tuƙuru domin sake gyara kanta domin ceto ƙasar nan daga kangin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kamal Ahmad Azare
K. Media, 11/3/2026

10/03/2026

Those who laugh at supporters of the PDP should know that, if they truly understood what is happening, they would realize that these people actually deserve sympathy.

The people whom some have turned into objects of ridicule and mockery are the same people who have not given up, have not lost hope, have not grown tired, and have not surrendered to continued oppression and domination in the name of democracy.

They are the people who refused to collect money and sell out the masses just to gain personal benefits. Considering the situation Nigeria is currently facing, they are the true patriots who have stood up to fight for the sake of God, for the people, and to secure a better future for you and your children.

By the mercy of God, we have now reached a new stage. You will remember that I said the PDP will be reformed and will regain its strength to rescue you and Nigeria as a whole. And by the grace of God, we shall succeed.

K. Media

Gabanin Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan Rikicin Shugabancin PDP:Ku kwantar da hankalin kuma ku bi doka – Gwamnonin PDP g...
08/03/2026

Gabanin Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan Rikicin Shugabancin PDP:

Ku kwantar da hankalin kuma ku bi doka – Gwamnonin PDP ga Mambobi da Magoya baya a Faɗin Ƙasa

1. Ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP (PDP Governors’ Forum – PDP-GF) ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, CON, Gwamnan Jihar Bauchi, tana sanar da mambobin jam’iyyar da magoya bayanta a faɗin ƙasar nan cewa, yayin da Najeriya ke jiran hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara a ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026, dangane da rikicin shugabanci da ke cikin Jam’iyyar PDP, muna kira ga kowa da kowa da ya kasance cikin natsuwa.

2. A halin yanzu muna cikin wani muhimmin lokaci a tafiyar dimokuraɗiyyar ƙasar nan. Bangaren shari’a, a matsayinsa na mai tabbatar da adalci, yana ɗauke da babban nauyi na tabbatar da gaskiya, adalci da kuma kiyaye zaman lafiyar ƙasa. Ko wane irin hukunci kotu ta yanke, PDP tana sake jaddada girmamawarta ga tsarin shari’a tare da kudurin tabbatar da zaman lafiya.

3. Jam’iyyar PDP ta kasance ginshiƙi mai muhimmanci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya. Jam’iyyar ta taba mulki, ta kasance a matsayin ’yan adawa, kuma ta taka rawa wajen ƙarfafa cibiyoyin da ke kare haƙƙin ’yan ƙasa. Don haka muna kira ga mambobinmu, magoya bayanmu, da ma dukkan ’yan Najeriya da su kasance cikin natsuwa tare da nuna ladabi wajen martani ga hukuncin kotu. Dole ne amsarmu ta nuna martaba da cikakken girmamawa ga doka. Muna roƙon dukkan mambobi da shugabannin jam’iyya su nuna matuƙar haƙuri, natsuwa, da bin doka kafin, lokacin da bayan yanke hukuncin. Haka kuma shugabannin jam’iyyar za su gana nan da nan bayan hukuncin domin nazari da tsara matakan da za a bi bayan hukuncin.

Dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar bambancin ra’ayoyi, gasa ta tunani da kuma damar da ’yan ƙasa ke da ita na zaɓar shugabanni daga sahihan zaɓuɓɓuka. Jam’iyyar PDP za ta ci gaba da kasancewa wakiliyar waɗannan ƙimomi. Don haka muna kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da ke da burin tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 su ci gaba da yarda da ikon jam’iyyar wajen samar da sahihin dandamali da zai tabbatar da nasararsu a zaɓe. Duk da cewa INEC ta riga ta fitar da jadawalin babban zaɓen, jam’iyyar za ta tabbatar da karewa da cikar burin siyasar mambobinta.

5. Idan muka dubi zaɓen 2027, jam’iyyar PDP tana nan daram wajen kudurinta na bai wa ’yan Najeriya madadin shugabanci mai ƙarfi, nagarta, da mayar da hankali kan buƙatun jama’a. Babu wani hukunci da zai iya goge burin ’yan Najeriya na samun tsarin siyasa mai gaskiya da gasa. A shirye muke mu shiga dukkan matakan dimokuraɗiyya domin tabbatar da cewa muryar jama’a ta samu wakilci da girmamawa.

6. Bangaren shari’a ya ci gaba da kasancewa mafi zaman kansa kuma mafi kusanci da jama’a a cikin rassan gwamnati, wanda jajircewarsa wajen kare kundin tsarin mulki ya tabbatar da dorewar dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Signed:
Dr. Emmanuel Agbo FNMS MFR,
Director General,
Abuja.

Breaking!PDP Leadership, State Chairmen Convene Strategic Session Ahead of Landmark E-Registration Launch.In a decisive ...
02/03/2026

Breaking!

PDP Leadership, State Chairmen Convene Strategic Session Ahead of Landmark E-Registration Launch.

In a decisive move to modernize party operations and expand its grassroots reach in line with the new Electoral Act, the National Chairman of the Peoples Democratic Party (PDP), Kabiru Tanimu Turaki, SAN, alongside members of the National Working Committee (NWC), are currently in a high-level virtual consultative meeting with the Chairmen of the 36 State Chapters and the FCT ahead of official launch of its e-registration process.

Details later.

PRESS STATEMENTELECTORAL ACT AMENDMENT: A TREACHEROUS BETRAYAL OF NIGERIANSThe anti-democratic stance of the Senate and ...
18/02/2026

PRESS STATEMENT

ELECTORAL ACT AMENDMENT: A TREACHEROUS BETRAYAL OF NIGERIANS

The anti-democratic stance of the Senate and the sudden somersault by the House of Representatives on the amendment of the Electoral Act 2022, specifically on the mandatory electronic transmission of election results from the polling units is an act of treachery against the Nigerian electorate. This is a huge betrayal of the collective trust of Nigerians, who unambiguously expressed their overwhelming demand for the electronic transmission of results.

This betrayal is most painful because it strikes the core of democracy, electoral sanctity.
The shocking aspect of the whole drama is the brazen manner in which the legislators acted-they clearly showed disdain for the Nigerian people who voted them into office by openly challenging the supremacy of the voters. The excuses advanced for inserting this obnoxious proviso are weak, illogical, and insulting to the intelligence of Nigerians. When lawmakers begin to dilute transparency mechanisms ahead of elections, only one conclusion is rational: there is a calculated attempt to create room for electoral manipulation. By this act, the National Assembly has violated the foundation of legislative representation, which is anchored on mirroring the wishes of the majority of their constituents. This is a painful betrayal, which the people will certainly repay in equal, if not heavier measures.

Furthermore, the restriction of party primaries to Direct and Consensus methods constitutes a blatant intrusion into the internal affairs of political parties. The Supreme Court has consistently affirmed that political parties possess autonomy in managing their internal processes. This provision is therefore ultra vires, and the attempt to constrict political parties is condemnable.

Additionally, If the ruling party truly believes it enjoys the support it claims, it should welcome every mechanism that guarantees transparency. Their shameless support for this anomaly shows their fear of impending defeat in a free and fair election. It is most shameful that a party that demanded electronic voting in 2015 is now unwilling and unprepared to have electronic transmission of results-this is a crying shame.

Finally, we call on all Nigerians, the organised labour and Civil Society Organisations to use all lawful means to express their displeasure on the anti-democratic actions of our National Assembly, in the hope that they will reconsider their position. This hard-won democracy must not be allowed to suffer decline in the hands of retrogressive politicians, masking as legislators.

Signed:

Comrade Ini Ememobong, mnipr
National Publicity Secretary
Peoples Democratic Party
18022026

12/02/2026

08/02/2026
Democracy thrives on one thing: Trust. When the leadership of an electoral body begins to take sides in the internal dis...
08/02/2026

Democracy thrives on one thing: Trust. When the leadership of an electoral body begins to take sides in the internal disputes of political parties, that trust is shattered.
The current INEC Chairman’s interference isn't just a procedural error; it’s a direct threat to the independence of our institutions. To preserve the sanctity of the 2027 cycle and protect our hard-earned democratic progress, we need leadership that is beyond reproach. For the sake of the nation, the Chairman must step down”

Bauchi at 50!The PDP National Chairman, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, and other members of the party’s National Working Com...
07/02/2026

Bauchi at 50!

The PDP National Chairman, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, and other members of the party’s National Working Committee (NWC) are currently in Bauchi, Bauchi State.

The NWC members were invited to attend a lecture titled “Honoring the Past, Building the Future” as part of events marking the state’s 50th anniversary.

More details to follow...

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa halartar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP karkashin...
07/02/2026

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa halartar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Anyanwu a taron tattaunawa da jam’iyyun siyasa da aka gudanar kwanan nan ba ya nufin hukumar ta amince ko ta goyi bayan wani tsagi na musamman a cikin jam’iyyar.

Hukumar ta yi wannan karin haske ne biyo bayan cece-kuce da s**a taso kan dalilin da ya sa kwamitin Anyanwu kaɗai ya halarci taron, yayin da ɓangaren da ke karkashin Turaki bai samu wakilci ba.

Da yake amsa tambayoyi a wata hira, Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na INEC, Malam Wilfred Osilama Ifogah, ya ce hukumar ta aika gayyata ne ga jam’iyyar PDP gaba ɗaya, ba ga wata ƙungiya ko ɓangare a cikinta ba.

“Ana tura gayyata ne ga jam’iyya, ba ga mutum ɗaya ko wata ƙungiya ba,” in ji Ifogah, yana mai bayyana cewa ana aika irin waɗannan wasiƙu ne zuwa ga shugaban jam’iyya da sakatariyarta.

Ya jaddada cewa INEC ba ta da hurumin yanke shawarar wa zai wakilci jam’iyya a tarurrukanta, yana mai cewa hukumar tana karɓar duk wakilan da jam’iyya ta turo.

“Duk wanda jam’iyya ta turo wakilci, hukumar za ta karɓe shi. Domin wasiƙar gayyata ana tura ta ne ga jam’iyya, ba ga mutum ɗaya ba,” in ji shi.

Game da rashin halartar ɓangaren Turaki, Ifogah ya ƙaryata zargin cewa hakan yana nuna INEC ta amince da kwamitin Anyanwu ne kaɗai.

Yana mai jaddada cewa hukumar ba ta tsoma baki cikin rikicin cikin gida na kowace jam’iyya.
A cewarsa, a irin waɗannan tarurruka, wakilan jam’iyyun siyasa kan gabatar da kansu, inda s**an bayyana ko suna wakiltar manyan jami’an jam’iyya ne ko kuma su ne masu mukaman kai tsaye.

“Sau da yawa, za ka ji mutum ya ce yana wakiltar shugaban jam’iyya ne, ko kuma shi ne shugaban, sannan wani ya ce yana tsayawa ne a madadin sakatare,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa INEC ba ta bincike ko tantance sahihancin irin waɗannan wakilce-wakilce, muddin jam’iyya ta amsa gayyatar taron.

“Ba mu san wanda jam’iyya za ta turo ba. Jam’iyya ce kawai ke tura wakilanta,” ya jaddada.

Da yake magana kan rikicin shugabanci da ke addabar PDP, Ifogah ya bayyana cewa rikicin cikin gida ba ya cikin ayyukan INEC.

“Rikicin cikin gida ba ya damun mu. Ba mu shiga ciki. Idan sun warware matsalolinsu, mu ma za mu ci gaba da aikinmu,” in ji shi.

Sai dai ya nuna damuwa cewa irin waɗannan rikice-rikice na iya shafar shirin jam’iyya idan ba a warware su kafin manyan ayyukan zaɓe ba.

“Shawarar da muke ba jam’iyyun siyasa ita ce su warware duk wata matsala kafin ayyukan da ke da wa’adi su zo,”

A cewarsa, rashin samun shugabanci sahihi na iya hana jam’iyya shiga wasu muhimman tsare-tsare.

“Dole ne shugabancin da aka amince da shi ya sanya hannu kan takardu domin jam’iyya ta shiga tsari. Idan ba haka ba, idan lokaci ya ƙure kuma suna buƙatar wani abu, wannan matsalarsu ce,”

Ifogah ya jaddada cewa manufar tarurrukan INEC da jam’iyyun siyasa ita ce tattaunawa da haɗin kai, ba amincewa ko ƙin amincewa da wata ƙungiya ba.

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne jam’iyya ta halarta ta kuma shiga taro. Sashen Zaɓe da Kula da Jam’iyyun Siyasa ne kawai ke aika gayyata, kuma jam’iyyun s**an amsa,” in ji shi.

Address

Bauch State Yan Doka Road
Bauchi

Telephone

+2348032828654

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PDP Digital Media Concern posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to PDP Digital Media Concern:

Share