26/07/2025
HOTO MAI MAGANA
Assalamu Alaikum
nazoda bayanaina ga Al'ummar jahar niger state mussanman Zuwaga wasu Yan Barandar siyasa dawasu yan social media. Kamaida hankali akan abinda zan gayamaka kuma ka lura kamaida hankali kayiwa kanka karatu na nutsuwa da samawa kanka mafita. Katsaya ka kalli wa'annan hotunan da idon basira kafahimci kowanne uba yana gina yayansane ta hanyarda yake ganin itace mafita domin gobensa tayi kyau. Kakalla da kyau idan zasuje camping ko wajan wata hayaniya basa zuwa da yayansu saikai dabakasan ciyon kankaba ake daukarka akaika nan gobe akaika cen. Yayansu kullun suna jikinsu suna basu kariya. Idan abokanansu sukazo suyiwa yayansu kyautarda idan anbaka zai iya zama silar arzikinka. Amma sai akabarka da GARIYO DA ADDA DA WUKA - kana yawoda sanduna a hannu kamar wani makiyayi anbarka cikin jahilci da rashin aikinyi. Sunbgrkada waya kullun kana ciki kar muradunsu Anki ataimakeka domin gobenka tayi
kyau saidai kullun abaka 100k
kokasada haka da kakashe gobema ka dawo insungadama bazaka gansuba harsai bukatar anfanidakai tataso. In kakirasu sai sungadama su daga inkai rashin sa'a su haukada fada kana damunsu da kira.
Yakamata kazama mutum mai cikaken yanci kada ka yadda wani yayi amfanidakai domin cimma tasa bukatar. Kasani bakada wata muhimmanci a wajansu domin kallon
DAN BARANDAR SIYASA sukemaka kuma a haka zasu cigabada kallonka matsawar bakayiwa kanka fadaba. Basai kamaida kanka dan Dababar siyasa zaka samu abinciba. Nunamusu kaima dane kamar yadda suke kallon yayansu saikafi mutunci a wajansu.
Tambayarda zakayiwa kanka meyasa basa barin yayansu suna cuďanya daku?
Meyasa basa yawon camping da yayansu?
Meyasa basasa yayansu a makarantarda yayanka suke dukda sunki gyara makarantuda yayanka suke?
Duk wannan abune da yakamata kamaida hankali kayiwa kanka tinani.
Wannan shawarace zuwa gareka inka dauka ya amfaneka inkaki kuma wannan ya rage naka.
Sannan kaikuma mai zagi ko zargi nanma ya rage naka ba abinda zagi zai rageni dashi kaikuma ba baunda zai karama. Kaikasan gaskiya na gayama domin zuciyarka tasan gaskiya saidai ka bijiremata sabuda son zuciya.
A karshe inama kowa fatan Alkhairi Allah ya hadamuda masu kaunarmu masuson cigabanmu a rayuwa ba sumaidamu used a dumped ba kamar yadda yan siyasa suke.
Allah yasadamuda dukkanin Alkhairi Aameen Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalali walikram
Ibrahim Muhammad
Dan Malam