20/12/2025
Tsakaninmu da Bafarawa.
Ku aje siyasa a gefe, hakika Mai girma Tsohon gwamna jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto) ya cancanci samun ragowa da mutuntawa, ba sai ya shiga wata jam'iyya ko alakanta kansa da wasu yan siyasa ba.
Ya kasance a tun tashin sa, yana yiwa addinin Musulunci da al'umma hidima, bayar da goyon bayansa ga taimako da yada ababen alheri ga dorewa zaman lafiya da ci gaban kasa ba jahar sokoto kadai ba.
Mafi rinjayen wadanda suke rubutu na cin fuska ko batanci da shagube akan wannan shugaba, Bawan Allah idan sun koma gida zasu tarar uwayen su ko yan uwansu ko masu gidajen su duk mafi rinjaye sun ci amfanin Bafarawa a bangare dabam dabam na rayuwa kamin abin da yake faruwa a yau.
Uwayen nasu sun amfana da arzikinsa da taimakonsa ta hanyoyi iri iri kamin su kai matsayin da suke a bisa yau, koma na wadanda suke yiwa fadanci.
Ko shakka babu, Bafarawa ya taka muhimmiyar rawa da aiki ga baiwa jahar Sokoto alkibla, daraja ta tarbiyya addini da ilmin zamani, daukaka a fannoni iri iri kamin da bayan mulkinsa.
Yayi mulki a cikin natsuwa, ci gaba da tarbiyya ga samarwa jahar Sokoto makoma mai amfani da habaka zamantakewa da inganta rayuwa tun daga 1999 zuwa 2007.
Kashi 90% bisa dari na wadanda s**a rika mukamai ko zama wata tsiya a cikin tafiyar siyasa a jahar Sokoto daga koyarwarsa da taimakonsa ne.
Don haka, wadanda ke ganin yin butulci ga taimako da kauda ido garesa, har wasu yan yaran social media na gidajensu, yaran da basu kammala balaga da sanin ciwon kansu ba; suke cin zarafin akansa, hakika basu yiwa al'umma adalci da godiya ba.
Ra'ayin siyasa ko goyon baya, kacokan yana ga mutum ne akan abin da ya dauka ko yake so; Mai girma Attahiru Bafarawa a farko da inda aka fito Allah Ya bashi lamuni da mafi rinjaye na dukkan wadanda suke tinkaho da zama wata tsiya a Sokoto da Zamfara; tabbata daga gidan siyasa sa da kokarinsa s**a fito har yau suke wani abu a cikin al'umma.
Babu wani shugaba mai hankali da mutunci da zai yarda yaransa na kushe da cin zarafin wani dattijo ko babban mutum saboda banbancin ra'ayin siyasa , sai fa idan ya koma DATTIJON WUKARI
Don haka, yin shagube, ko tsokana ko cin zarafi ga na taking Tsohon gwamna jahar Sokoto, Garkuwan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa tamkar cin mutunci jahar Sakkwato ne da al'ummarta, kasance wani Uba, Kaka, kuma jagora ga dukkan wani mai bugun gaba dan siyasa ne a Sokoto a yau.
Gidan Bafarawa a siyasa, tankard Makaranta ce ta Firamare inda anan aka fara Kyenkyeshe kowane anhu da minhu kamin ya samu admission na ci gaba da karatun tsayi da kafarsa har yayi nasa.
Don haka tsakaninmu da Bafarawa sai addu'a da yi masa fatan alheri na makoma tagari a gobe, sakamakon irin tafarki da tsarin da yabi na aza jahar Sakkwato da siyasa Sakkwato a lokacin da yake da dama bisa sadaukarwa, zaman lafiya, ci gaba, da'a, mutunci, alheri, amfani, tarbiyya da gaskiya.
Duk mafi rinjaye na wanda yake hankoron wata tsiya ne a yau; ga jahar Sokoto daga gidansa yayi baranta, yayi koyo ya karbi taimakonsa har ya zama abin da ake baiyana sa a yau.
Tarbiyarsa, karantarwasa da taimakonsa sun baiwa Sokoto da Sakkwatawa daraja da kima da dauka ka tun daga 1999 zuwa abin da ake Kwatance na soyayya.
Matasa su daina komawa yan kore, ko makamin cin zarafi da wulakanta wasu saboda cimma burin wasu dabam.
Allah Yayi mana mafita ya agaje mu ga shiga tarkon 'yan hawu!
- Yusuf Dingyadi
Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
20th December, 2025