07/09/2026
SOBA TA KARƁI SHIRIN DUBA MARASA LAFIYA DA TIYATA KYAUTA.
Al’umma mai lafiya itace ginshiƙin cigaba. A saboda haka, ƙaddamar da shirin duba marasa lafiya da yin tiyata kyauta a Ƙaramar Hukumar Soba, babban abin farin ciki ne, musamman ga marasa galihu da waɗanda ke fuskantar ƙalubalen kuɗin samun ingantacciyar kulawar lafiya.
Shirin, wanda Uba Sani Engagement and Sensitization Forum (USESF) ta shirya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Adamu Sani, zai taimaka wajen kusantar da kulawar lafiya ga jama’a, tare da ba mutane damar samun magani da tiyatar da suke buƙata ba tare da nauyin kuɗaɗen asibiti ya hana su ba.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Soba, Hon. Muhammad Shehu Molash, ya bayyana matuƙar farin cikinsa da wannan shiri, tare da yabawa jagororin USESF bisa wannan kyakkyawan tunani da sadaukarwar da s**a yi wajen tallafawa al’umma. Ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin ƙaramar hukumar ga duk wani shiri da zai kawo sauƙi da inganta rayuwar jama’a.
Hon. Molash ya kuma miƙa godiya da jinjina ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa yadda gwamnatinsa ke ƙara faɗaɗa ayyuka da shirye-shirye zuwa ga jama’a a fannoni daban-daban, musamman harkokin kiwon lafiya. Ya bayyana cewa irin wannan himma na nuna ƙudirin gwamnati na tabbatar da jin daɗin al’umma.
Wannan mataki ya sake bayyana irin tsantsar goyon bayan Hon. Muhammad Shehu Molash ga manufofi da tsare-tsaren gwamnatin Sanata Uba Sani, tare da ƙudirin ci gaba da haɗa hannu da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin al’ummar Soba sun ci gaba da amfana da ayyukan cigaba.
Haka kuma, Hon. Molash na cigaba da ƙoƙarinsa wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da jagoranci a Soba, tare da yin aiki domin ganin APC ta samu cikakkiyar nasara a dukkan kujerun da take takara a Ƙaramar Hukumar Soba.
7 ga Satumba, 2026