LAYIN ZOMO MEDIA FORUM

LAYIN ZOMO MEDIA FORUM LAYIN ZOMO MEDIA FORUM
Was created to serve as way of delivering information concerning the layin zomo area of Sabon gari local government, kaduna state

STILL ON THE MATTER OF LAYIN ZOMOJARIDAR AMANAHome About Us Contact UsHome Labarai Ya kamata a tuna damu cewar matasan L...
28/09/2022

STILL ON THE MATTER OF LAYIN ZOMO

JARIDAR AMANA
Home

About Us

Contact Us
Home Labarai

Ya kamata a tuna damu cewar matasan Layin Zomo

Jaridar Amana September 23, 2022

Daga Umar Idris Kaduna

Da safiyar ranar Talata ne kungiyar ci gaban Layin zomo dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna s**a koka akan yadda garin nasu ya zama abin kyama ga yan siyasa bayan sun basu kuru'unsu a lokutan zabe.

Wakiliyarmu ta ziyarci Anguwar yayin da yan anguwar s**a baiwa manema labarai goron gayyatar gani da ido a wannan yankin

Yayan kungiyan ta bakin shugaban su malam Danjuma Bawa sun bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani abin da zasu iya nunawa a matsayin romon Kamakuradiyya a halin yanzu.

Shugaban yace duk wani aikin da aka gani a yanzu to aikine da gwamnatin PDP a lokacin baya.

Tuni yayan kungiyar s**a koka bisa irin kokarin da s**ayi a wannan gwamnatin ta APC kafin hawanta karagar mulki.

Yayan kungiyar wanda galibinsu matasane masu jini ajika sun baiyana cewa yanzu haka akwai hanyoyi da s**a lalace a tsakiyar garin Layin Zomon amma babu wani dan siyasa da ya taba zuwa domin kawo masu tallfin gyarawa.

Haka zalika matasa sunce yanzu haka kadar da ta hada garin Falladan da Layin Zomo itama ta lalace gaba daya.

Yayan kungiyar sun bayar da misali da makarantar UPE na Layin Zomon cewa yanzu haka Awaki ne ke kwana a ciki sakamakon yadda ta lalace.

Sun kawo maganar Asibitin su dake anguwar tasu shima sun koka da cewa ba kayan aiki ba magani da sauran abubuwan da asibiti ke bukata.

Karshe matasan sun nemi alfarma ga dukkan masu fada aji na karamar hukumar ta Sabon gari da suyi wa Allah da Annabinsa su sa hannu akan halin da garin yake ciki a halin yanzu.

Kuma sunyi kira ga Dan majalisar taraiya Honorabul Garba Datti Babawo da ya waiwayi matasan yankin Layin Zomo a shirinsa daya saba gudanarwa lokaci bayan lokaci kamar yadda yake waiwayan sauran takwarorinsu dake fadin karamar hukumar ta Sabon Garin baki daya.

Malam Muhammad Mudassir shene sakataren kungiyar ta ci gaban Layin Zomon shima cewa yayi ya kamata yan siyasan karama hukumar Sabon Gari su gane cewa Layin Zomo ba abin yardawa bace domin sunada kuri'u masu yawa da yawansu na taka rawar gani sosai lokacin zabe bisa haka ne yace suna sane da duk wanda ya taimaki yankin su

Suma idan lokaci yayi suma zasu taimaka mashi da ikon Allah

Malam Zakari Sani tsohon shugaban Yan bangan Layin Zomo shiko cewa yayi gaskiya bai kamata ace sai dai jama'ar Layin Zomo suga ana yin wasu aiyuka a wasu yanki su kuma suna gani.

Bisa haka yayi kira ga shugaban karamar hukuma da yan majalisarsu da suyi abin da ya kamata a wannan anguwa don haka ne zai karawa jambiyar APC farin jini tare da samun nasara a nan gaban.

Karshe suyin fatan Allah ya kawo wanda zai share masu hawayensu ba tare da wani matsalaba.

Created By Blog | Distributed By Jaridar Amana

Don Allah wai me LAYIN ZOMO tayi ne aka maida ita saniyar ware a gundumar BASAWA bawani abu na cigabaSani Jibril Chikaji...
19/09/2022

Don Allah wai me LAYIN ZOMO tayi ne aka maida ita saniyar ware a gundumar BASAWA bawani abu na cigaba
Sani Jibril Chikaji , Auwal mebege chikaji, Hon Hudu Dufa-dufa ,Hon.Hudu Hon Hudu Dufa-dufa Tafarki
Don Allah ku isar da koke na wajen .
Hon. Garba Datti Babawo da Engr. Muhammad Usman Maku.
Dafatan koke na zaikai wajen da Yakamata.

08/04/2022

Allah ya amshi ibadinmu
Ya samu cikin bayinsa dazai Gafara, rahama da kuma yanci da ga wuta

01/04/2022

Allah yabamu zaman lafiya
A ƙasar mu
Jihar mu
Karamar Hukumar mu
Anguwar mu Layinzomo

Allah ya kyauta makwanci yasa aljanna makoma da sauran mamata mu ya sa inna mu tazo mucika da imani
14/06/2021

Allah ya kyauta makwanci yasa aljanna makoma da sauran mamata mu ya sa inna mu tazo mucika da imani

14/06/2021

Fatan alheri ga daukacin jama ar layin Zomo
Allah yasada mu da alherensa
Yahada kanmu
✍️ Muhammad Mudassir

30/01/2021

ABIN BAIYI DAƊI BA
Zaman lafiya yafi komai daɗi mutan layin Zomo mudunga kai zuciya nesa don in ansan farko fitina qarshen ta ba lailai bane yazamo a sani
Kira ga Yara matasa muyi qoqarin tafiyar da quruciyarmu ta hanyar da ya dace saboda inyau matashi ne kai gobe zaka zama mai gida ko dattijo baza kaso ai maka abinda kayi ba mara kyau don haka wasanni dazasu jawo mana cecekuce a wajen manyan mu mu gujesu.
Manyanmu/yayyi mu/iyayen mu mu kai hankali nesa wajen ɗaukan mataki musamman lokacin fushi don zai iya samu mu aikata aikin danasani wanda zai rura wata wuta daza tacigaba da ruruwa bayan abinda ya faru.
Aqarshe kira ga sarki da masu unguwanninsa dama hukuma baki daya da su samar da dokoki da tsare-tsare daza su kiyaye faruwar makamancin wannan lamari.

✍️ Muhammad Mudassir

GAYYATA GAYYATA GAYYATA
15/01/2021

GAYYATA GAYYATA GAYYATA

Matasan mu  Allah yama Rayuwa Albarka
10/01/2021

Matasan mu
Allah yama Rayuwa Albarka

26/12/2020

Assalamu alaikum
Mutane
Layin Zomo
Da fatan muna lafiya
Allah yasa haka
Ameen

   Na miqa saqon ta aziya ga yan uwa da iyalaiAllah yasa Aljanna makoma
24/10/2020


Na miqa saqon ta aziya ga yan uwa da iyalai
Allah yasa Aljanna makoma

Address

Sabon Gari

Telephone

+2348081008168

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when LAYIN ZOMO MEDIA FORUM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to LAYIN ZOMO MEDIA FORUM:

Share