Yobe Progressive Youth Movement

Yobe Progressive Youth Movement Empowering the youth of Yobe State through leadership awareness, civic engagement, and community development.

Together we build progress, unity, and a stronger future.

17/05/2026

MAHAIFIYAR UMAR ABAR ZARGI CE!!!

A cigaba da Sauraren Shari'ar da ake yi wa su Umar da abaokan ta'addancinsa a bisa tuhumar kashe kashe a Unguwar Tudun Yola da Unguwar Ciranci

Jiya a zaman kotun Mijin ƙanwar Mahaifiyar Umar Wanda s**a kashewa matansa a Unguwar Tudun Yola ya Shaidawa kotu cewa

Bayan kisan da a ka yi wa matarsa kafin a raba gadonta Sai mahaifiyar Umar wacce Yayar mamaciyar ce ta kira Shi ta ce ai Umar ya ba wa ƙanwartata mamaciyar ajiyar kuɗi naira dubu ɗari biyar 500k da ɗan kunnen gwal

Sai mijin ya shiga tunani Saboda bai san da maganar ba matrsa bata sanar da shi ba amma a haka ya ɗauki kuɗin ya biya don a zauna Lafiya

Abin mmaki kuma Sai yanzu Shi Umar ɗin ya Shaidawa Jami'an tsaro da kotu ce wa Sam bai bata ajiyar Kuɗi da Gwal ɗin ba ƙarya yake yi kawai sun shirya haka ne don samun kuɗi

Kuma Shi Umar ɗin ya ce yana daga cikin dalilin da ya sa s**a kasheta har da hana su wannan kuɗin da ɗan kunnen Gwal da ta yi

Anan yakamata Mahaifiyar Umar ta zamo abin Zargi Saboda yadda ta goyi bayansa a kan zalunci da zambar kuɗaɗe da ya Shirya ta kasa banbance tsakanin gaskiya da ƙarya

In Shaa Allah duk Lokacin da gaɓa mai mahimmanci ta baiyana a cikin wannan Shari'ar za a bayyana muku

Allah Ya kyauta Ya Shiga tsakanin nagari da mugu Ya tsare mu damalmalewar wannan zamanin.

Abbas Adamu - 16 - 5 - 2026 -

Wasikar gyara kayanka kenan da muka karba daga wani bawan Allah da be bayyana sunan sa ba.SAI BANGO YA TSAGE...Assalamu ...
17/05/2026

Wasikar gyara kayanka kenan da muka karba daga wani bawan Allah da be bayyana sunan sa ba.

SAI BANGO YA TSAGE...

Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu

Ya yan uwa 'yan Arewa ina kira da bada shawara da babbar murya, dan Girman Allah mu daina zagin juna da cin mutunci tsakanin mu saboda siyasar Atiku da Kwankwaso,

Da 'yan kudu da wasu makiya Arewa suna kulle-kullen ya zasu raba kanmu a Arewa tsakanin Musulmin Arewa da Kiristoci, tsakanin Hausawa da Fulani, tsakanin sauran kabilu da Hausa/Fulani, duk basuyi nasara ba Amma yanzu sun sami hanya mai sauki a siyasance

Abin kunya, abin kunya wai dan Arewa Northeast yana zagin dan Arewa Northwest, dan Northwest yana zagin dan Northeast saboda Atiku da Kwankwaso dan Allah wace irin tarbiyya gare mu?

Su 'yan kudu basa zagin manyan su sai mu kowa yana da yancin ya shiga ko wace siyasa yayi takara, babu dole sai wani yabi wani, koko dole wani ya hade da wani. Idan wani bai hade da wani ba yayi laifi.

DAN ALLAH DAN GIRMAN ALLAH, MU SO JUNAN MU, MU DAINA CIN ZARAFIN JUNA, MU DAINA ZAGI DA CIN MUTUNCIN JUNA DA MANYAN MU

'yan kudu sunayi mana dariya, suna zagin mu, gamu da addini amma bama aiki dashi.

SAI BANGO YA TSAGE.....

17/05/2026

Shin Ko Kasan Halin Da Kanwarka Take Cikk a Gidan Mijinta?
Ka ziyarci Yar uwarka a gidanta na Aure kuyi hira da ita kayi wasa da yaranta ka bata wani abu dai-dai iko na kyautatawa, hakan zai sa taji cewa tana da Uba na biyu mai taimakonta.

Ka daure a yau dinnan ko naira dari biyar ne ka aika Mata dashi hakan zaisa ta farin ciki sosai, awannan yanayin da akeciki.

Ku tausayawa yan uwanku mata da suke gidan Aure ku jasu a jiki ku dinga tuntubar su akan yanayin zamansu, kuna yi musu nasiha da basu shawarwari lokaci Zuwa lokaci, hakan zai toshe wasu matsalolin gidan aure masu yawa. ALLAH YA SA MUDACE

Ayi Sharing Pls 🙏

17/05/2026
17/05/2026

NDC JAM'IYYAR 'YAN BIAFRA NE

NDC National Chairman= Igbo
NDC National Spokesperson = Igbo
NDC National Treasurer =Igbo
NDC National Secretary= Igbo
NDC Campaign manager = Igbo
NDC Legal Adviser= Igbo
NDC Presidential Candidate = Igbo

Ba shakka NDC jam'iyyar 'yan Biafra ne, kuma sun kafata ne don manufar Biafra, ya kamata Jagora Kwankwaso ya bude idanunsa sarai👀

Tun a tsarin jam'iyya sun nuna kabilanci b***e kuma ace sun kafa Gwamnati, inda zasu tsaya a kabilancin kadai da sauki, da zaran sun samu iko sai sun karya kowa, sai sun rusa kowa

Ya kamata ace Maigirma Kwankwaso ya jima da fahimtar cewa mutanen nan amfani dashi zasuyi domin su cimma burinsu na Kafa Kasar Biafra

Sun yaudari Kwankwaso sun jashi jikinsu don neman biyan bukatar kansu bayan sun gwada siyasar addini da kabilanci basu ci nasara ba

Da Igbo ko 'yan Biafra su karbi mulki gara Tinubu ya tabbata a kan mulki har karshen rayuwarsa

Yaa Allah Ka nesanta 'yan Biafra daga zuwa kusa da madafun ikon Nigeria

17/05/2026

Wato yakamata ace ’yan siyasar Jihar Yobe da kuma al’ummar jihar suna koyi da sauran jahohin Arewa kamar Kano da Bauchi. Shekarar 2023, jam’iyyar NNPP ba ta da ko kansila a Jihar Kano, amma sai da ta samu governor, senator, da wasu kujeru masu muhimmanci. Amma a Jihar Yobe suna ganin kamar jam’iyyar da take da mulki ce kawai za ta ci zaɓe. Wannan ba dimokuraɗiyya bane wallahi, kuma ba masu laifi kamar matasan jihar, domin su ne goben jihar.
‎Yanzu haka Kauran Bauchi yana ƙoƙarin kawo ɗan takararsa a jam’iyyar APM, kuma ina tabbatar zai ci zaɓensa. Wannan shine dimokuraɗiyya, yakamata matasan jahar yobe mu farka‼️.

By Ibrahim mamu jalo
(TATAMAMU)

'Yan siyasar kasar nanda yawa baza suga Annabi ba~Naja'atu Bala Muhammad 'Yar Gwagwarmaya Haj. Naja'atu Bala ta bayyana ...
15/05/2026

'Yan siyasar kasar nanda yawa baza suga Annabi ba
~Naja'atu Bala Muhammad

'Yar Gwagwarmaya Haj. Naja'atu Bala ta bayyana hakan ne yayin tattaunawa da gidan jaridar Freedom Radio Nigeria.

15/05/2026

Kadan daga shiri na musamman kan siyasar Kano, wanda ya mayar da hankali kan tasirin siyasar a Kano tare da Haj. Naja'atu Muhammad da zai zo muku a tasharmu ta Youtube a Freedom Radioa Nigeria.


















Address

Sabon Tasha Along Jos To Maiduguri Road Potiskum
Potiskum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yobe Progressive Youth Movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share