Tsohon Nguru Community Development Forum

Tsohon Nguru Community Development Forum The Page Was Created To Serve Tsohon Nguru Community

Tsohon Nguru Community Development Forum tana miƙa saƙon ta'aziyarta ga Vice Chairman na wannan qungiya, Babagana Mele M...
03/06/2026

Tsohon Nguru Community Development Forum tana miƙa saƙon ta'aziyarta ga Vice Chairman na wannan qungiya, Babagana Mele Mai Nguru bisa rashin Kaka da s**ayi yau Laraba.

Muna addu'a Ubangiji Allah ya gafarta mata

Chigiya! Chigiya!! Chigiya!!! Muna bada chigiyar wannan yaro, yanzu haka yana gidan Ari mai unguwa a Tsohon Nguru.Duk wa...
30/05/2026

Chigiya! Chigiya!! Chigiya!!!

Muna bada chigiyar wannan yaro, yanzu haka yana gidan Ari mai unguwa a Tsohon Nguru.

Duk wanda ya san shi, sai yaje chan ya kaishi gidansu.

A taimaka Please, yaro ne ƙarami, baya faɗan ko sunansa ma, ballantana sunan mahaifansa ko unguwarsu

Saƙon Taya Murna Qungiyar Tsohon Nguru Community Development Forum tana taya Babagana Muhammad Shettima BMS, wanda shine...
29/05/2026

Saƙon Taya Murna

Qungiyar Tsohon Nguru Community Development Forum tana taya Babagana Muhammad Shettima BMS, wanda shine chairman BoT na qungiyar da kuma Mallam Bashir Lawan , wanda shi kuma member ne a BoT ɗin qungiyar murnar sauƙe farali na Hajji.

Muna musu addu'a Allah ya ƙarbi ibadar da s**ayi, Allah ya dawo da su gida lafiya

Nan wanne layi ne a Tsohon Nguru 👇🏿Saka mana a comment section idan ka gane
29/05/2026

Nan wanne layi ne a Tsohon Nguru 👇🏿

Saka mana a comment section idan ka gane

Chairman, Muhammad Sani Amadu Nguru tareda Patron na wannan qungiya, Tsohon Nguru Community Development Forum  kuma ɗan ...
29/05/2026

Chairman, Muhammad Sani Amadu Nguru tareda Patron na wannan qungiya, Tsohon Nguru Community Development Forum kuma ɗan takarar gomna na jam'iyyar APC na jihar Yobe, Alhaji Baba Mallam Wali

MASALLACIN JUMA'A NA NATON AREWA NGURUYau Juma'a, 29th ga watan May aka gudanar da taron buɗe sabon masallacin juma'a a ...
29/05/2026

MASALLACIN JUMA'A NA NATON AREWA NGURU

Yau Juma'a, 29th ga watan May aka gudanar da taron buɗe sabon masallacin juma'a a unguwar Naton Arewa dake anan Tsohon Nguru.

Sheikh Khalifa Fatihu ne ya jagoranci buɗe Masallacin wanda Shehu Muhammad Mahiru ya gina.

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!! Ana farin cikin gayyatar ƴan'uwa musulmai zuwa buɗe Masallacin Juma'a gobe Juma'a, 29th ga...
28/05/2026

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!!

Ana farin cikin gayyatar ƴan'uwa musulmai zuwa buɗe Masallacin Juma'a gobe Juma'a, 29th ga watan May a Naton Arewa, gefen maƙabartar Sheikh Ngibirima dake anan Tsohon Nguru wanda Engr. Yusuf Maihaja (Garkuwa) yagina.

Sanarwa: Tijjani Abubakar

Ziyarar Barka Da Zuwa Hakimin Tsohon Nguru Ngilewa, Alhaji Zannah Mai Dala ya kaiwa Sheikh Mallam Musa Kallah ziyarar ba...
28/05/2026

Ziyarar Barka Da Zuwa

Hakimin Tsohon Nguru Ngilewa, Alhaji Zannah Mai Dala ya kaiwa Sheikh Mallam Musa Kallah ziyarar barka da zuwa da yayi daga ƙasar Egypt domin yi masa aiki.

ZIYARAR GAISUWA DA BARKA DA ZUWA Kwamishinan Ilimi Matakin Farko na jihar Yobe,  Associate Abba Idris Adam ya kai ziyara...
28/05/2026

ZIYARAR GAISUWA DA BARKA DA ZUWA

Kwamishinan Ilimi Matakin Farko na jihar Yobe, Associate Abba Idris Adam ya kai ziyarar jaje da gaisuwar lafiya ga Malam Musa Kallah bayan dawowarsa daga ƙasar Egypt, inda ya je domin kula da lafiyarsa.

A yayin ziyarar, Kwamishinan ya bayyana farin cikinsa da ganin Malam Musa Kallah cikin ƙoshin lafiya bayan dawowarsa gida lafiya. Yace wannan ziyara ta nuna muhimmancin kula da juna da kuma nuna ƙauna da tausayi tsakanin al’umma, musamman ga waɗanda s**a fuskanci rashin lafiya.

Kwamishinan ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ci gaba da ba Malam Musa Kallah cikakkiyar lafiya da nisan kwana, ya kuma kare shi daga dukkan wani rashin lafiya a nan gaba. Haka kuma ya jajanta tare da ƙarfafa masa guiwa kan muhimmancin cigaba da kula da lafiyarsa kamar yadda likitoci s**a ba shi shawara.

Shi ma Malam Musa Kallah ya nuna godiya matuƙa bisa wannan ziyara ta karamci da nuna kulawa da Kwamishinan Ilimi ya kai masa, yana mai cewa irin wannan ziyara na ƙara dankon zumunci.

✍🏿 Muhammad Adamu Malami
P.A to the Honourable Commissioner,
MOBSE YOBE STATE
28052026

Address

Tsohon Nguru Ward, Nguru Local Government
Nguru

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsohon Nguru Community Development Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category