Engr. Ibrahim Yakubu Youths Solidarity Movement

Engr. Ibrahim Yakubu Youths Solidarity Movement A political platform created by youths to complement the good initiatives of Engr. for his community.

Nasrun minallāhi wa fatḥun qarīb.
10/02/2026

Nasrun minallāhi wa fatḥun qarīb.

26/01/2026

Celebrating my 1st year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

03/07/2025

Engr Ibrahim Yakubu Nguru kowa naka

DUK DAN HALAL BAYA TABA MANTA ALKHAIRI Daga Engr Ibrahim Yakubu Nguru, FNSEA rayuwa, akwai mutane da sukan taka rawa ta ...
11/06/2025

DUK DAN HALAL BAYA TABA MANTA ALKHAIRI

Daga Engr Ibrahim Yakubu Nguru, FNSE

A rayuwa, akwai mutane da sukan taka rawa ta musamman wajen gina al’umma da ɗaukaka rayuwar wasu. Daya daga cikin wadannan mutane shine Sheikh Professor Isa Ali Pantami mutum mai nagarta, hangen nesa, da zuciya mai kaunar alkhairi.

Na samu damar yin aiki tare da shi a lokuta biyu masu matuƙar muhimmanci a rayuwarsa ta shugabanci. A farkon lokaci, na kasance mataimaki na musamman gare shi a lokacin da yake Babban Darakta na Hukumar Raya Fasahar Sadarwa ta Kasa wato NITDA daga shekarar 2016 zuwa 2019. A wannan lokacin, na shaida irin yadda ya canza fuskar hukumar zuwa cibiyar kirkira da ci gaban fasaha a Najeriya.

Daga bisani kuma, bayan samun ci gaban zama Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, na ci gaba da aiki tare da shi a matsayin mataimaki na musamman a bangaren tsare tsare. Wannan dama ta kara bude min ido, domin na ga irin zurfin basira da hangen nesa da ke tattare da shi.

Wani abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba shi ne mutum ne wanda “baya manta alkhairi.” Duk wani ƙanƙanin alkhairi da ka masa, zai tuna, kuma in Allah ya yarda, sai ya saka maka da dubunsa. Wannan hali ya kara min imani da cewa mutunci da sadaukarwa ba su taɓa bacewa ba.

Har ila yau, aiki tare da shi yana da matuƙar ban sha’awa da kalubale, domin kwakwalwarsa kamar computer ne ko kuma processor mai saurin aiki fiye da tsammani. Akwai buƙatar ka kasance a shiri koyaushe, domin aiki tare da shi yana ƙara maka kwarewa, ilimi da kuma ƙarfin tunani. Alhamdu lillahi, mun karu matuƙa daga ilimummuka, ladabi, hangen nesa da tsarin aiki, kuma har yanzu muna kan karuwa.

Bayan wannan, akwai wani bangare mai matuƙar taɓa zuciyata tuno da mahaifiyarsa, wadda tun kafin rasuwarta ta zame mini uwa a al’amura da dama. Mahaifiyarsa tana kula da ni da kulawa ta musamman. Tana da wata irin qauna da take yimin da kullun naje gaishe ta sai na ci abinci ko Kayan Marmari kafin in tashi. Mun koyi darussa da dama wurin kulawa da ya bata wanda ba zan taɓa mantawa ba. Allah ya jikan ta da rahma, ya sa aljanna ta zama makomarta.

A karshe, ba komai zan iya cewa ba sai “Aiki ga me yinka.” Prof. Pantami mutum ne da ya cancanci ya jagoranci alumma. Allah ya ci gaba da kare shi, ya kawo babban rabo, yasa mu wanye lafiya, ya kuma sa mu ci gaba da amfana da iliminsa da jagorancinsa.















Address

Nguru

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Engr. Ibrahim Yakubu Youths Solidarity Movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share