14/12/2024
Assalamu alaikum
Jiya mun tashi da labarin rasuwar mahaiyar Hon. Suleiman Mohammed Bello (Raya Karkaran Misau).
Yau kuma du Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyar Hon. Salisu Hussaini (Wakilin Arewan Misau), shugaban ƙaramar hukumar Misau.
Tabbas mutuwa babbar jarabawa ce, mun yi rashin iyaye kuma sun tafi har abada ba za su dawo ba. Muna addu'a Allah ya gafarta musu, ya sanya su a aljanna, Allah ya kyautata bayansu amin.
Ƴan uwa muna muku ta'aziyya, Allah ya bada haƙurin rashi.
Arc. Sadiq Ahmed Iliyasu, Gmnia, Fimc, CMC
(Sarkin Yakin Misau)
14/12/2024